Sashe 118
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai a can? Sai tambayar arshe shin wa kika bari da mijinki a gidanki matsayinki na matar aure ki kai tafiya har ta tsawon watanni, shin da sanin mijinki da kuma amincewarsa kika tafi?" Ba A'isha ba hatta iyayenta sai da zufa ta yanko masu jin tambayoyin Lauyar masu kama da tonon asiri a bainar jama'a. A'isha cikin ru ewa tace, "Ni ba inda naje kuma ban je ko'ina da wani ba Allah." Barista Jiddah ta dube ta tai murmushi tace, "A watanni uku da suka shige kinje Amurka ke da shugaban majalisar dattawa kuma ba harkar siyasa bace ta kaiku kin je ne a matsayin yarinyarsa wadda duk inda yake kina tare da shi. Sannan ba Abubakar bane ya kashe Aminatu ba ke ce kika kashe ta saboda kin dawo kin samu labarin zai aureta don haka kika kashe ta kika li a mai laifin kisan saboda kina ta amar kina da dukiya iyayenki ma nada dukiya. Sannan ta wani angaren ma kina harka da manyan dilan wayoyi wanda ke ce ke fitar da wayar ta hanyar fitar da kike da shugaban majalisar dattawa . Ta gefe guda kuma kin zubar da cikin Abubakar sau uku saboda yana takura maki wajen tafiyar da harkokinki. Ina da wa annan hujjojin a rubuce da kuma a cikin wannan faifan mai auke da sautin muryarki da duk wasu abubuwan da kika aikata ciki har lokacin da ki kai kisan kuwa." Ta mi awa Al ali an abin shi kuma ya bada aka kunna. Sai ga muryar A'isha na gayama mahaifiyarta ta kashe Aminatu saboda zata auri Abubakar ita kuma tace tai maza ta kira an sanda tace shi ne ya kashe ta bayan ta tabbatar da ya ri e wu ar da tai kisan da ita don sawun hannunta ya fice nashi ya zauna. Sai kuma aka kunna na kallon inda take amsar wayoyin tana zubawa a jaka da inda take kwance jikinsa a cikin jirgi tamkar wani mijinta. Sai kuma aka hasko lokacin data take cakawa Aminatu wu ar shi kuma ya shiga jin ihun Aminatun sai ta fisge wu ar daga cikin Aminatu ta jefa mai shi kuma ya auka ya ri e yana tallafe da Aminatun har an sanda suka shigo suka amshe wu ar suka tafi da shi kamar gawa. Sai kotu ta auki kabbara don an jima ana wannan shari'ar ta i ci ta i cinyewa sai aga ta ake kamar wani bukin da ake son rushewa. Sai Aisha ta kama zage-zage tana tsinewa Abubakar da Barista Jiddah. ali ya wanke Abubakar ya ba da damar kama A'isha da mahaifiyarta wadda ta taimaka mata gun oye laifinta ta ora shi kan mijinta. Nan take kuma aka ba damar kawo mutanen da A'isha ke harkar wayoyi da su, hatta shi kanshi an majalisar sai da aka ce a kamo shi an yanke mai hukuncin kisa ta hanyar jefewa, saboda ya yi tayayya da matar aure. Kotu ta tashi ana ta ara yabawa Barista Jiddah. Bayan sun dawo gida Abubakar ya zo ya sake bata ha uri yana kuka yana arawa. Alawiyya ce ta dube shi ba fara'a tace, "Kasan da cewa tun a binciken farko na gane ba kaine ka kashe yarinyar ba? Nayi ta jan shari'ar ne don kawai na rama wa Jiddah abin da kai mata, amma har ga Allah na tsara wannan shi ne zaman arshe da za ai da kai, daman so nake ka talauce ka shiga gararin rayuwa yadda ka jefa ta cikin unci kaima ka shiga cikinsa ka ji yadda taji kuma dama so nake ka rasa ku in da kake ta ama ka samu wanda saboda su ne ka gujeta." Kowa ya kalle ta, sai ta mi e tsaye tace, "Jiddah sai dai ki yi ha uri amma sai Yau nasa aka saki Baba da Deeni ba tare da ko sisi sun mallaka ba sai tarin nadama da nemanki ido rufe don su nemi gafararki, sai dai ban basu wannan damar ba, baki ayansu motar Jalingo nasa aka sasu domin na cika burina da nayi cewar duk wanda ya ta a saka ki kuka sai na sa shi mafiyin wanda ya saka ki. awarki ce dai Safiya lokacin da nake nemanta ban same ta sai bayan data fara amsar tukuicin abin da tayi na ganta a garin nan ne a sabon gari gidan karuwai da yarinyarta guda wadda ita kawai ta mallaka a duniya kuma abin takaici yarinyar bata sunna bace ba, sannan ta ha u da lalurin acin jiki wanda hakan yasa masu bin ta duk suka gujeta komai ya are mata ga wasu irin abubuwa da suke ta ara bayyana a jikinta ba kyan gani duk ku in data samu a harkar sun are kuma bata warke ba don haka ta koma saida goro shima ba mai siya daga arshe dai bara ta koma yi yarinyarta kuwa duk da antar ta maza sun fara bu e mata ido wanda ita ce ke sana'ar uwar tana ci da uwar haka nan a wahale ko gun kwana mai kyau ba su da shi haka suke kara zube a zauren gidan karuwan." Jiddah ta fashe da kuka jin abin da Alawiyyar tace mata, tabbas zata je da kanta ta ceci rayuwar yarinyar ko da ita ne Safiya ta tsira. Haka ita ta jima da yafe ma duk wanda ya cuce ta ranta fari tas ne kan kowa yanzu haka. Alawiyya ta dubi Jiddah tace, "Amma ina kika samo hujjar da kika bada a kotu kan A'isha?" Jiddah tai murmushi tace, "Yau kwana hu u kenan muna chat da Matashi sai naga ya yi status in wani pic wanda ya auki hankalina har nayi mai magana nace suwaye a jikin hoton daya ora a status insa? Shi ne yake gayamin abokinsa ne ke birthday party, to a jikin hotunan mata biyu ne rak don haka sai na sake tambayarsa matan fa suma duk abokanka ne Matashi? Sai ya ce min a'a aya yarinyar abokinsa mai birthday in ce gudar kuwa abokin wani ne daga abokan ya zo da ita gun bai san ta ba sai a hoton don bai je gun ba. Sai zuciyata ta dinga hasko min fuskar matar Abubakar duk da sau uku zance na ta a ganin hotonta amma don kauda kokonto sai na kira Abubakar nace ya turomin hoton matarsa, shi ne ya turomin a take na gane ita ce a jikin wancan hoton na abokin Matashi don haka sai na sake tambayarsa yana da kyakkyawar ala a da wanda ya zo da ita ne gun? Ya yi dariya ya ce ga alama dai tana cikin komarki don haka zan nemo maki labari kanta sosai amma dai ina fatan ba wani case bane mai girma ba kanta? Nai dariya nace ko ka an kawai sunanta dana abokin nake son ji ya wadatar ma da Ni. Ba a jima ba ya kira Ni ya ce min sunan ta A'isha shi kuma Abdul abokin kasuwancinta ne amma ban san wane kasuwanci bane suke. Nayi mai godiya na aje waya sai ga sa on number Abdul ya turomin kamar yasan abin da nake tunani kenan. [11/5/2022, 9:26 PM] Haupha: Cigaban page 42 Ban ata lokaci ba na auki lambar na saka a layina na aiki na kira shi ta jima tana ara bai auka ba sai kuma ya auka yana tambayar waye. Na gyara muryata sosai nace mai awar A'isha ce na kira ne na gaya mai gaskiya kanta idan ba damuwa. Ya yi jim sai kuma ya ce ina jinki amma ke ya sunanki? Ban oye mai sunana ba nace Jiddah sunana , ya ce min "Ina jinki to meke faruwa ne?" Nace ko kasan da cewar ta kashe ar aikinta ta ora wa mijinta laifin kuma yanzu haka tana shirin fallasa ala arka da ita a kotu saboda wani oyayyen dalili nata? Ya yi wani uban ashar ya ce, " arya take wallahi bari na kira Oganmu ki turomin account inki zan saka maki na kati na gode sosai da taimako." To sai na dasa alamar tambaya a gun, me yasa ya ru e don nace Aisha zata tona ala arsu? Waye Ogansu da zai kira? Me yasa ya ce zai min kyautar ku i don na taimake su? Nan da nan sai walwata ta fara nazari tana sa awa tana tacewa sai kawai na ora su a mazaunin masu laifi su duka don haka yanzu ina tare da masu laifi uku ne aya nasan laifinta kisan kai ne, su kuma biyun ne ban da tabbas kan nasu laifin amma ina da tabbacin masu laifi ne. Don haka sai na kira A'isha a waya nace mata, "Ina magana da A'isha matar Abubakar ce? Sai ban amsa da e ita ce lafiya nake nemanta? Ina na samu lambarta ? Nace mata na kira ki ne daga cibiyar bincike ta asa bisa jagorancin abokin har aklarki guda dana kama mai suna Abdul M Adam ina fatan kin san sunan koma ince mai sunan? Ta ja gwauran numfashi tace min tabbas tasan sunan tana jina. Na cigaba da ce mata, ki kwantar da hankalinki ba kece abar harina ba kamar yadda ba Abdul bane abin harinmu ba, idan kikai min yadda Abdul ya yi min tabbas ba zan sake kiranki ba, haka ba zan bari sunanki ya fita a jerin sunayen abokan cinikayyar ki ba. A'isha ina jiranki ki yi min bayanin irin har allar da kika san kuna yi sai ki ban sunan mutum guda cikin manyan dilolinku tare da bayani ka an to Ni kuma zan cire ki a list in wa anda za a kama. Cikin ikon Allah tai min bayanin wayoyi ne suke safara amma ita iyakarta fitar masu da ita asashen waje kawai saboda tana tare da babban mutum mai madafan iko wanda jirgin kansa garesa daga shi sai ita ke tafiya cikin jirgin sai mai tu in jirgin don haka suke amfani da damar suna bata wayar tana kaiwa duk asar da suka je ita da an majalisar. Ta ban sunan dilansu da arin bayanin inda take zuwa tana amsar wayar duk na na e a wayata. Bayan mun gama wayar na shirya kai tsaye na isa inda tai min kwatance na yi sa'a ba kowa gun