Sashe 84
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 39 Kotu Wajen ya yi tsit sai arar na'ura mai bada iske dake juyawa, sai kuma arar takardu da ake karantawa. Magatakarda: ya mi e ya ce, "Kotu na cigaba da sauraren shari'ar Malama Fatima wadda ta kashe mijinta har lahira, kamar yadda mai Shari'a ya yanke hukunci, don haka idan Malama Fatima na kusa ta matso. Nan da nan aka fito da Fatima zuwa inda ake ajiye masu laifi. ali tunda ya shigo yake kallon mutanen wajen musamman masu sanye Da kayan Lauyoyi amma bai ganta ba, hakan yasa ya kasa natsuwa ya jawo wayarsa ya kira lambarta, amma sai ya jita a kashe, nan da nan hankalinsa ya tashi domin yasan da wa take shari'a, yasan basu da imani akan shari'ar nan babu abin da ba za su iya aikatawa ba. Shi kanshi sun ba shi manyan ku e sun harha e shi da cewar kar da Barista Alawiyya tai nasara akan shari'ar nan so suke a kashe Fatima kawai saboda son zuciya da ganin bata da kowa bata da galihu. Ya ja ajiyar zuciya lokacin da ya tsinkayi muryar Lauyan mai ara na yi wa Fatima tambayoyi. Lauyan mai ara, "Malama Fatima wancan zaman kin maida mutane marassa amfani kin yi amfani da baiwarki kin rufe bakinki ruf kin i bayyana ko da kalma guda ce kan duk wata tambaya da akai maki, hakan na nufin cewa kin san kin aikata laifin da ake tuhumarki baki da bakin kare kanki ne ko ko ya abin yake?" Fatima, "Ba haka bane ba, wancan lokacin na kasa magana ne sam." Lauyan mai ara, "Ko dai wancan lokacin baki da wata kariya ne yasa ki kai hakan don a dinga jan shari'ar har zuwa lokaci mai tsawo don ki ata ma mutane lokaci?" Barista Alawiyya, "Ya mai girma mai Shari'a ya kamata Lauyan mai ara yasan abin da yake gayama wanda ake tuhuma saboda yana sauka kan layi sosai." Mai Shari'a cike da jin zafin Barista Alawiyya dama ga an ba shi an canji kanta don haka sai ya ce, "Ba ki da ikon hana Lauyan mai tuhuma aiwatar da aikinsa yadda ya kamata ki kiyaye harshen ki." Lauyan mai tuhuma cike da jin da i ya sake duban Fatima ya ce, "An ce dama can baki son shi lokacin da ku kai aure don haka ki ka dinga zubar mai da ciki idan kin samu wanda hakan ya ata mai rai sosai har ya ta a dukanki wanda kika sha alwashin ba zai sake dukanki ba don haka kika kashe shi." Fatima cikin alamar kuka, "Ba gaskiya bane ba, mijina bai ta a dukana ba, tunda na aure shi, kuma ba auren dole nayi ba." Lauyan mai tuhuma, "Kin ce ba auren dole ku kai ba, shin kina da shaidar hakan ne?" Fatima, hawaye suka zubo mata, domin ta tuna da tsohuwa ko tana ina yanzu? Ita ka ai ce shedar ta kuma bata san inda take ba, don haka tai shiru. Lauyan mai tuhuma cikin murmushin mugunta, "Kotu na bu atar ganin shaidar ki akan ba a uren dole ku kai da marigayi ba... Tsohuwa, "Assalamu alaikum. Ina da magana ya mai Shari'a, domin nice shaidar da ake nema wadda ta bada auren Fatima ga mijinta mai rasuwa." Nan take sai surutu ya hautsine a kotun, shi kanshi Al alin sai ya ji wani iri domin an tabbatar mai da cewar Fatima bata da kowa a Kaduna daga Lagos aka auro ta kuma bata da iyaye irin karuwan can ne kawai aka auro. Kotu ta ba tsohuwa damar fitowa fili ta tsaya aka bata Alkur'ani tai rantsuwa. Fatima ta kalli tsohuwa cike da mamaki fal a fuskarta har hawaye suka zubo mata na farin ciki, tabbas ta fita daban a mutane domin ita ce mai kukan farin ciki cikin kukan ba in ciki a lokaci guda. ali, "Tsohuwa kotu na bu atar jin gaskiyar abin da kika sani ga me da auren Fatima da mijinta." Tsohuwa, cike da natsuwa ta fa i yadda akai auren ba tare da ta ara komai ba ko ta rage komai ba. Lauyan mai tuhuma, "Tsohuwa to ke ya kike da Fatima ne?" Barista Alawiyya, "Ina neman alfarmar kotu ta tsawatar wa Lauyan mai tuhuma saboda yana mata tambayoyin da ba huruminsa ba ne ba." ali cike da fusata ya ce, "Kotu zata kore ki daga wannan shari'ar idan kika sake irin wannan maganar Barista... arar sautin takalmi mai tsini ne yasa kowa ya kalli ofar shigowa, tana sanye cikin doguwar rigar leshi ta ora rigar Lauyoyi bisa rigarta fuskarta kamar ko da yaushe ba wata kwalliya sai kwalli da man le e da powder kawai a fuskarta amma sai she i take, Barista Jiddah kenan wadda bata samu damar fitowa da wuri ba saboda ta shiga kasuwa siyen kayan Lauyoyi kasancewar bata da su kuma bata gayama Alawiyya ba saboda tana son ta siya da kanta ne kawai, sai dai kuma suna dawowa ne ta lura da Mustapha bai lafiya sai nishi yake don haka ta sake fita ta siyo mai magani sai dai ba abin da maganin ya yi tamkar ana ara mai ciwon ake ma, hakan yasa ta ru e ta ki ime sosai ta rasa abin da ke mata da i baki aya sai ta ji ta tsani kanta da kanta, sai a lokacin take jin me yasa bata ce ya koma gida ba tun da ya rako ta? Me yasa ta bar shi nan bayan yana da iyali, tana lura da yadda kowace rana sai sun kira shi kuma ga yanayin fuskarsa ba kiran mutunci ba ne su ke mai ba domin tana ganin yadda damuwa ke kwanciya kan fuskarsa idan yana amsa wayar. Shi kuma Mustpha ya yi haka ne daman don kada Jiddah ta je kotun Al ali ya ganta saboda ya lura da yadda Al alin ke son ta, don haka kishi yasa ya kwanta jinyar arya har ma ya daure akai mai allura har biyu don dai kada Jiddah ta je kotun tunda ga Alawiyya yasan zata gama komai. Sai dai kuma ganin yadda Jiddah ta damu har ta fara ha a mai kayansa tana cewa za ta saka direban Alawiyya ya kai shi gida yasa dole ya mi e ya ce mata ya samu sau i kuma ba zai tafi ya barta ba, yadda suka zo tare haka za su koma tare. Shi ne fa da taga ya dawo hayyacinsa ta tuna da wayarta ta kunna sai ga sa on Alawiyya na cewar idan ba ta zo ba za su fa i a shari'ar shi ne fa tai gaggawar zuwa kotun yanzu cike da burin cin nasara. Kai tsaye wajen da Barista Alawiyya take ta nufa bayan ta watsa ma Al alin kallo na musamman, shi kau sai da ya yi ajiyar zuciya saboda farin cikin ganinta. Barista Alawiyya ta koma layin an kallo ta zauna domin ta lura wannan shari'ar ba ta ta bace babu komai cikinta sai tarin cin hanci da soyayya don haka zata koma gefe taga tsakanin soyayya da cin hanci wanne zai galaba. Barista Jiddah ta bada gaisuwata ta musamman ga Al ali ta ara da bada uzurinta na cewar ta je nemawa an'uwanta Yayanta wanda suke tare magani don haka a gafarce ta sai yanzu ta samu damar zuwa. ali ya kalle ta fuska cike da fara'a ya ce, "Kotu tai maki uzuri kan koma miye Barista za ki iya cigaba da aikin ki." Barista Jiddah ta dubi Lauyan mai tuhuma ta ce, "Wannan karon kai zan tambaya Lauya. Shin Fatima ita ka ai ce a gidan mijinta?" Lauyan mai tuhuma ya zaro ido waje, domin babu bu atar sako sunan su Hajiya Turai a shari'ar har a gama ta don haka ya yi shiru. Barista Jiddah, ta dubi Al ali ta duka mai murmushi sannan tace, "Ya mai girma mai Shari'a ya kamata Lauyan mai tuhuma ya dinga amsa min tambayata saboda duk suna cikin arin haske kan shari'ar nan." ali ya maka ma Lauyan harara ya ce, "Kotu na umaryarka daka bu e baki ka dinga ba Barista amsar tambayar ta tunda ba wajen wasa bane nan ba." Barista Jiddah ta sake sakar mai murmushi tace, "Godiya nake ga adalin Al ali, Allah Ya cigaba da kare mana kai daga sharrin masu sharri dai." ali, cike da oki ya amsa da "Amin Barista." Barista Jiddah ta sake kai dubanta ga Lauyan mai tuhuma tai mai kallon zaka gane kurenka tace, "Shin matan Marigayin nawa ne, kuma yana da a ko bai da su?" Lauyan mai tuhuma, cikin in'ina ya ce, "Ina ga kamar yana da mata." Barista Jiddah cikin murmushinta na rainin hankali tace mai, "Barista kamar ya kana ga yana da mata? Shin baka san waye kake karewa ba ne ko ko ya akai?" Barista ya kalli Al ali domin yasan Al ali yasan komai na case in sun gama tsara komai Yau za ai faka-faka a rufe case in a tura Fatima a kashe ta ta hanyar rataye wa. ali ya doka mai harara ya ara aure fuska ya sake gyara zaman tabaran fuskarsa yai mirsisi. Barista Jiddah ta kalli Al ali fuska fal fara'a tace, "Ya kai wannan adalin Al ali shin wace irin Shari'a ce wannan ake yi? Ta ya za a ce Lauya bai san waye yake karewa ba?" ali ya kalli Lauya fuska tur une ya ce, "Kotu bata san wasa balle shashancin banza Barista kasan inda ka ke kafin nasa a tunatar da kai." Barista Jiddah ta sake wurga ma Al alin murmushi shima caraf ya maida mata da martani. Barista Jiddah ta dubi jama'ar kotun tana murmushi tace, "Ina son tunda Lauyan mai tuhuma bai san wa yake karewa ba to wadda ake tuhuma ta bayyana mana waye shi, sannan ta gangaro kan ita kanta ta bayyana mana wace ce ita saboda wannan hanyar ce kawai kotu zata fahimci gaskiyar lamarin sai kuma na gabatar da manyan hujjojina dake ajiye gefe." ali ya jinjina kansa alamar ya amince da maganar Barista Jiddah. Ta