← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 133

Sashe 91

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 41 Cikin sanyin jiki ta aje wayarta ta koma ta kwanta tana jin tamkar ba ita ba. Ji take tamkar rayuwarta ta baya ba ita ce tayi ta ba, baki aya komai sai yake zuwa mata tamkar a mafarki ko a wani littafi da take karantawa. Lumshe idonta tai tana hango yadda Mustapha ke marairaicewa yana nuna tsantsar kulawa da ita da duk abin da ya shafe ta, tana lura da yadda yake yawan kallonta yana murmushi yana girgiza kansa alamar yana cikin farin ciki da nisha i a duk lokacin daya ganta. Ita kam tasa a ranta ta gama soyayya haka zalika ba zatai aure ba duk dan wasu shekaru biyar zuwa goma masu zuwa, amma ga shi kai tsaye abin mamaki abin al'ajabi ta amsa ma Mustapha da bakinta cewar tana sonsa, kenan tana shirin komawa a fagen masoya a karo na biyu a rayuwarta kenan? Hakan na nufin ta manta da abin da Abubakar ya yi mata kenan na cin amana da muguwar yaudara? Gaskiya batai ma kanta adalci ba amsa soyayya da tai kai tsaye batare data tuna baya ba kota ji kishin abin da Abubakar ya yi mata ba ta amsa ma Mustapha cewar tana sonsa. Shin wai ma ya zatai da tarin matansa ne duk da ya ce mata yanzu matansa biyu ne? Ita fa bai kamata ace ko aure zatai ba ta auri mai mata ba, kamata ya yi ta auri wanda bai da mata wanda zata zauna ita ka ai a gidanta sai mijinta su yi rayuwa mai cike da soyayya da kula da juna, amma idan tace zata auri mai mata tabbas ba zata samu damar cika burinta ba na yin soyayya da rayuwar farin ciki a gidan aurenta ba, ta sani sarai yadda wasu matan ke hana amarya rawar gaban hantsi a cikin gidan aurenta suna cewa ta zo da rayuwar banza zata lalata masu tarbiyyar yara daga an fara maganar shike nan sai komai ya zama tarihi na rayuwar farin cikin. Ita kuma ta jima da tsarawa kanta irin rayuwar auren da zatai indai zatai aure da gaske to sai dai ta auri wanda zasu maida tsakar gidansu tamkar filin wasa inda za su sakata su wala su dinga saka kaya anana masu aukar hankali suna wasan zagaye gidan suna komai tare irinsu wanke-wanke da wanki da girki ya zama komai zatai tana jikin mijinta suna yi tare suna firar soyayya suna ba juna nisha i suna faranta ran juna. Idan kau haka ne ai bai kamata ta amsawa Mustapha ba cewar ta amince da soyayyarsa ba tunda yana da mata yana da yara kenan ba zai iya bata irin kulawar da take bu ata ba. Ta sake gyara kwanciyarta sosai tana hasko yadda ma lamarin zai wakana a tsakaninsu da matansa. Afnah ce ta shigo da gudu tana sallama tace ta je ana kira inji Baffa haka suke kiran maigidan su duka don haka ake kiransa. A hankali ta tashi ta fice tana tunanin ko Kano zai je ne yasa yake kiranta ko tana da sa o. Tana sallama ta sha jinin jikinta domin ganin Kawu Mansur zaune yana latsa waya yasa ta fahimci inda kiran yake da ma'anarsa. Cike da natsuwa ta arasa ta fara gaida shi sannan ta zauna ta sadda kanta asa bata da ta cewa kuma sai jiran abin da zai ce mata kawai. Kawu Mansur da sai kallonta yake gani yake ta ara kyau ganinta yake tamkar ba ita ba, ganinta yake tamkar an sauyo ta batai kama da wadda ta aje yara har uku ba, tafi kama da budurwa ar jami'a mai karatu a matakin farko. Bayan ya gama kalle ta yana ta jin nisha i tare da jin cewa yafi kowa dace da samun mace a rayuwarsa ya samu da yar ya saita kansa ya ce mata, "Ranki ya da e nasan ba za ki yi mamaki ba don kin ganni ba a gidanku, saboda ke ba yarinya bace ba, kuma dama can ban asa a gwiwa ba sai da na bayyana maki abin da ke asan zuciyata game da ke, na yadda kika sace min zuciya kikai min fashin duk wani kuzari da jin da i na rayuwata ta hanyar cusa min tsumin aunarki a jinin jikina Jiddah. Ina so ki sani wallahi ba ki bina bashin rantsuwa amma ban ta a ganin yarinya ko kamuwa da soyayya ba farat guda irin yadda na kamu da taki soyayyar daga ganin farko da nayi maki a kotu ba. Jiddah ki sani cewa ba komai ba ne a tarenmu illa HA IN ALLAH saboda shi ne kawai ya ha a mu a lokacin da nake niyyar yanke wa anwata hukuncin da bai kamata ba nasa son zuciya da son abin duniya a lokacin idanuna sun rufe an ban ku i na aje komai na manta koni waye na manta yadda nayi al awarin zan yi adalci zan guji rashawa da cin hanci a kan aikina, sai gaki a lokacin da babu wani tsoron Allah ko jin nadamar abin da zan aikata kika juya min zuciyata daga kallo guda aya na sauka daga layin dana hau na cin amanar aikina na koma na daidai wanda ashe alheri ne hakan a gareni saboda ar'uwata ce ashe a gabana ban sani ba. Jiddah don Allah ki sake taimakona a karo na biyu ki sake ceto zuciyata daga irin son da take maki mai cike da tsabta da nagarta." Ya yi shiru yana kallonta don jin me zata ce. Jiddah da take jin tamkar duk an aure mata duk wata jijiya ta jikinta ta bu e bakinta da yar tace, "Na gode sosai kuma na fahimce ka Kawu amma sai dai don Allah ina son kai ha uri ka bar wannan maganar saboda Ni ba aure ne a gabana ba yanzu, asalima so nake na cigaba da karatuna saboda ina da sha'awar yin karatu mai zurfin gaske a rayuwata ko don yarana idan sun girma su yi alfahari da hakan. Don haka nake baka ha uri don Allah Kawu Mansur kar kai mun mummunar fahimta don Allah." Hawaye suka zubo mata domin sai taji zuciyarta ta kare sosai. Shima sai ya ji jikinsa ya yi sanyi sosai, matarsa dake la e tai murmushin mugunta ta ji har a ranta zata taimakawa yarinyar don ganin ta samu abin da take bu ata na rayuwa don dama taji matu ar tausayin yarinyar ranar da taji labarinta kawai kishin mijinta ne yasa ta binne tausan a asan ranta. Cike da aunar Jiddah ta koma gidanta ba tare da taji me mijinta zai ce ma jiddar bama. Muryarsa irinta masu karaya ya ce mata, "Shike nan Jiddah zan yale ki a yanzu na baki lokaci ki yi karatu ki yi duk abin da kike amma ki sani ina sonki kuma idan ke in rabona ce nasan zan sameki insha Allah. Ina maki fatan alheri kuma ko da yaushe ofar taimakona gareki a bu e take Jiddah ke da yaranki." Ya tashi ya fice yana jin kamar ya yi kukan shima. Nan ta zauna ta ci-gaba da kukan da bata san ko na me ye ba, har taji muryar Baffa kanta yana cewa, "Haba Jiddah ba kuka ya kamata ki yi ba tunda ya fahimce ki sai ki gode wa Allah ai ba ki zauna ki kama kuka ba. Ina jiranki ki kawo min takardunki da sunan makarantar da kike son zuwa naga yadda za ai." Ya kama hannun Afnah suka haye bene. Alawiyya sai yamma ta sauka gidansu Jiddah saboda jin haushin in amsa mata waya da tai kuma ta kama waya ta kashe yasa Alawiyya yi mata zuwan bazata don ta yi wa mijinta kamun afa saboda ta gaji da yadda yake rayuwa a wahale ya takura kansa ya takura wa su dake tare da shi hatta yaransu ba wanda yake kulawa sai Jiddah ita ma tasan saboda mai sunanta yake kulata. Tana shiga ba kowa a gidan ga alama don haka tai nufin shiga sashen Jiddah ta watsa ruwa ta kwanta kafin su dawo ta an huta da gajiyar tafiyar da tai. Sai dai tana zuwa ta iske Jiddah kwance tamkar tana barci sai ajiyar zuciya take alamar ta ci kuka ta gode wa Allah. A hankali ta isa gabanta ta ora mata hannu kan fuskarta ta ambaci sunanta a hankali. Jiddah ta bu e idonta ta ora su kan fuskar Alawiyya sai kawai ta wume ta sosai ta fashe da kuka sosai. Ita ma Alawiyya dama zuciyarta tuni a karye take don haka sai ita ma ta fashe da kuka ba mai lallashin wani a tsakaninsu. Jiddah ce cikin kuka take cewa, "Wai me yasa ne rayuwata ba zata gyaru ba? Me yasa har zuwa yanzu na kasa samun natsuwa kamar kowace mace? Me yasa ne wai na kasa yin farin ciki har yanzu?" Alawiyya ita ma cikin kukan take cewa, "Kar da kice haka don Allah Jiddah ke in ta musamman ce nasan dole sai kin ga abubuwa masu dama na musamman kema kafin komai ya zama tarihi a gareki. Shin Jiddah baki da labarin cewa sai macen da takai mace maza kamar irinsu Faisal da Mustapha ke cewa suna so? Baki da labarin cewa sakayya ce tasa maza ke kwana da tashi da ciwon sonki ? Na rantse maki da Allah ban ji komai ba dana fahimci Babansu Anam na sonki sai farin ciki da nayi da jin da i saboda nasan duk gidan da kika shiga sai ya yi albarka sai kwanciyar hankali ta yawaita da jin da i don haka nake kwana taya mijina addu'ar Allah Ya mallaka mai ke a matsayin mata, kinga kenan ba za mu sake yin nesa da juna ba zamu rayu a waje guda gida guda asan miji guda Jiddah. Amma kar ki auka dole zan maki Jiddah ina so dai ki yi tunani ki nazari a tsakanin Mustapha da Faisal ki za i guda domin na yadda da son da kowane daga cikinsu ke maki." Jiddah ta janye jikinta daga na Alawiyya ta
Chapter 91 · 0% Book details