← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 133

Sashe 44

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

shi sai ince Allah Ya addara saduwarmu a can don nafi son mutuwa da rayuwata." Barista Alawiyya "Kenan kina nufin don ki mutu kema kika kashe mijinki?" Fatima, "Nice dai na kashe shi! Barista Alawiyya, "Ba ke kika kashe shi ba, tun yaushe kika makance?" Fatima, "Shekara tara data wuce." Barista Alawiyya, "Makaho na iya yanka Kaza ne?" Fatima, "Nice na kashe Alhaji da hannuna." Barista Alawiyya ta dubi mahaifiyarta cike da tarin damuwa tace, " Mama bayan rabuwarmu dake wace irin rayuwa kika kasance ne ?" Wani irin kuka mai karfi ya wace mata, wanda kowa sai da ya kalleta . Barista Alawiyya tayi murmushi ta zo gun da take bu ata, don haka ta dubeta tace, "Alokacin da za ki bi mijinki babu irin ro on da ban yi maki ba amma kika tsallake ni gaban Inna kika bi mijinki baki ko jin tausayina matsayina na wadda na rasa Uba kuma Uban nawa ke ce ya ba amanata saboda yasan ke ce kawai za ki iya jure zama da Ni duk rintsi duk wahala, amma saboda son mijinki ya rufe maki ido kika watsar da ni kika bi shi batare da ko waigena kin yi ba... Fatima ta fashe da kuka sosai tace, "Don Allah Alawiyya kar da kice min duk tsawon lokacin nan kina ri e da Ni a zuciyarki ne? Tabbas Alawiyya nayi godiya ga Allah tafi dubu lokacin da na bi mijina ban tafi dake ba, saboda da yanzu kin jima da barin numfashi Alawiyya." Sai tai shiru kamar wadda aka rufe wa baki. Barista Alawiyya ta dube ta tace, "Lokacin da kika tafi ita ma Inna tafiya tai har Yau bata dawo ba." Fatima ta zabura tace, "Wallahi Alawiyya dole ce tasa na yale ki ban sake nemanki ba, domin nima rayuwa nayi tamkar matacciya kawai banbancina da matacciya shi ne ina numfashi haka ana bautar da Ni ana amfani dani gun abubuwa masu yawa wanda ko da yaushe ji nake ina ma ace mutuwa nayi madadin rayuwar da nake mai cike da son kai da son abin duniya? Tabbas Alawiyya rayuwata bata da wani amfani ta baya da na bayyana maki ita, ko da yake akwai wani sirri wanda zai min katanga gun bayyana maki bayan rabuwarmu wanda nasan sai bayan an yanke min hukunci gobe kamar yadda aka gayamin zai bayyana saboda ita gaskiya bata ta oyuwa sai dai ta jima bata bayyana ba." Barista Alawiyya, "Kina nufin gobe ne za a fara zaman kotun?" Fatima, "E haka aka gayamin azun za a shiga dani kotu gobe gun da ban da kowa ba mai kareni. To nima murna nake da kashe Ni da za ai domin na gaji da rayuwata Ni ka ai babu ahalina ban da kowa Alawiyya sai fa ke to zuwana a rayuwarki yana nufin kema zan shafa maki kashin Kaji ne don haka zan tafi kotu gobe da warin gwiwar amsa duk wata tambaya kamar yadda aka gayamin amsar da zan bada saboda ina sonki rayu Alawiyya ban san a ce baki aya zuri'armu ta shafe a doron duniya." Cikin kuka Alawiyya tace, "Tabbas ahalinki ba zai ta a shafewa ba a doron duniyar nan ba Mama domin yanzu haka kina da jikoki guda uku mace guda namiji aya yanzu haka ina auke da wani cikin wanda nake saka ran wasu an biyunne ko an uku a cikinsa, kin ga kau ai zamu ya u a duniyar muma ba zamu gushe ba." Fatima ta rungume Alawiyya tana kukan farin ciki mai cike da jin da i, ita ma ashe ta zama Kaka,tana da jikoki har guda uku. Barista Alawiyya ta ci-gaba da cewa, "Ina son ki sani cewa kina da iyar da zata iya jan tunga a gaban kowa ta watar maki ancinki ta goga da kowa a kanki ta shiga ta fita ta tabbatar da cewa kin amshi ha inki gun wa anda suka wace maki shi, saboda Ni in Barista ce aikina kenan watar ma wanda aka cuta ha insa. Kin ga kuwa an Malam ya yi rawa an masa li o ina ga an maka i? Kawai ki gayamin gaskiyar abin da ya faru karki damu da komai kina tare da gatanki kamar yadda kowa ke tare da ni gatan Mamana." Fatima ta zabura hankali tashe tace, "Dama kece Lauyar da ake ta maganar ta tsaya min,za a kashe ta?" To idan dai na isa dake kin amince cewar nice na haifi ke to ina son ki janye daga wannan shari'ar saboda ban san na rasaki ban san ki shiga damuwa bayan wadda kika shiga a baya." Kawai ta tashi tana neman hanyar tafiya ranta a ace. Daidai nan wayar Dr. Faisal tai ara, wayar Daddy tai ara ita ma Barista Alawiyya wayarta tai ara. Baki aya suka aga kiran suna sauraren abin da ake gaya masu lokaci guda. Tare suka aje wayar kamar an basu umarni a tare suka kalli juna,ba wanda yace ala. Ko me aka gaya masu? Anya kuwa Fatima zata ba Barista Alawiyya Bello Gareji damar yin aikinta yadda ya kamata? Shin wane mataki Barista Alawiyya Bello Gareji zata auka a wannan shari'ar? Don Allah ku yi min afuwa abubuwa ne suka cakude min kwanakin nan don haka kuke jina shiru. Taku a kullum Haupha [8/12, 12:50 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 44 · 0% Book details