← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 133

Sashe 39

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne mai amfani don haka na biyo ki domin ki ban umarnin zuwa gidanku ta hanyar yi min kwatance idan na dace." Kamar dai bata magana yanzu ma amma sai ya samu kunnuwansa da jin muryarta mai da in gaske tana cewa, "Lafiya kake neman na baka kwatancen gidanmu?" Tabbas ya ji da in muryarta don haka bai asa a gwiwa ba ya ce mata, " Babban laifi ma kuwa ki kai wanda ba inda ya kamata ai maki hukunci sai gaban iyayenmu." Walau ta an watso mai manyan idanunta masu haske, alamar tsoro da mamaki sai kuma ta basar bata ce komai ba. Hakan yasa yasan cewa zai aiki kafin ya samu abin da yake so. Cikin alamar zolaya ya ce mata, "Kar dai ace kin razana bayan kin san kin aikata abin da nace?" Dariya ta an yi mai alamar murmushi tace, "Uhmm! Akan me zan razana tunda ban sanka ba, baka ban aikata maka komai ba?" Murmushin shima ya yi, ya ce, "To yanzu dai kar da na tsaida ki, zan so ki ban damar mallakar sunanki, da arzi in sanin inda gidanku yake don Allah." Tai murmushi karo na barkatai domin amshin turarensa na tafiya da imaninta yadda ya kamata, ashe shi ne ke wannan amshin turaren duk lokacin da zata wuce tana jinsa, bata ta a tunanin daga gunsa yake ba ai sai yanzu. Cikin sakin fuskar da bata san tana da ita ba tace, "Sunana Maryam kuma gidanmu na bayan layin nan, ban san kuma me kake so ba, bayan hakan." Ta fa a tana kallonsa idanunta cike da haske. "Gaskiya godiya zan jibga maki na bani wannan gagarumin abubuwa masu daraja a guna." Daga hakan ya dube ta yana jin nisha i fal a ransa ya ce, "Mu je na raka ki ko kin yafe min rakiyar? Amma fa ki sani idan kin yafe min rakiyar nan tabbas zuciyata zata yini cikin hukunta ni, saboda ban bata damar raka wadda take da dogon burin bayyanawa abubuwa masu yawa a gareta ba." Batai mai musu ba, don haka suka jera suna tafiya yana bata labari mai kama da labarin soyayya. Bayan wani lokaci soyayya mai girman gaske ta bayyana tsakanin Mustapha da Maryam, wanda nan da nan iyaye suka shiga cikin maganar ba tare da ata lokaci ba aka saka wata shida na aurensu. Sosai yake nuna mata soyayya duk da ita ma ba laifi tana nuna mai so iyakar iyawarta, sai dai shi a nashi hangen ba irin wannan son yake so ba, yafi son soyayya irinta wayewa wadda zata dubi idonsa ta zayyana mai yadda take jinsa a ranta da zuciyarta, ta dinga nuna mai yadda take jin kewa idan yana gun aikinsa, ta dinga tura mai sa on soyayya akai-akai ta waya. Amma ya lura ita hakan ba shi ne gabanta ba, kawai dai tana son shi don haka ba sai kuma ta ara da wani abu ba bayan son da take m ai ai tunda tace zata aure shi to a ganinta magana ta are ta gama mai komai. A ganinsa idan akai auren zata daina, zata zama yadda yake sonta zata dinga yi mai abin da yake bu ata, don haka sai ya tattara damuwar komai na rashin nuna mai soyayya da take ya watsar gefe ya dage da shirin aurensa, yasa a ransa idan ta je gidansa zai koya mata zata zama yadda yake so, ba mamaki ma ta iya soyayyar yanzu tana jin kunya ne da nauyin ba ai masu aure ba, don haka bata iya furta mai ko da kalmar ina aunarka ne a gabansa, sai dai wani lokacin a wasi a takan ce mai "I love U." Duk abin da aka tsaida rana to tabbas za a wayi gari ranar ta zo, don haka Yau kowa ya shaida aurin auren Mustapha Kabir da amaryarsa Zainab Usman, kan sadaki lakadan ba ajalan ba. Tun a satin farko ya fuskanci Maryam bata da matsalar komai wajen girki ba laifi ta iya girki, sai dai har zuwa yanzu ya rasa yadda zai ta daina nu u-nu u a gabansa, sam bata iya ko cire kaya a gabansa, ya auka don ciniki bai fa a bane don haka a ranar da tai saki guda cif da zuwa gidan ya lalla a ya amshi ha insa gunta, ta sha wahala sosai saboda shi ne karon farko, hakan yasa ya auke ta da kanshi ya nufi toilet don ya taimaka mata ta gyara jikinta, sai dai sam Maryam ta i ko bu e idonta ta ganshi saboda tsabar kunyar da take ji tashi, shi kam har ga Allah bai san wannan kunyar da take nuna mai, domin alama ce ta zata danne mai abubuwa da daman gaske, wanda ko shakka ba zai iya jurewa ba. yar ya samu ya taimaka mata tai wankan suka dawo aki, kafin ya je ya yi nashi wankan har ta auki kayanta ta saka ta shige cikin bargo tai kwanciyarta. Babu abun da ke ma shi da i ko a tunaninsa irin ya ganshi kwance jikin matarsa suna kwance sun yi lamo yana wasa da gashin kanta yana lalla a ta har tai barci, sosai yake da wannan burin na ganin komai zai matarsa na manne a jikinsa tana zuba mai shagwa a yana ta lallashinta, sai ya ji ya halaka baki aya. Yana ta tunanin ne ya shirya ya fesa turare ya haye gadon ya yaye bargon ya fesa mata turaren don bai ji alamar ta fesa ba, yana gamawa ya shige cikin jikinta, ya juye ya koma kan katifar ya maida ta saman irjinsa. Yana da niyyar cigaba da wasa da gashinta ne kawai ya ji ta zame daga jikinsa ta sauka ta koma gefe ta kwanta. Murmushi ya yi don ya yi tunanin ko an fushin nan ne na amare ta nuna mai. Don haka ya sake mirgina wa yasa hannu ya kamota ya jawo ta jikinsa yasa hannunsa duka biyun ya rungumeta yana ra a mata kalmomin ban ha uri a cikin kunnenta. Sai dai da gaske Maryam take ba ta iya kwanciya a jikinsa don da gaske ta ture shi, ta koma wani wajen ta kwanta har da ture bargon ta lullu e da zanin gado. Nan da nan damuwa ta ziyarci zuciyarsa baki aya sai duk wani farin cikin da yake ji da karsashin da yake ji ya fice daga zuciyarsa sai tunanin yadda za ai ya yi rayuwar da Maryam ke so bayan shi ba ita ce rayuwar da yake mafarkin yi a gidansa ba. Washegari ya rigata tashi, don haka sai da ya jira ta tashi ta yi masu breakfast, ko a nan ya so warai ta zuba masu a waje guda, sannan ya so warai ace yana bata a baki tana ba shi amma sai Maryam ta ha e rai karma yaga wargi ya kawo mata raini. Yana kallonta ta aje mai na shi ita kuma ta auki nata ta nufi aki, hakan yasa ya fahimci shima wannan tsarin ba zai yiyu a gidansa ba kenan na zama tare a ci abinci ana annashuwa da farin ciki tare da tsokanar juna. Bayan hakan yana cikin mafarkinsa na zaman aure. Cikin wata guda abubuwa suka dinga faruwa marassa da i tsakaninsa da Maryam, sam bata san ya dawo daga gun aiki ba ta je ta tarbeshi ba, haka bata san idan gari ya waye ba ta gaida shi ba, haka bata da lokacin zama da shi su yi hira balle yasan damuwarta kawai idan tana son abu zata dinga kumbure-kumbure ne sai da kanshi ya fahimta ya tambaye ta damuwarta sannan zata ce ka za take so. Idan bai mata ba sam bata jin nauyin gaya mai maganar duk da ta zo bakinta haka zata ya a mai hankalinta kwance. Bata damu ba idan ta ganshi a damuwa ba ta zauna gabansa ta tambaye shi damuwarsa ba. Saboda ya samu natsuwa da kwanciyar hankali yasa ya nemi transfer daga gun aikinsa ya dawo Kano amma duk a banza sai ma ya ji ina ma ace bai dawo ba? Ina ma ace sai arshen satin yake zuwa ya kwana biyu ya koma kamar yadda yake tun baya? Ace kana auren mace amma sam bata san ta dinga maka kissa da an kisisina ba, babban damuwarsa bata ta a nuna tana son ko da wasa ba ta nemi ha inta ba na aure sai dai kawai idan ya neme ta zata amince amma ita kam tafi arfin ta neme shi, hakan na ci mai tuwo a warya sosai. Ganin har ta samu ciki bai samu damar karkato da hankalinta ba kan irin rayuwar da yake mafarkin yi da ita ba yasa ya gina akinsa daban ya kwashe kayansa ya koma can da rayuwarsa domin cikin yasa baki aya ta ida azancewa ba ruwanta da shara ko wanke-wanke sai ta tara kayanta baki aya sannan take zama ta wanke da yar. Ko da ya koma akinsa daban shi kenan sai sharar nata akin ya faskara balle ta je ta share nashi akin, haka zai share abinsa bata jin komai, haka ko a jikinta. Sai su jima bata je ko hanyar akinsa ba, abinci ma idan ya dawo ya le a ya ganta ne zata tambaye shi ko zai ci abinci? Idan ya ce mata zai ci shi ne zata kai mai, idan ya ce ya oshi shi ta shafa ba ruwanta. Ganin ya kasa samun abin da yake so ne yasa ya fara neman wata yarinya ya aura, mai suna Hafsat, sosai yake da burin yarinyar ta kasance cikar burinsa saboda har ga Allah bai da burin tara mata a gidansa yafi son ya yi rayuwa irinta hutu da jin da i yasan kuwa tara mata ba zai ba shi damar hakan ba,amma ya zai yi, dole ya ara aure indai yana son kwanciyar hankalinsa na zaman auren daya tsara a rayuwarsa. Hafsat yarinya ce wayayya wadda ta gama karatunta, tana da kyau daidai nata, sannan tafi Maryam surutu nesa ba kusa ba, hakan yasa yake tsammanin zata cike ma shi gurbin da Maryam ta kasa cike mai na rayuwar aure. Lokacin da labarin aurensa ya isa gunnen Maryam ba irin haukan da batai mai ba, amma ya nuna mata ko
Chapter 39 · 0% Book details