Sashe 83
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Alh Abu Katsina wanda nake turama motocina da nake saye ina gyarawa yana siye. Sosai muke kasuwanci da shi wanda shi ne yaban shawarar na koma Katsina da kasuwancina sai na fi samun alheri. Kamar ba zan yadda ba sai da wata rana ya kirani a waya ya ce min, "Nasa anyi maka istihara an tabbatar min da cewar zaka ga Alawiyya amma fa a asar Katsina sai dai ban san a wane gari bane ba ko auye ne za ku ha u ba. Hakan yasa na shirya kayana tsab daman na biya ku in aikin hajji zan je sai na tsara tafiya ta jihar Katsina yadda idan na dawo zan cigaba da zama a Katsina kawai ina cigaba da neman Alawiyya. Bayan na dawo Makkah abubuwa suka ara bu ewa sosai da sosai arzi i ya zauna na zama babban attajiri sai na dinga siyen gidaje ina zuba mutane marassa arfi a kyauta kafin su yi nasu. Haka a kowace rana ana dafe min buhunnan shinkafa na bada sadaka duk don Allah Ya bayyana min iyata. Kar da ku auka na manta da iyayena a'a suna raina amma dana tuna sune silar rabuwata da ahalina dai na ji na tsane su ban san komawa gunsu sai da ahalina da suka raba mu. Haka zalika nayi al awarin ba zan ta a aure ba sai na samu labarin rasuwar Fatima sannan zan sake aure amma idan ba mutuwa tai ba zan ta jiranta har ta bayyana a gareni. A haka ne wata rana ina zaune sai ga aya daga cikin yarana yake gayamin aya daga cikin ma'aikatana bata lafiya ga iyarta na son gani na, na ba shi damar shigowa da ita, abin godiya ga Allah sai ga Alawiyya na gani, tunda na rabu da Alawiyya bata ta ace min ba ko a fuska don haka ina ganinta na gane ita ce Alawiyya jinina iyata da nake nema shekara da shekaru. Wannan shi ne labarina cewar Daddy yana kallonsu. Su duka su kai shiru suna jinjina lamarin rayuwar tasu baki aya, Alawiyya ta dubi Jiddah tace, "Wai kam baki samu labarin inda Babanki yake ba har zuwa yanzu ba Jiddah?" Jiddah ta ta e bakinta tace, "Ki manta kawai Barista ya manta da Ni kamar yadda na manta da shi nima, amma ina mai addu'a Allah Ya shirya shi Yasa ya gane cewar yara na da ha i kan iyayensu kamar yadda iyaye ke da ha i kan yaransu." Ta are maganar tana share hawayen takaici. Mustapha sai kallonta yake yana ji a ransa cewar duk ranar da ya aureta zai mata gata zai maida ta sarauniya tabbas zai sa ta mance duk wani acin ranta na baya. Bai ta a tunanin akwai ranar da zai zubar ma wata mace da hawayen tausayi ba sai ga shi yana zubarwa Jiddah lokuta da dama. Jiddah ita ce macen da yake mafarki, ita ce yake gani suna rayuwar farin ciki ita ce yake fatan ta gyara mai gidansa ta zama silar wanzuwar farin ciki a gidansa. Bai jin zai iya aga ma kowa akan auren Jiddah ya shirya ya gama komai na auren Jiddah jiran lokaci kawai yake domin bai yadda cewar akwai wanda zai iya auren Jiddah ya saka ta cikin farin ciki fiye da shi ba. Hakan yasa yake hangen kowane namiji ba zai iya ri e Jiddah yadda zatai farin ciki ba shi ne kawai zai iya ri e Jiddah ta rayu cike da jin da i domin yasan cewa zai iya ha ura da farin cikinsa ya sa Jiddah farin ciki haka zai iya ha ura da komai indai Jiddah bata muradi to shima bai muradin koma miye. angaren Dr Faisal kuwa shi ma ji yake ba wata katanga da zata iya shiga tsakaninsa da auren Jiddah, bai jin zai saken da zai rasa macen kirki kamar Jiddah mai ladabi da biyayya mai rayuwa kamar ta matan Sahabbai. Ya kalli Alawiyya gabanshi ya so fa uwa amma sai ya dake domin bai kamata ba ace matarsa anwarsa ta zama abar tsoro a gare shi ba, kamata ya yi ma ace ita ce zai fara tunkara da maganar neman auren Jiddah domin ta shige mai gaba kan yiyuwar lamarin matsayinta na babbar Aminiya kuma ar'uwa da suka tashi waje guda. Barista Alawiyya kuwa hangen ta inda zata fara take kawai, shin Baban Jiddah zata fara nemowa ko mijin Jiddah? Tabbas al awarinta sai ya cika sai ta hukunta mahaifin Jiddah ko da Jiddah zata nuna mata rashin jin da inta haka sai ta hukunta Deeni ko da yaran Jiddah ba za su auke ta matsayin uwa ba. Ya zama wajibi ta bazama neman mahaifin Jiddah duk duniyar da yake domin ta koya mai karatun da bai koya ba, ta ora shi kan hanyar da ya sauka ta gyara mai kuskurensa kamar yadda ta koma ta auki fansa gun Hakimi ta hanyar banka shi kotu ta dabaibaye shi da manyan hujjojin ta kai tsaye ya amsa laifinsa na kashe matarsa Baba Hassu wanda yanzu haka yana gidan yari an yanke mai hukuncin kisa ta hanyar zama gidan yari na har abada. Fatima kuwa tunanin ta yanzu ya zatai da Al ali ne ya turo mata sa on yana son ganinta kafin a koma kotu ya ara da gaya mata ta kwantar da hankalinta Shari'a zatai mata kyau kamar yadda take da kyau. Shin me yake nufi da kalamansa ne? Ita fa ba mutunniyar banza bace balle ya yi amfani da hakan ya cutar da ita ba, idan kuma sonta yake ita kam tayi bankwana da aure har abada, domin tana cikin tsanar maza ne kan abin da Abubakar ya yi mata bata manta ba ga zamanta da Deeni da bai goge mata ba a zuciyarta ba, ina ita ina wani aure yanzu? Me mazan su kai mata na kirki da zatai wani aure? Ai yanzu aikinta kawai da yaranta da mahaifiyarta ke gabanta bata da sauran wata damuwa yanzu sai ta wannan shari'ar ana gama ta zata tattara ta koma garinsu domin watarwa mata da dama ha insu da yara anana wannan shi ne sabuwar rayuwar da zata mutu kanta. To jama'a kun dai ji tunanin kowa. Sai ku biyo Haupha don jin yadda za ai. Taku a kullum Haupha [9/18, 12:17 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa