Sashe 15
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 13 Ciwon ciki sai gaba, yake na rasa Uwa mahaifiyata, ba zato ba tsammani naji wani irin kashi ya taho min, cikin dauriyar gaske na nufi waje da nufin ko tsakar gida nayi shi gobe na kwashe, don ban iya zuwa har toilet in kashin. Sai kuma wata dabarar ta zo mun na sa a hannu gefen kujera na auko ba ar leda na rarrafa na fita waje. Sai kuma tsugunnin ya gagara, dana tsugunna da zummar yin kashin sai naji wani uban nishi ya taho min, sai na daina yun urin kashin. Ina haka naji surutun mutane, ashe gidansu ya je ya taho da kishiyoyin Mamarsa. aki ya shige ko sannu bai min ba, su ne suka kama ni muka shiga aki suna jera min sannu wata kan wata. Shiru-shiru ba haihuwa ba alamar ta sai an karen shan wahalar da nake, ganin hakan yasa aya daga cikinsu tace gaskiya a samo mota a kaini asibiti tunda abin ya i hannu. Shi dai Deeni yana cikin uryar aki bai ce min sannu ba ko sau aya, ganin suna ta maganar ya fito ya samo motar kaini asibiti ya i guda daga cikinsu ta le akin. Salati ta kamayi tana tafa hannuwa tana cewa, "Yau ni Asabe naga ikon Allah! Matarka na halin na uda kai kuma ka kama kanata barci? Kai Deeni me ke damunka ne haka kamar dai wanda bai da tausayi?" Ni dai abin da ya ishe ni ya ishe ni don haka nace masu, "Don Allah ku kama ni mu tai asibitin haka nan a asa indai zan haihu na daina jin ciwon nan don Allah." Dukkansu sai suka tasa ni gaba suna jera min sannu amma Deeni yana ta barci ya i fitowa ya samo motar da za a kaini asibiti. Ganin dai abin da gaske yasa guda ta fice zuwa gidan ma wabcinmu ta buga, cikin ikon Allah yana gari tun da aiki yake zuwa wani gari ba ko da yaushe yake kwana gida ba. Ya fito ta nemi alfarmar ya taimaka ya kaini asibiti haihuwa tayi gardama, cikin azama ya fito da motar yana ta addu'ar Allah Ya raba lafiya. Deeni na cikin aki muka nufi asibiti bai le o ba balle ya ji wane asibiti za a kaini . Ina jinsu a mota suna ta fa an halin Deeni bai da kyau mutum kamar bai da zuciya a jikinsa, ace matarka na a wannan yanayin amma kai ko a jikinka? Ni kam addu'a nake yanzu Allah Yasa ajalina ne ya zo ta haka kowa ma ya huta nima na huta da angin da nake ciki kawai. Muna zuwa aka rubuta abubuwan da ake bu ata aka ce a nemo da sauri, amma ga alama cikinsu babu mai ko sisi ko da yake ko akwai ma ai basu ne ke da alhakin badawa ba, don haka su ka amshi takardar su kai shiru kowacce ta kasa cewa komai. Sai ma wabcinmu ne ya amsa ya tafi ya siyo ya kawo yace ba a samu guda uku ba ciki ance ana samunsu a nan cikin asibitin don haka su amso can, ya yi min fatan alheri Ya tafi yana jaddada Allah Yasa a rabu lafiya. To su kuma ko auka su kai ya je can ya biya ku in guda ukun kamar yadda ya biya sauran magungunan da alluran daya kawo ? Sai suka je kawai suka amso su ka bada zuwa lokacin an kai ni can cikin akin masu haihuwa, na fara fita hayyacina sai make-make nake tamkar zance ga garinku. Likitan ne ya kira wanda suka kawo ta yace "Jininta ya yi matu ar hawa, don haka ba zata iya haihuwa ba, ga shi abin da ke cikin nata arin fitowa. Yanzu sai dai ai mata aiki kawai a fito da abin da ke cikin, idan ba haka ba za a iya rasa ta a rasa abin da ke cikin cikinta." Su duka suka auki Salati suna jinjina maganar, "To yanzu Likita ya za ai kenan?" Cewar guda daga cikinsu. "Muna bu atar mijinta ya saka hannu ko wani na kusa da ita sosai sai a shigar da ita akin aikin gaggawa a fito da babyn." "To Likita ai mijinta na gida, yanzu haka mu kishiyoyin Mamarsa ne, ya kira mu yace zata haihu a gida, to ganin tana ta wahala ne yasa muka kawo ta nan shi bai zo bama." Cike da mamaki Likitan ya maimaita kalmar mijinta na gida. Wata nurse ce ta fito da sauri tana kiran "Doctor ta haihu yanzun." Bai saurari komai ba ya wuce gun ta don yaga a yanayin da take ciki. Iyakar tausayi yarinyar ta ba shi tausai gata arama ga ciwon hawan jini ya yi mata kamun gaske. Yaro namiji ne ta haifa ya dudduba ta ya taimaka mata da allurai ya tabbatar da bata cikin hatsari sannan ya fice, ya bar nurse na gyara ta da babyn. Bayan an kammala komai ne aka mi a masu yaron ni dai ban iya tuna komai, kawai dai gani kwance kaina na mugun ciwo jikina ba arfi ko ka akin hutu aka kaini don ara tabbatar da yanayin jikina, domin Likitan yace hawan jini gare ni, kuma irin wanda ke yin asa ne ba sama ba, yace yafi ha ari irinsa sosai, dole sai na dinga kiyaye abubuwa da yawa don kare lafiyata. Wata nurse ta le o tace a bada ku in allurai guda uku da suka amso gunsu kafin na haihu. Nan fa su kai shiru, da yar guda tace " Sai mijinta ya zo zai bada yana hanya." Shiru-shiru ba Deeni ba labarin Deeni har nayi awa biyu da haihuwa su kuma ba ku in da za su biya na allurar, don haka ban san ya akai ba naga sun tashi sun ce min "Jiddah bari mu je can gida mu gaya masu, har Deenin ma sai a gaya mai." Suka goya yaron suka tafi suka bar ni kwance yunwa na damuna bakina kamar ya afe don ishirwa. Tunda suka tafi basu dawo ba haka ba wanda ya zo ga nurse in nan bata da mutunci sai masifa take kar a gudun masu da ku i,abin duk ya taru ya yi min yawa. Na haihu ko fuskar yaron ban gani ba, ga yunwa, ga ishirwa, sannan an barni kan gadon asibiti da bashin da ban san ko nawa bane ba. Mutane nata shigowa gaida marassa lafiya nan wata awar Mamana ta ganni kwance ta iso gadona tana min ya jiki ta tambayeni yadda akai. Na gaya mata sun je da abin da aka haifa gida tun azun basu dawo ba su nake jira mu tafi tare. Nurse in nan ce ta dawo tana ta masifar duk abin da nake tana kallona ba zan gudar masu da ku i ba. Kawar Mama ce ta dube ta tace, "Ke kam baiwar Allah ku in har nawa ne da kike ta wannan masifar? Kuma ita miye nata a ciki ba kawo ta akai ba?" Nurse ta ta e bakinta tace, "Ai dole nayi masifa Naira ari tara ne da talatin ku in, kin ga kau ba nayi shiru ba a wuce da su ba." Zaninta ta kwance ta fito da Naira dubu ta bata, "Ga shi ban canji, Allah Ya sawwa e." Ta amsa tana "Amin dai." Waje ta fita ta siyomin taliya da ruwa, na kuwa cinye ta tas, sai naji ciwon kan ya rage har ina iya tashi. Ganin hakan yasa tace "Daurewa za ki yi mu isa can gidansu mijin naki Jiddah? Sai na kai ki na je na sanarwa da Innarki halin da ake ciki." Na ji da i, domin zaman asibitin ya ishe ni sosai. asa muka tafi gidan, domin babu masu mota, Ni kuma ban iya hawa mashin saboda ciwon kaina ga marata na juyawa lokaci zuwa lokaci. Da muka isa gidan har an ma yaro wanka an goye shi , suna ta hidimar su kamar ba a bar kowa asibiti ba watau ni Jiddah uwar yaron. Suna ganinmu sukai ta irin abin nan na jin kunya, nan da nan aka ora ruwan wanka aka zubomin tuwo. Ita kuma ta wuce don isar ma Mamata sau on haihuwar. Sai da nayi wanka na fito na gyara jikina don ma naga ban zubar da jini sosai, ko da yake mi na ci wanda zai sa na samu jini mai yawa a jikina? Babbar Yayarsu ce ta goya yaron muka tafi gida har zuwa lokacin ban saka Deeni a cikin idanuna ba. Muna zuwa muka iske gidan a bu e, ga wuta na ci alamar girki Deeni ke yi, yadda na bi shi da kallo haka ya bini da kallo yaron kawai ya amsa ba tare da yace komai ba. Ni dai kwanciya nai ma, don na gaji sosai kamar an mun dukan tsiya haka nake jin baki aya jikina. Sallamar dangin mahaifiyata naji sun shigo da yawansu suna ta fara'a da jera min sannu ba iyaka. Bokiti ne ri e a hannun anwar Mamarmu cike da kunun kanwa sai amshi yake. Ko ba ace daga Mama ba nasan ita ce ta damo min shi. Ai kuwa naji da in kunun sosai, domin na lura tunda na haihu motsi ka an sai in ji cikina babu komai yunwa na neman zautani. Duk abin nan sai lokacin Yayar Deeni ta amso yaron a hannunsa ta kai masu, shi kuma ya fito ba kunya ba komai ya juye taliyar da ya dafa ya koma aki, sai su ne ma suka dinga gaida shi suna yi ma shi barka an samu aruwa. Yana gama cin abincinsa ya fito ya bar gidan ba tare da ko kalma guda ta shiga tsakanina da shi ba balle ya sammun taliyar daya dafa. anwar Mamarmu ta kira ni cikin aki daga ni sai ita tace, "Innarki tace a tambayeki kuna da kayan abinci? Kuma akwai ku i gunki? Kina da kayan da yaron zai sa?" Kaina asa nace "Babu komai gidan Inna." Nan tabar ni ta fice ina jin lokacin da take ce ma