Sashe 76
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Jiddah ya nemi afuwa gunta? Tabbas yana bu atar ganin Jiddah don ta yafe mai duk abin da ya yi mata su koma da rayuwarsu cikin aminci da kwanciyar hankali, zai dinga kula da ita iyakar arfinsa ba zai sake mata abin da bata so insha Allah. Haka Deeni ya koma rayuwa a cikin aki guda tal ba katangu ba komai sai wannan aki guda, duk abin duniya ya dame shi ya rasa aikin da zai samu ko na abinci ya dinga samu sai dai kullum yana bin gidajen danginsa wani gidan a ba shi wani gidan ai kamar ba a san da zuwansa ba. Duk wanda yasan Deeni idan ya ganshi yanzu sai ya tausaya mai, domin ya koma kamar mahauci tsabar wahalar rayuwa, icce ya ke zuwa daji ya yo da yar yake samun mai siyen iccen wani lokacin ma bai samun mai siyen iccen sai dai ya kawo gida ya aje kuma sai yara su sace shi. Iyakar ganin rayuwa tabbas yana ganin rayuwa abin ba a cewa komai sai dai abi shi da Allah Ya kyauta.. Yanzu kwata-kwata babu ma maganar wani aure a gabansa domin bai da abin yin auren bai da inda zai aje matar, hakan yasa ya fara shawarar ibar gidan ya saida ko kuma ya saida gidan baki aya ya samu ko na asa ne ta siya arami sauran ku in sun ishe shi ya biya sadakin Jiddah ya sai mata an kayan fita biki ya bata su zauna ta ci-gaba da sana'arta tana samun ku en ci da su cikin kwanciyar hankali. Wannan shawarar ya aminta da ita, don haka ya saka gidan a kasuwa nan da nan kuwa aka saida shi aka ba shi ku in ya ce a samar mai aramin gida zai siya kamar yadda ya yi shawara kafin ya saida gidan. Sai dai yana kwance cikin dare arayi suka diro mai su kai mai dukan tsiya suka amshe ku in gidan duka sukai tafiyarsu suka barshi a kwance rai hannun Allah. Sai da asuba mutane suka shigo su kai mai jaje suka fice kowa na cewa alhakin matarsa ne ke bibiyarsa wasu ma cewa su ke ka an ya gani ai. A hankali Deeni ya koma shiru-shiru marar magana ya daina zama cikin mutane ya daina aikin komai sai zama akin mahaifiyarsa kawai, sai wanda ya ga Allah cikin mutanen gidan kawai ke ba shi abinci wani lokacin.