← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 133

Sashe 106

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zama sorry. Ita kuma duk lokacin da aka kawo mata zugarshi sai taji ya bata tausai amma dai Hausawa na cewa ana tauna tsakuwa ko dan aya taji tsoro sai ta kira shi a waya taita fushi tana cewa ta gaji da surutun mutane kada fa ace da gaske ne. Bawan Allah zai ta lallashinta yana rantse mata kan idan ya ci amanarta Allah ya saka mata kawai hassada ce ake mai don zai aure ta. Ni da Bilkisu awata sai komai ya lalace domin na fahimci munafuka ce tana son samun magana daga bakina don ta gayama matarsa Maryam sai kawai na rufe ta na fice daga sabgarta amma sai ta dinga biyoni har gidan Hajjo tana son bugar cikina don taji yadda muke ciki da Prince, Ni kuma sai na i gaya mata komai sai ta koma yi min bincike a waya tana duba sa onni da hotunan da mukai da shi, hakan yasa na fito na gaya mata cewar mun ata da Mustapha yanzu har na fitar da wanda zan aura a Kaduna bu ar bakinta sai cewa tai, ai wallahi daman nasan kin fi arfinsa yo me za ki yi da Mustapha Allah na tuba? Ai ba ajinki bane ba ya je ya ji da kansa ma da hayaniyar gidansa ina shi ina ke ban da neman magana? Ai daman nasan yaudararsa kawai kike don ki yagi abin da kika yaga ki kama gabanki don bai da wayau kashe ma mata ku i kawai yake suna mai wayau don ba mai iya aurenshi ta kawo kanta gidanshi duk masifa da azanta ta kashe ta." Tun da naji haka daga bakin Bilkisu sai nayi mata dogon layi mai kyau na saka ta ciki kawai na rufe. A farko tana gaba wajen cemin nayi dacen miji domin bai da matsala har cewa tai yafi mijinta kula kawai mata ne bai dace ba amma mutum ne har da ari Yau kuma ga abin da tace min saboda ta ha e kai da matarsa bata son na shiga gidansa da sunan aure. Sai na sauya mata ko a fuska na daina ko doguwar magana da ita kawai na kame kaina na daina bata ko wayata duk da cewar tana tambayata . Sai kuma suka tsiri turo min yara su gani ko Mustapha na gidan Hajjo sai ina zaune naga yara na le e duk na tarkata su na watsar kawai nasa a raina aurene dai nice mai yinsa don haka zan auri Mustapha ko da ace munanan halayen da ake ambata yana da su to tabbas ina da tabbacin zan iya sauya shi indai da gaske yana sona nima ina sonsa to sauya shi ba wani abin ku zo ku gani bane ba. Tunda nayi rayuwa da Deeni wane namiji ne ban iya rayuwa da shi? Ban ganshi ba zan iya rayuwa da kowane irin namiji a yanzu Ni. JALINGO Tafiya mai da i a gunsu Alawiyya da Prince Ni kam murna aya nake zan je na ga Mamana ban da wannan ba wata murna da nake sai kawai kallon titi, lura da hakan da sukai ma yasa sai fira su ke su ka ai basu saka Ni don hankalina ba kansu yake ba ya koma a can shekarun baya na koma tunano rayuwar da nayi a baya mai cike da alubale kala-kala ko ince iri-iri a cikin garin Jalingon. Har muka isa fuskata ba walwala gidan Mamana muka fara sauka da yake tasan da zuwanmu ta shirya mana abinci mai rai da lafiya naji da in yadda na ganta cikin aminci da natsuwa bata tare da damuwa ko takaici hakan yasa na sake sakin fuskata na ji da i ya ziyarci zuciyata baki aya har ma na ware ana ta fira da ni kamar ba nice mai ha e ran nan ba sam ba fara'a kan fuskata ba. Daga nan gidajen dangin Mamata muka je suka ga wanda zan aura sunata addu'a suna nuna jin da in su kan auren da zan yi kuma ga alama duk sun yaba da za in nawa. Sai daga arshe muka nufi gidan Babana tun daga nesa naga gidan duk ya sauya kamar ba shi ba, haka mu kai fakin muka sauka. Yana zaune yana jan casbaha a hannunsa duk ya rame ya koma kamar ba shi ba, ga alama ma bai da wadatar lafiya, a hankali muka isa inda yake muka gaida shi amma abin takaici abin mamaki Alawiyya kawai ya gane ya zabura yana ro onta ta kaishi inda zai ga Jiddah don Allah. Kaina na asa ina kukan takaici aka nuna mai Ni matsayin iyarsa wadda ya manta da ita wadda bai sonta wadda bai damu da ita ba ita ce gabanshi tsugunne bai gane ta ba. Ya kama Ni ya ri e yana kuka yana neman afuwata sai kuma tari ya taso mai kamar zai sume hakan yasa zargina ya tabbata bai da lafiya ganin mutane sun fara taruwa yasa muka shiga cikin gidan baki aya. Komai na yadda yake yadda na sanshi yadda na barshi sai dai tsufa kawai da gidan ya yi na rashin fenti . Mutanen gidan suma kowa na nan sai ara manyan ta da sukai ba kunya ba tsoron Allah haka suka dinga ihun murnar zuwan Jiddah gidan nasu. Lokaci ka an kowa ya hallara don haka Mustapha ya gaida kowa ya gabatar da kansa matsayin wanda ke neman auren Jiddah ba musu kowa ya amince to daman wane musu za su yi tunda ba wanda ke ci da ita ko shayar da ita balle ya damu da halin da take ciki ko a baya balle yanzu? Washe gari Baffa ya zo da tarin mutanensa inda dangin Mustapha suka iso suma da zummar kawo ku in neman aure sai dai labarin ya sha bamban inda nan take aka ce a bada ku in sadaki dana jin magana da komai a aura auren. Cikin ikon Allah mutane suka shaida aurin auren Hawwa'u da Mustapha akan sadaki naira dubi hamsin cif. Nan da nan bakin ango ya kasa rufuwa ya dinga kiran abokai da an'uwa yana gaya masu an aura mai aure da Jiddah yanzu haka a Jalingo. Cikin murna ya kira matarsa Maryam ya gaya mata an aura aurensa da Jiddah tai ta ruwan masifa da bala'in nan za a zo a iske su a tai a barsu dai. Washegari aka dunguma baki aya har da Baban Jiddah sai Kano don ganin inda za a aje Jiddah. Gida mai kyan gaske kuwa aka kai kayan Jiddah wanda tsayawa bayyana su abin kamar auyanci ne, saitin kaya biyu masu kyan gaske an yayi Baffa ya yi ma Jiddah da kujerunta masu kyau komai ya ji a gidan sai fatan zaman lafiya ga masu gidan kawai. An tsaida lokaci Jiddah zata tare gidanta bayan sati biyu cif wanda hakan sam bai ma ango da i ba ji yake tamkar an ce sai bayan shekara biyu Jiddah zata tare a gidan nashi. Jiddah kuwa ta ji da in hakan don ba shirin da tai, don haka cikin lokaci suka fara kimtsawa ita da Alawiyya, ba a bar Iyami (Jiddah) a baya ba itama ta tashi tsaye ta shiga kimtsa Jiddah ta ko'ina Jiddah amsar kayan gyaran jiki take hakan yasa duk lokacin da suka ha u da Prince sai ta yi da gaske suke rabuwa sai ya bi ya narke ya koma abin tausayi ya ce bata jin tausansa ta daina sonsa orafi kala-kala kuma wai sati biyun ta i yi ma shi ina zai sa kansa? Duk inda Jiddah ta saka afa Mustapha na biye da ita, haka duk inda zai je tana tare da shi hakan yasa Hajjo ta agara su tare gidansu ma a huta da nacin da Mustapha ke yi duk da yadda matansa ke ruwan masifa da aiken ba en maganganu abin bai mata da i amma ta lura ita uwar gayyar ko a jikinta harkar gabanta kawai take ba ruwanta da ananan lamurran da ake yi kanta da mijin nata. Bayan sati biyu Tunda safe ya kira Alawiyya a waya yana tambayarta yanzu za a zo aukar amarya ko ko sai da rana?" Abin dariya ya ba Alawiyya ta dubi agogo taga arfe bakwai na safe amma yake kiran yanzu za a zo aukar amarya, lallai Mustapha abin nashi azimun ne don haka sai tace ka kira Hajjo ka ji man ai sune masu bada amaryar. Jiddah na gefen Alawiyya ta dubeta suka fashe da dariya suka tafa , Alawiyya tace "Ke nifa ban ga laifinsa ba taya ina da mata kamar ke ace kina can ina can? Tab ai kawai ya yi magana akai mai matarsa kowa ya huta shima ya huta kema tsohuwar munafuka ki huta. Yawwa wai ya akai kika gayama Yusuf Matashi za ki aure har naga ya aiko maki da sa on Allah Yasa alheri da kyautar girma Jiddah?" Jiddah tai murmushi tace, "Ranar da muka fito kotu kan case in Abubakar a ranar ya turomin da hotonsa da wata yarinya ya ce min ita ce za in da mahaifiyarsa tai mai ta kuma yi rantsuwa cewar ba zai auri Lauya ba ar wuta ba ya kai mata cikin zuri'a ba. Hakan yasa yake ban ha uri don Allah na yafe masa amma don Allah kar da mu yanke zumunci nayi murmushi nace abin ya yi min da i don haka bayan kwana biyu na tura mai hotona da Prince nace mai ga wanda zan aura an'uwana ne. Shike nan yanzu haka maganar da nake maki suna matu ar mutunci da Prince nima ina gaisawa da matarsa Hanan sunce ma yau za su zo gun tare wa ta insha Allah." "Kai Jiddah tabbas kina da sa'a a rayuwarki duk yadda abu ya dun ule maki sai kinga inda haske ya fito ya warware maki shi." Cewar Alawiyya kenan tana murmushi. Da yamma aka auki amarya sai gidan mijinta kuma Prince inta. Mahaifinta ya jima yana mata nasiha haka ma su Baffa sun yi mata nasiha sosai ta zauna gidanta lafiya da abokan zamanta kar da ta zama silar damuwa ga mijinta. Bayan kowa ya watse ne Alawiyya ta dubi Mustapha tace, "A al'adarmu bayan an kawo amarya an watse Ni zan sake aukar amarya na kaita gidana
Chapter 106 · 0% Book details