← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 133

Sashe 41

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 25 Tana zaune ta buga uban tagumi, kowa yasan ta da wannan tabi'ar ta zama ta buga tagumi cikin zuzzurfan tunani, wanda wani lokacin sai dai kaga hawaye sun gangaro daga idanunta. Tun da ya shigo gidan ya ji tsit yasan ta fara sana'ar tata, shi kau da ace yasan yadda zai ya wanke mata zuciyarta daga tunanin baya tabbas daya wanke mata, amma ta ya zai yi? Duk wani abin da yasan zai sata farin ciki da walwala ko da yaushe yi mata yake, ba shi ka ai ba, kowa na nuna mata auna kowa sonta yake, yanzu ta zama daidai da kowa a cikin mutane amma Alawiyya ta kasa cire tunanin mutane biyu a zuciyarta, mahaifiyarta da awarta Jiddah. Babu ranar da bata zubar da hawaye, kamar yadda babu ranar da bata bin tashar motocin garin Kano don a cewar ta zata ha u da ko Jiddah ko Mamarta a tashar haka jikinta ke bata a kullum. A hankali ya isa inda take yana jin tausayinta na yawo a cikin ilahirin jikinsa, ta bayanta ya zagayo ya rungumeta yana mai saukar da ajiyar zuciya. Saurin goge hawayen idonta tai, don tasan babu abin da ya tsana irin ganinta cikin kuka da tashin hankali. Yana mamakin yadda take da dakiya da jajircewa ace wai ita ce ko da yaushe sai kuka. Ita ce mai saka mutane da dama kuka, a kotu amma ita a gida kullum sai ta yi kuka. Ta zama babbar Lauya wadda baki aya jahar Kano ke ta ama da ita, domin babu case in da zata amsa batai nasara kansa ba. Jama'a da dama na jinjina mata wasu na yawan turo mata da wasi ar rayuwarta na birge su, ina ma ace suma yadda ta taso suke? Da sun ji da in sosai domin kowa ya ganta bai ta a cewa tasan miye damuwa ko matsala, sai hanyar warware su kawai ta sani. A duk lokacin da taci karo da zantukan mutane a shafin ta na Facebook, IG, Twitter, WhatsApp, sai na ji hawaye sun zubo mata, domin da sun san ba ar wahalar data sha a rayuwarta kafin ta kai wannan matakin sam da babu wanda zai sha'awar kasancewa a matsayin da take ko da wasa. Sai dai daman haka abin Allah yake sau tari sai ka ci ba ar wahala ka shiga muguwar matsala sai kaga lokaci guda komai ya koma maka daidai, ka wayi gari ka ganka cikin ni'ima, hatta mutanen da suka dinga hantararka suka dinga aibantaka sai ka ga duk sun dawo fadawanka. Ikon Allah kenan mai juya lamari a lokacin daya so. Ya azurta wanda Ya so, alokacin da Ya so. Wata gurguwar mata ce ta tu o keken guragunta ta isa inda Alawiyya ke zaune tana ta kuka riris, mijinta Dr. Faisal na ta lallashinta tamkar yana ara mata aimin kukanta. Cikin sanyin jiki tsohuwar ta dafa kafa ar Alawiyya tace, "Haba ke ko, kullum sai kin saka mu kuka a cikin gidan nan, bayan ke ce kullum ke saka jama'ar gari dariya a waje, me yasa kika za i saka mutanen da suke da kusanci dake kuka madadin dariya ne Alawiyya?" Cikin Muryar kuka tace, "Kaka wallahi ko da yaushe ina ganin Jiddah da Mama a mawuyacin hali, duk sanda nayi istihara na kwanta sai na gansu a mummunan hali, shin taya ba zan koka ba? Babban abin da yasa na karanci lauya don kawai na watarwa yara da mata ha insu kan mugayen mazajensu na dinga watarwa yara irinsu Jiddah ha insu kan iyayensu, amma a banza ban samu damar ganin Jiddah ba alokacin da burin nawa ya ci ka ba, shi yasa kika ga ban ta a amsar ku in Shari'a ba indai ta shafi neman anci ne ta yara ko mata ba, duk saboda Ni ka ai nasan wace irin rayuwa mu kai a Lagos Ni da Jiddah. Sannan a gabanki na ida rayuwata mai cike da tsana da tsangwama asalima kina cikin mutanen da suka fi kowa nuna min tsana da tsangwama a lokacin. Shin taya ba zan kuka ba idan na tuna cewa mutane biyu da suke da muhimmanci a rayuwata basu tare da ni kuma ban da tabbacin suna cikin aminci ko akasinsa? Don Allah ku dinga min adalci akan dukkan lamurrana Kaka indai... Maganarta ta ma ale lokacin da gidan talabijin suka hasko fuskar wata mata aure da ankwa ana fa in ta kashe mijinta mai suna Captain Aliyu Masani wanda suke zaune a cikin garin Kaduna, shi dai marigayi sojan yana da mata uku ne amma Fatima ita ce amarya a cikin matansa, wanda sun yi aure shekaru masu dama da suka shu e... Sai dai ganin Alawiyya akai ta sulmiyo daga kan kujerar da take ba numfashi. A daidai lokacin wayar Alawiyya tai ara, Faisal ya auki wayar don yaga sunan mahaifin Alawiyya ne ke yawo kan wayar, shima a cikin muryar tashin hankali yake cewa, "Maza ki kunna talabijin ki ga Fatima wai ta kashe mijinta! Wallahi nasan Fatima ba zata ta a kashe mai rai ba, balle mijin da take aure ba." Shi dai sai ya samu kansa da gayama Daddyn abin da ya faru da Alawiyya sakamakon kallon matar da tai itama. Cikin tashin hankali ya ce, "Maza ka shafa mata ruwa tai waya can Kadunar ta tabbatar da ita ce zata tsaya ma mai laifin." Kafin Faisal yace komai ya kashe wayar ga alama gidanma zai nufo. Alawiyya na farfa o wa ta jawo wayarta, bugu biyu aka auka, domin kowa yasan wacece Barista Alawiyya, lauyoyi da dama suna son buga Shari'a da ita, musamman don su samu damar samu sunansu ya yi tambari a duniyar jaridu. Duk da cewa sun san duk wanda ya tsaya kotu buga Shari'a da Barista Alawiyya to tabbas shi ne ke fa uwa amma ba su damu ba, saboda ita in ta musamman ce a fagen iya aiki da nuna warewa kan aikinta. Cikin Muryar kuka take tabbatar da cewa ita ce zata kare matar data kashe mijinta. Ba wani ja aka amsa mata don sanin wacece ita. Cikin lokaci ka an ta shirya kayan da take bu ata, a bakin gate in gidan sukai karo da motar mahaifinta shima ya zo, don haka a waya kawai su kai magana suka cinna kan motarsu suka kama hanyar Kaduna cike da tashin hankali da muguwar fargaba. Tabbas ko a mafarki taga mahaifiyarta sai ga gane ta balle a fili, duk yadda ta sauya ta lalace ta fice hayyacinta hakan bai hana ta gane ta ba, to tsohon mijinta ma ya gane ta balle ita da ta tsugunna ta haifa? Tabbas zata baje duk wata basira da hikimarta tare da warewarta domin tabbatar da gaskiyar abin da ke faruwa da mahaifiyarta. "Wallahi ba zata kashe mutum ba Mama." Cewar ta da arfi tana jin tamkar tai wauta data taho a mota inama ace a jirgi ta nufi Kadunar tabbas da ya fi sauri. Shi ma ta angaren Alh. Bello abin da yake rayawa a ransa kenan, me yasa ba jirgi suka hau ba? Kada fa kafin su je wani abu ya sameta! Fatima har zuwa yanzu kina nan da kyanki duk da tarin wahala da jigatar dake shimfi e a jikinki sai da na gasgata kyanki na kuma amince da bake kika kashe mijinki ba sam." Sai surutu yake shi ka ai, Allah ne kawai ya kai su Kaduna lafiya. Suna isa kai tsaye office in da aka kai ta suka je, har an kaita gidan yarin dake Kabala Custom ajiya kafin a fara Shari'a. Cikin sauri aka tarbi Alawiyya don kowa yasan ta kafin ma tace ga ta an gane ta. Neman izinin mai laifin tai, nan take aka bata dama ta je ta zauna inda zata gana da ita. Zaune take ita ka ai a akin cikin duhu kasancewar mijin nata babba ne a gun aikinsa, ba aramin duka da izaya ta ci ba kafin a kawo ta nan wajen ba, addu'a take Allah Yasa ta mutu kafin ma a fara Shari'ar, fata take Allah Ya auki ranta ta huta da ba ar rayuwar da take mai cike da unci da takaici. Har zuwa yanzu ta kasa cire iyarta da danginta daga cikin zuciyarta rayuwa take kawai tamkar matta, ita daman tasan ba banbanci gareta ba tsakaninta da gawa ba, domin rayuwar da take ciki mutuwa ta fi sau i a gare ta... "Ke munafuka maza ki taso an zo gunki. Amma wallahi ban so Barista Alawiyya ta shiga case inki ba, munafukar Allah ta'ala sai wani sinne kai kike kamar mutunniyar arzi i, amma ta banza ce." Ta dinga ingiza eyarta tana tujara da masifa kamar mijinta ne ta kashe ko ubanta. Tana zuwa akin Alawiyya ta ruga ta rungume ta sai kuka ya wace mata mai cin rai. "Mamana! Mamana! Mamana! Ina kika shige ne? Wace duniyar kika tafi kika barni? Mamana me yasa kika manta da Ni?" Kamar ko da yaushe haka ta auka Yau mafarkin iyarta take, sai dai Yau kalaman iyarta sun sha bambam dana ko da yaushe da take yi. "Fatimaaa! Ya ja sunan da arfi ya iso daf da su, sai dai ita in ba matarsa ba ce, don haka ya ri e Alawiyya gam madadin Fatimar. Kamar muryar Bello take ji, namijin da har duniya ta na e bata ta a samun wanda zai ko da kama rabin yatsansa ne a gunta. Mutumin da ya nuna mata soyayya da kulawa ba yama ba mugunta ko da yaushe cikin tattashinta yake. Tabbas mafarkin Yau insha Allah wanda zai tafi da ruhinta ne, don haka ta nemi sulale don kar ta mutu a tsaye. Sai dai Alawiyya ba aramin ri o tai mata ba, hakan yasa ta fara fahimtar kamar da gaske ba mafarki take ba, kamar fa da gaske jikin Alawiyya take, to idan haka ne muryar Bello da ta ji itama da gaske ne yana gun? Allah Sarki da ace tana gani da taga yadda Alawiyya ta girma ta koma da taga yadda Bello ya koma
Chapter 41 · 0% Book details