Sashe 26
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana ban ha uri, tace zai je ya sameta, Ni dai ha uri kawai nake bata don ban da ta cewa ( arawo hannun mata) ta gama fa anta sosai tace zata aiko min da geron damun kunu da masara a dinga tuwo da dare nai mata godiya ta tafi. Sai ga gero da masara kuwa yara sun kawo na amsa na aje ina ara gode wa Allah daya rufa min asiri ban kasa samun abin da zan ci ba a wannan haihuwar ba. Cikin dare ya dawo har nayi barci ya tada Ni cike da bala'i yake cewa, "Ke har kin isa ki ha a Ni da mahaifiyata ne? To akwai uban daya isa yasa Ni yin abin da ban yi niyya bane ba? Ban da rainin hankali irin naki ma Ni nasan ma lokacin da za ki haihun ne? Ba kawai don an auke Ni an iska ba sai aka same Ni aka gayamin wai kina asibiti baki lafiya don kuma an auke Ni an iska sai aka kai ki asibitin ku i tunda ga Sakarai ko? Ai shi yasa na yale ku na i zuwa." Ni yanzu fa an Deeni bai damuna don haka har ya yi abin sa ya gama ban tanka mai ba, sai da ya dube ni yace "Yara kuma aya ta ci sunan budurwata Safiya ayar kuma sunan awar Safiya ne A'isha." Idona waje nace "Gaskiyar magana ban san suna ko guda a cikin sunayen sai dai a sake wasu amma baka saka min sunan Safiya da awarta a yarana haka kawai su kwaso mugayen halayen masu sunan." Har ya wani zaburo zai kawo min duka sai kuma naga ya janye hannunsa ya buga tsaki yace, "Tunda yaran naki ne ai sai ki sauya masu sunan. Ke bari ma ki ji ba dan Safiyar taban ha uri ba wallahi da ban yi masu yankan sai da tasa baki sannan na amince zan masu yanka amma da yake baki da godiya baki san mutunci ba shi ne don ta za i sunayen da za a saka ma yaran za ki ce baki so, to wallahi sai an sa su ki mace idan an gaya maki sunayen ranar sunan." Daga haka ya gyara kwanciyarsa ina jinsa ya kira waya wadda nasan mace ce ya kira daga jin yadda yake tambayar ta batai barci ba?. Wannan karon ma Hajjo daren suna ta zo sai dai ba ta kawo min kayan abinci kamar wancan karon ba ta dai zo da sutura na yaran da nawa masu kyau ko Ni kala shida ta kawo min yaran kuwa akwati biyu aka kawo masu hatta Haidar an kawo ma shi kala biyar masu kyan gaske. Washegari ranar suna ina ta jiran naji sunan yara sai ga shi kam ance min an samu Safiya da A'isha. Hawaye suka zubomin Mamar Khairat ta tambayeni abin da ya faru na gaya mata yadda mu kai da Deeni kan sunayen yaran. Ta girgiza kanta tace, "Manta da shi duk sunan da Uwa take kiran yaranta da shi to ba shakka shi ne ke bin yaran don haka ki za i sunayen zamani masu da i ki dinga kiran yaranki da su, sai an wayi gari idan ba makaranta ba babu wanda zai san asalin sunayen yaran." Hajjo dake zaune ta gyara zama tace, "Kai anyi wal uba yaron nan Deeni, amma ai idan yasan wata bai san wata ba, shin akwai masu yin sticker ta haihuwa nan garin? Idan akwai a kira min shi ya zo ya yi wa yaran sticker ya sa masu suyanen da ake so sai inga ta iskanci." Nan da nan kuwa Maman Khairat ta kira mai masu hoto ta tambaye shi yace ai yana yi anyi sa'a kuma yanzu zai je fitar da wata don haka bari ya zo ya ha a sai ya kawo ta yanzu insha Allah. Mai hoto ya zo ya yi wa yara har ma muma akai mana ya tambayi sunayen yaran da za a saka na gaya mai Safiya ya saka mata nickname in (Afnan) A'isha kuma yasa mata nickname in (Afnah) kowa yace kin yi daidai kuwa Jiddah sunaye masu da i irin na an boko kuwa. Wajen sha biyu aka shigo da Tumaki guda biyu na yanka ba laifi suna da an girma, Hajjo ta dube ni tace, "Shin anyi wa Haidar yanka kuwa daga baya Jiddah?" Kaina na girgiza nace, "Ba ai ma shi ba Hajjo." Ta muskuta ta fiddo ku i masu dama ta ba Maman Khairat tace " irga min nan ki ga ko nawa ne ki ba mijinki a nemo min rago a ha a ai ma Haidar yanka bako aya." Dubu ashirin da biyar ne cif cewar Maman Khairat. Ta mi e kuwa ta fice zuwa aiken Hajjo. Ba a wani jima ba sai ga uban rago mai girman gaske an kawo, ba kunya sai Deeni ya kira Ni wai zai kama tunkiya guda ya saida tunda ga wani rago ya gani. Na kada baki nace ai Ragon na Hajjo ne zata yanka ma Haidar tunda ba ai mai yanka ba. an tsura min ido, "Da gaske Hajjo ce ta bada ku in Ragon?" Cike da warin gwiwa na tabbatar ma shi da haka ne. Ya ja tsaki, "Waccan tsohuwar na shigar min hanci Wallahi." Sanin zai iya fa in abin da zai sosa min rai yasa na bar gun na koma gun mutane aka ci gaba da harkar arzi Ana ta taron suna Deeni ya aiko na bada an ciki da abincin suna akai ma shi. Na gayama Maman Khairat a zuba mai, ta dube ni tace "Ya bada wani abu ne bayan Tumaki? Nace a'a bai ba da ba, amma idan ba a kai mai ba yana iya zuwa cikin mutane ya yi min tujara. Tace "Allah Ya sawa e! Ta samu manyan kuloli ta zuba komai ta ba yara su kai sai Hajjo ta hango ta kuwa ta so tace, "Ina za a kai wannan abincin?" Maman Khairat ta gaya mata yadda mu kai. Hajjo ta ja tsaki tace ma yaran "Maza ku kai abincin gidan mahaifiyarta kuce "Ga shi nan in ji ni taba nata mutanen." Ga kawo Naira ari taba yaran ladan aike. Suka kuwa tafi suna murna. Hajjo ta auki farar leda ta tsinci an hanjin rabin laida ta ulle ta ba wata yarinya tace maza ta kaiwa Deeni tace ya bada ku in magi da man da aka sakama naman, abinci kuwa muna jira ya kawo a dafa mai." Hatta hantar cikina sai da ta ka a don jin abin da Hajjo tai ma Abban Haidar, amma ya zan dole na shige aki gun mutane ina jiran amsar da Deeni zai maido. Mai hoto kam ya cika al awari sai ga shi ya kawo nan take akai ta ba mutane, kowa nata yaba sunayen wai na an gayu ne. Shiru-shiru Deeni bai sake aikowa ba, tun ina tsammani har na daina, abin ya ban mamaki sosai, domin na auka sai ya zo da kanshi yayi ruwan rashin mutunci amma shiru. Bayan taron suna ya watse aka fito da duk abin da na samu tas. Hajjo ta dube ni tace, "Iyayenki sun bada dubu hamsin na kawo maki sunan a wajena, sannan Uncle Salim inki ya bada kayan abinci yace a kawo maki, amma ban kawo maki su nan ba, domin an gaya min yadda mijinki ya sace wa ancan kayan abincin ya saida ya amshe ku en ya kashe ya barki kina ta gararanba ba abinci ba sana'a. To wannan karon yadda na zo da ku in nan da su zan koma Kano, amma bayan kin gama wanka yaranki sun yi wari ki shirya ki je Kano zan kai ki kasuwa ki yi sarin kaya ki dawo ki ci-gaba da sana'arki Jiddah kin ga dai wannan karon yara biyu Allah Ya azurtaki da samu, zama ba sana'a ba naki bane ba, bin makwabta neman abinci ba naki bane ba, Jiddah ki zama jaruma, ki zama tsayayyar mace wadda zata ji da duk matsalolinta wadda zata tsaya kan afarta akan duk wasu bu atunta, kinga dai yadda Allah Ya juya lamarin Mahaifiyarki ya kaita inda ba da i inda take fama da kanta to bai kamata ba ace Uwa kwance a kwance ba, ya kamata ace kin zama jajirtatta wadda za ki share hawayenki ki share na Mahaifiyarki Jiddah." Nayi na'am da shawarar Hajjo kamar yadda kowa gun ya yi na'am da ita, nayi godiya sosai nace ai ma iyayena godiya suma. Hajjo ta sake fiddo waya mai kyau tace In ji Uncle Salim na kaima Mahaifiyarki tata ita ma tare ya sai maku yace akwai lambarsa a ciki ko da kina bu atar kiransa." Allah Sarki Uncle Salim! Yana matu ar tausayina yana min abin da mahaifina bai min, don haka kallon mahaifi nake ma shi ko da yaushe. Yau sam Deeni bai dawo ba kamar yadda ya yi a haihuwar Haidar har Hajjo ta kore shi Yau bai zo ba. Hajjo tace ya kyautawa kansa don idan muka ha u sai ya biyani ku in da ya amsa munafikin ." Washegari akai suyar nama aka gama aka fitar dana gidansu Deeni dana gidansu Babana har da na Babana kanshi sannan aka fitar dana Deeni suma kowa ya auki nashi aka fitarma da Mamana da nata. Ba laifi an aje min nama mai yawan gaske, suka aga gadona suka saka aka aje marar yawa a fili saboda Deeni. Sai da suka gyaramun komai na gida suka tafi Hajjo ta ban dubu goma tace na ri e a hannuna ko da zan nemi wani abu, kayan abincina kuwa za a dinga aiko min daga gun Mamana duk bayan lokaci. aki na shige na tasa yarana gaba ina kallo Haidar na zaune nata wasa, Abban Haidar ya fa o gidan. Kallo guda nai mai na kauda kaina na bishi da sannu can cikin ma oshina don har ga Allah ban san kallon fuskar Deeni yanzu wata muguwar tsanarsa ke bijiromin duk lokacin dana sauke idona kan shi. "Ke wai me kike nufi ne da aka hanani abincin suna jiya kuma baki ce komai ba? Me ya hana ki sa akai ma Safiya ita ma? Wallahi Jiddah idan kika sake sai na baki