Sashe 40
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
a jikinsa kawai hidimar aurensa yake bai tsaya bi ta kan haukanta ba, nan da nan ya tsira akin amarya cike da farin cikin cikar burinsa na samun wadda zai dinga farin ciki da rayuwar jin da i da ita watau Hafsat. Cikin ikon Allah akai auren wanda ba irin tashin hankalin da Maryam ba tai ba, har barazanar zubar da cikin dake jikinta tayi amma ya yi mata ko'in kula, da taga ba Sarki sai Allah ta shafa ma kanta lafiya. Amarya Hafsat ba laifi tana da wayewa amma sai dai sam bata da kunya abu ka an tana iya dan ara mai zagi, bata jin shakkar gaya mai kowace irin magana, idan ya tanka mata nan take zata kwashe kayanta ta nufi gidansu tayi yaji sai ya bita. Ga shi Allah Ya ora mai masifar son Hafsat, duk yadda take ci mai mutunci take gara shi hakan bai hana shi sonta. Ga shi Maryam ta haihu amma sun kasa zaman lafiya koda yaushe suna cikin masifa da fa a da juna, abin takaicin kuma kowace laifinsa take gani domin gani take yana bayan waccan ne bai bayanta. Baki aya komai ya yi mai tsaye ko da yaushe cikin tashin hankali yake a gidansa, abin da ya kai su da ba mai ganin kowa da mutunci a tsakaninsu. Ban basu daraja shi kowacce kanta kawai ta sani, basu damu da yadda yake fa i tashi kansu ba, ko da yaushe cikin damuwa yake baki aya gurinsa ba wanda ya ci ka na rayuwar aure kullum sai an zo rabon fa a gidansa, ko kuma ko da yaushe iyaye na gidan yin sasanci. A haka dai itama Hafsat ta samu nata cikin wanda ba abin da ya ragu na fitinar da ake cikin gidan sai ma abin da ya yi gaba. Ko da yaushe cikin zullumi da tunanin yadda zai da rayuwar gidansa yake abin da yasa abokansa da dama ba shi shawarar ya ara aure ya aje matar gidanta daban ya barsu can sui ta abun da suka saba shi kuma ya nema ma kansa wadda zata kula da shi. Ganin kamar hakan mai ullewa ne yasa wani abokinsa nema ma shi yarinyar makwabtansu mai suna Badiyya cikin lokaci ka an akai komai sai dai matsalar da aka samu ashe Badiyya bata son shi kawai ta aure shi ne don cikar wani burinta. Lokacin da ta fahimci burin ba zai cika ba sai kawai ta fito da munanan halaye masu ciwo ita ma ta dasa daga inda su Maryam suka tsaya. Badiyya bata damu ba don ta kwashi anyen abinci ta kai gidansu ko ta saida ta kashe ku in, sam bata da tausayi ita kawai burinta a bata ku i ne ai mata hidimar ku Zuwa lokacin Maryam da Hafsat kowace ta tara yara don haka hidimar tai mai yawa ga rashin kwanciyar hankali ga hidimar gida ta mata uku da yaransu domin itama Badiyya ta haihu. Suna a haka ne Hafsat ta cika jakarta da kaya ta watsar da yaranta tace dole sai ya sake ta, ga shi yana masifar sonta duk abin da suke mai a cikinsu babu wadda zai iya rabuwa da ita domin baki aya so yake ya shafe tabon da mutane ke mai na cewa bai iya ri on aure, saboda babu wadda saki bai ratsa a tsakaninsu ba da ita. Mutane ba ruwansu da tambayar ko jin gaskiyar magana kawai sai suka yanke mai mummunan hukunci na cewar bai ri on aure wasu ma cewa su ke zagi da dukan mata yake bayan bai ta a dukan mace ba sai maida magana idan suna yi mai rashin kunya. Saboda mutane ne yasa bai da burin ara sakin kowace mace daga matansa wanda hakan da suka fahimta yasa suke gwara mai kai tamkar wani majaujawa idan wannan ta yi yaji ta tafi gidansu ya samu ta dawo sai waccan ta tafi nasu gidan. Yanzu haka Badiyya ke gidansu mahaifinta ya tabbatar mai da cewa ba zata sake komawa gidansa ba, haka itama kullum sai ta kira shi a waya ta gaya mai magana mai ciwo akan ya sake ta ko tai mai rashin mutuncin da bai ta a zato ba...yana cikin lamarin ne kuma Jiddah ta fa o rayuwarsa a karo na barkatai. Ajiyar zuciya ya saki lokacin daya dawo daga duniyar tunaninsa. Yanzu kuma ya kasa gane inda ya nufa tabbas yana son Jiddah amma bai san matsayinta ba tana da aure ko babu. Mu ha u a kashi na gaba. Taku a kullum Haupha [8/6, 11:00 AM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa