Sashe 125
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ji ana maganar shi ya saima Jiddah komai na akinta. Ko kallo bata ishe shi ba, saboda ba ta ita yake ba, shi baki aya hankalinsa yana kan Jiddah jin amshin turaren ta yake a hancinsa, hasko yadda take lafewa jikinsa kawai yake a idonsa tana wasa da gemunsa ko ma allan gaban rigarsa, ko kuma ta dinga jan hancinsa tana cewa yafi nata bata yadda sai sun yi musaya. (Irin abin da matanmu su kai sake kenan yanzu, baki iya shigewa jikin mijinki ki yi duk wani kalar karuwancin da zai birgeshi ki koma aramar yarinya a gunsa ki dinga wasa da abubuwa da dama na jikinsa kina yaba kyansa kina arawa hakan ba aramin so da sha uwa yake arawa ba sannan ko baki nan zai dinga tunawa dake komai yake kina cikin ransa zai dinga sauri duk inda ya je don kawai ya dawo gunki ki dinga saka shi nisha Ganin ya i kula ta yasa ta fara zage-zage, sai alokacin hankalinsa ya dawo kanta, ya nuna mata ofa ta bar mai aki, amma kamar ya sake tunzura ta ma sai ta cigaba da zagin tana kiran shi mugu azzalumi wanda bai san adalci ba, hakan yasa ya mi e da nufin yabar mata akin sai ta sha gabansa ta ci gaba da aibata shi son ranta, ganin zata fusata shi yasa ya ture ta ya bar akin ranshi a ace. Yana fita itama ta fice kai tsaye kayanta ta ha a ta bar gidan, yana zaune cikin abokansa sai ga kira daga surukarsa akan ya sakar mata yarinya ko ya ji kira daga kotu. Shi daman yasan duk abin da Hafsat ke yi mai da taimakon mahaifiyarta sam ba tai na'am da shi matsayin suruki ba duk irin aunar da yake ma Hafsat a banza bata gani sam, ita burinta ko da yaushe ya sakar mata yarinya shi kuma yana son matarsa don haka ma yake kauda kai daga duk wani iskanci da rainin hankali da Hafsat ke yi mai a zamansu. Duk lokacin da tai yaji bai natsuwa sai ya maidota ba don komai ba sai don shi da gaske yake son ta yana son zama da ita musamman da suka fara tara yara da ita, da farko bata biyewa mahaifiyarta amma daga baya sai ta auki duk wasu shawarwari da uwar ke bata. Hankalinsa baki aya ya tashi don shi mutum ne da bai san damuwa ko tashin hankali don haka ya dawo gidan ya shige akinsa ya rasa abin da ke masa da i sam. Sai ga Maryam ita ma ta shigo ranta ace tai tsaye tana are mai kallo cike da takaici tace, "Wallahi ka ji kunya, kuma insha Allah sai ka ga abin da kai ya dawo kanka. Shi ne tsabar rashin adalci ka koma ka tare jikin mace kana mata hidima ka bar mu nan ba komai sai kace ba aurenmu kake ba." Baki aya so suke su saka shi ciwon kai, ko da yake har yaushe ma tun kiran wayar Maman Hafsat kan shi ke ciwo ita ma gata ta zo da nata rashin mutuncin. Jiddah sai kiransa take ya agawa ta turo sa o fiye da biyar shima sai dai ya bu e ya aje wayar kawai bai san me zai ce mata ba. Ita ma Maryam haka ta are nata rashin mutuncin bai tanka mata ba, saboda bai san itama ta nufi nasu gidan ace kuma ya kora su daga yin aurensa. yar ya je sallar magrib yana fitowa sai ga Yayan Hafsat gabansa ya tabbatar mai da cewa ya ba anwarsa takarda don ba zata koma gidansa ba aurensu ya are. Duk lokacin da aka ce aurensu ya are sai ya ji kamar an caka mai mashi a ahon zuciya yake ji. Shi fa yana son matarsa yana son zama da ita don haka ba zai sake ta ba duk yadda za ai ba zai basu takarda ba. Har dare bai san ya zai ba, ga Jiddah ta dame shi da kida da turo sa o shi kuma ko guda ya kasa maida mata amsar sa onta balle ya aga kiran da take mai. A daddafe ya je gun abokinsa Ali angote ya ce ya raka shi gidansu Hafsat in ya basu ha uri ta dawo gidansa don ba zai iya sakinta ba yana son zama da ita. Suna zuwa aka bar su zaune falon gidan ko yaro ba wanda ya le a suka gaisa har wajen awa guda don har Alin ya gaji ya ce ya tashi su tafi amma ya ce shi sam ba inda zai je sai sun fito ya basu ha uri ya kuma gaya masu gaskiya kan abin da taji arya ne ba gaskiya ba. Bayan uban zaman da su kai ne sai ga Mamarta ta fito a fusace ta zauna ko gaisuwar da suke mata bata samu damar amsawa ba sai tambayar ina takardar yarinyata da ta jefa mai. Kanshi a asa cike da ladabi ya ce, "Mama don Allah ku yi ha uri wallahi ba haka bane ba, taya za a ce Ni nayi wa Jiddah kayan aki? Ba Ni nayi mata ba Allah kuwa Mama duk sharrin mutane ne da son ganin an yi tashin hankali kawai a tsakaninmu." Baki ta ta e ta kira Hafsat in da arfi, sai ga ta, ko kallon inda yake ba tai ba, ta samu waje ta zauna kawai tana kallon Mamar. "Wai kin ji ya ce ba shi ya yi mata kayan ba." Cewar Mamar Hafsat kenan tana watsawa Hafsat in harara. Kwance take kan gado ta rufe idonta tana jin saukar hawaye a idanunta amma sam bata damu ba, babban burinta shi ne meke faruwa da Prince ne haka? Tunda ya fice take kiransa bai auka ba, ta tura mai sa o ba amsa anya kuwa lafiya yake? Gabanta ya sake fa uwa ta sake aukar wayar ta kira lambarsa sai kawai ta ji ya kashe wayar. Zaune ta tashi ta dafe irjinta dake bugawa, tabbas ta fahimta kawai bai san kiran da take mai ne, tunda ya kashe kiran yanzu alama ce ta duk sa o da kiran da take turawa duk yana gani bai da lokacinta ne kawai. A hankali ta fara zagayen akin domin tunanin ko abin da tai mai kafin ya fita ko kuma daga zuwanta gidan zuwa yanzu? Tas ta tuna komai, ita dai bata ga abin da tai mai ba, tana arin inganta zamansu ta hanyar kulawa da ba shi duk wani ha insa to a ina ta rago shi ne ? Me yasa ya za i ranakun cin amarcinta ne ranar da zai fara yi mata sauyin yanayi? Ko dai bai same ta a yadda yake son mace ba? Ma'ana ko dai ita in bata gamsar da shi bane ba? Tabbas ba zata ce ya daina son ta ba amma dole akwai abin da ke faruwa ko ya faru a tsakaninsu, sai dai bai kamata ba koma miye ba ace ya auke shi da zafi haka ba, ya manta duk irin al awarin da sukai ma juna ne? Ya manta shi ne cikar farin cikinta ne? Ya manta nan shi ne aljannarta ta duniya sai ya bu a mata zata ji da inta? Kuka take sosai tana zagaye akin tana kiran wayar yana katse kiran. Ganin har dare ya yi bai dawo ba kuma bai amsa kiranta ba haka zalika bai turo mata sa o ba ko da na hujjar katse mata kira da yake sai ta samu a hankali tai wanka tai sallah ta jawo Alkur'ani ta ci-gaba da karantawa idanunta na zubar hawaye. Ta jima tana karatun sannan ta aje ta koma falo ta lafe cikin kujera abar tausayi ta fara tunanin. Dama haka Allah Ya addara mata rayuwar aure cikin matsala da damuwa ita kenan a rayuwarta? Kenan ba za ta dai ji da in rayuwar aure yadda take so ba kenan? Me yasa Prince zai mata haka tun yanzu? Me yasa ya kasa ri e ko da al awarin sati ne kafin ya bayyana mata waye shi? Cikin muryar kuka take cewa, "Ya Allah kaga halin da nake ciki, ina neman auki daga gareka, ina neman rangwame daga gunka, Ya Allah ka azurta zuciyar mijina da adalci ka wadata shi da halayen kirki kai mai sadakar karamci ka ba shi ikon zama da mu cikin aminci ka ara mai bu in alheri kasa ya gama lafiya." Kuka take tana nanata addu'ar a bakinta har zuwa arfe goma na dare ba Prince ba labarinsa don haka sai kawai ta takure a cikin kujerar tai lamo. Ba yadda bai ba kan tai ha uri amma Hafsat tai biris tace ita fa ko zata koma to sai ya bata wani abu tai gyare-gyaren akinta, duk da cewar ya basu nasu kason don su yi gyaran amma haka ya sake bata wasu masu dama har ma da Mamarta sannan suka tafi yana ara neman alfarmar ta koma gidan washegari tunda tace ba zata bi shi ba yanzu, sai kuma ta ta e baki tace "Idan ka zo gobe arfe shida na safe mu tafi idan baka zo ba zan yi tafiya ta garinsu Mama na huta." Ta kwashe ku en ta shige aki ita da Mamar suka bar su nan zaune. Zuwa lokacin karfe sha aya na dare don haka Ali angote ya gama fusata ko magana bai iya yi mai ba, kawai gidansa ya kai shi ya wuce na shi gidan. Yana turawa gidan ya bu e ya yi mamaki, domin ya auka ta rufe gidan, amma sai ya ganshi a bu e duk da daren da ya yi. Tana kwance falo ya wuce ta ko kallonta bai ba, kai tsaye akinsa ya nufa don bai san magana ko da yake bai san me zai ce mata bama idan tai mai maganar don haka ya za i shigewa akinsa ya rufe kawai ya kwanta. Kiran Hafsat ne ya shigo wayarsa da sauri ya auka don jin me ya faru kuma. "Har ka isa gidan?" Tace cikin muryar ko in kula. "E na isa harma na kwanta yanzu haka." Ya amsa mata da muryar ban tausayi. "Ni dai na gayama goben idan baka zo da wuri ba Allah sai dai ka iske yaranka