← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 133

Sashe 33

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ku i wasu kuma idan an kawo aka iske Abban Haidar bai ban sai ya kashe,sai dai idan naje bin bashin ace an kawo min suna hannun maigidana, idan na zo nayi mai magana bai tankawa shike nan ku in sun wuce Ni ba zai ta a ban su ba. Dana gane sai ya kasance duk wanda zan ba kayana sai na gaya mai idan zai ban ku i hannu da hannu zai ban kar aba Abban Haidar ku ina. Mutane da yake ba a iya masu nan wasu su kaita gulmata wai ban iya ba shi ko sisi ban iya sakar ma sa dukiyata yana mijina kaina kawai na sani sai yarana. Ni dai idan ana gaya min dariya kawai nake domin nasan shi yasan ina yi ma shi yadda ya kamata bai ta aukar shadda ko yadi ya biya ku in ba, haka duk wanda ya kawo ya sai kaya shi zai je ya amshi ku in bai ban su. Maganar abinci kuwa dama ya daina kawowa sai dai idan ya iske na yi ya auka ya ci har ya fitar majalisa. Ganin ku in kayana sun yi asa sosai sai na je gun Mama mu kai shawarar na sari hatsi da ku in na aje idan lokacin saidawa ya yi sai na fitar in samu ku in cigaba da sana'ata. Haka kuwa akai na sari waken suya da ku in duka na adana su a gidan Mama saboda ban san a samu matsala don sau hu u ina siyen tumaki yana saida min hatta kaji bai barinsu saidawa yake don haka na aje su can bakina alaikum. Ban san ya akai ba ashe Abban Haidar ya je gun Mama ya ce mata, ta ba shi rancen ku i zai siyi takin noma ya samu gonar da zai noma. Ita kuma tace mai bata da ku i amma ga waken matarka nan tunda duk abin aruwa ne ai ka auki buhu biyu ka saida ya isheka sai ka sai takin yafi ace a je wani waje neman rance. Nan da nan kuwa ya auki buhu biyu ya je ya siyar ya kama bushasha da ku in ni dai naga sai ya zo da lemu yana sha, ko ya zo da tsire yana ci ga fura mai madara yana zuwa da ita kullum, abin takaicin bai ba ko yaran dake kallonsa haka zai zauna ya cinye ko ma miye ya shigo da shi, sai dai duk yaron da ya kalle shi sai ya zage shi. Bayan wani lokaci kuma ya ha a baki da wani abokinsa ya je ya iske Mamarmu ya ce mata, ga Deeni can an rufe kan ku i Naira dubu arba'in ya ranta ne ya kai ma wani mutum da yace zai samar ma shi aiki ashe an damfara ne, nan dai Mama tace a ida kwashe waken a saida a je a biya ku in a fito da shi, duk ba abin da na sani sai da na je da niyyar aukar wake a saida sannan take gayamin yadda akai, tace ai ta auka ya gayamin komai ai shi yasa ban mata maganar ba tunda na sani. Kasa magana nayi kawai nace Allah Ya kyauta na dawo gida na rasa abin da ke min da i, ga shi na kasa daina tuna abin a raina kuma na kasa yi mai maganar sai dai na zauna nayi ta tunanin banza a raina. Haka na tafi rayuwa tai min zafi na koma tamkar ban ta a kama ku i ba, komai ya tsaya min wahala ta dawo sabuwa dal ga yara sai wanda ya ga Allah yaga Annabi kawai ke taimaka min. Don ma Maman Khairat na tsaye kaina da yarana yasa nake samun sau in wasu abubuwan, amma duk da haka sai da takai ga hatta sabulun wanki dana wanka ya gagareni. Ganin wahalar tai yawa Maman Khairat tai ma mijinta magana ya samar min aikin polio duk wata ana biyana ku in aikin, duk da ba cikin gari nake zuwa aikin ba ban damu ba murna nake domin duk sanda mu kai aikin ana ban kudin abinci dana mota dasu zan sai sabulun wanki dana wanka har na saima Mama itama a ciki. Cikin ikon Allah sai na fara samun sau in wahalar rayuwa, sai abin da ba a rasa ba. Duk da haka na kasa manta abin da Deeni da Safiya su kai min, ko da yaushe na tuna da abin sai nayi kuka haka sai naji tsanar Deeni fiye da baya a raina. Ban sani ba ko hakan yasa ma baki aya sha'awata ta auke oho, Ni dai nasan ba abin da na tsana a rayuwata irin daren da Deeni zai neme Ni sai naji kamar na kashe kaina na huta sam ban jin da in abin har ya yi ya gama ina hawaye wanda na lura shi baima san ina yi ba. Lokacin ne hawan jini ya takura min sosai, ga ba waya tsakaninmu da Hajjo da Uncle Salim tunda na saida wayata na ajiye sim card in Deeni ya auke shi daga aro yace min ya fa i, itama Mama ba waya gunta ya je ya amsa daga aro bai maida mata ba, don haka ban da labarinsu basu da labarina daman jira nake na saida wajen na ha a ku en na koma Kano sarin kaya sai naje can to ga yadda akai da waken babu shi ba ku in duk Deeni ya salwantar da shi. Duk lokacin da ciwon zai kwantar da ni sai dai mutanen unguwa su ha a ku i masallaci su sai min magani ko a kai Ni asibiti amma ba ruwan Deeni da ciwona ko sannu bai iya yi min idan ban lafiya. Sai ta kai ma idan an siyo min maganin yana auka ya je ya saida saboda suna da tsada maganin hawan jini, arshe suma an unguwar suka watsar da lamarina ko ban lafiya iyaka ai min sannu kawai sai masu dama ke aiko min da abinci idan sun girka da rana ko dare. Ina a haka na daure na shiga adashe na ku i Naira dubu biyar duk wata, saboda duk wata idan mu kai polio ana bamu dubu shida da ari shida, ganin halin da nake ciki ne aka ban kwasar farko -farko don in samu abin da zan tsaya da afafuna, ranar da aka kawo min ku in Deeni na kwance cikin aki ashe yana ji na irga ku i Naira dubu tamanin cif na zari dubu biyu nace ma Uwar adashen ga shi ladar gurbi tace Wallahi ba zata amsa ba, nayi-nayi da ita ta i amsa nayi godiya na tashi na rakata. Na dawo ina tunanin me zan da ku in wanda zan samu, har dai dare ban samu matsaya ba, don haka nace gobe zan je da su gun Mama mu ji wace sana'a zan fara da su. Ban saba makara ba sallar asuba amma Yau sai na makara, na tashi da sauri nayi alwala na fara sallah kenan naga Deeni ya fice da sauri rataye da jaka a kafa arsa, sai da na gama sallah nayi lazumi na sannan na fita tsakar gida na gama shara da wanke-wanke na dawo na gyara akin na kammala komai nace bari na auko ku in na irga sai na auki dubu na siyo fulawa nayi mana wainar fulawa, ku i suka ce auke mu inda kika aje mu. Abu kamar wasa na duba ku i basu ba labarinsu kaf akin, ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba, tabbas Deeni ne ya kwashe ku in ya fice tunda asuba. Cikin sauri na zari hijabina na rufe gidan yarana na barci na nufi gidansu Deeni ko zan iske shi ya je kalaci don can yake zuwa duk safiya yana karyawa mu ko oho. Ina zuwa muka gaisa da mutan gidan na tambaye su ko Abban Haidar ya zo, suka ce ya zo ya yi bankwana wai ya tafi yawon duniya na wasu kwanaki. Juyowa kawai nayi na koma gida, ina jin ya zama tilas na bar Uwata nabar yarana nima na bishi yawon duniyar. Ina kuka ina ha a kayana na gama na ulle a zani na dubi yarana nai masu kallon arshe na fice daga gidan. To masu karatu ko ina Jiddah zata je? Ina Deeni ya tafi da ku in Jiddah? Taku a kullum Haupha [8/4, 8:58 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 33 · 0% Book details