Sashe 117
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta zaune su ka gaisa kamar yadda suka saba, sai Bilkisu ta kalli Jiddah tace, "Kin ban mamaki awata ban ta a tunanin za ki yi min haka ba sai ga shi kin yi min." Jiddah ta dube ta da kallon rashin fahimta tace, "Bilkisu ban gane ba me kike nufi da hakan?" Tai dariya tace, "Yanzu ace kina soyayya da ma wabcina amma ko da wasa baki ta a gayamin ba?" Bilkisu tai murmushi don ta fahimci inda maganar ta nufa yanzu don haka sai tace cikin murmushinta "Au don zan soyayya sai kuma na gaya maki ashe? Na auka kin bari ai sai anyi bikin ban kawo maki kayan auren ba sai ki yi min mitar nayi aure ban gayyace ki ba." Ko da taji amsar Jiddah sai ta wayance tace, "Abin ne yaban mamaki Jiddah da Mustapha na soyayya wai." Jiddah tai dariya tace, "Bamu dace da juna bane ko yafi arfina Bilkisu?" Tana ya e tace, "Kai haba Ni na isa nace haka? Ai nasan idan ke baki ce kin fi arfinsa ba shi ba za a ce yafi arfin ki ba." Jiddah ta sake duban fuskar wayarta tana kallon hotonsu ita da Prince in tace, "Kin san shi aure HA IN ALLAH ne don haka Ni da shi HA IN ALLAH ne kawai ko Ni ba zan ce maki ga rana ko lokacin da na kamu da sonshi ba." Sai ta yamutsa fuska tace, "Amma dai kin yi dace don kun dace sosai ya huta da ba azanta da rashin godiyar matansa ma ai." Jiddah ta murmusa tace, "Wannan kuma daban kowa kansa ya sani Ni ban san komai ba sai soyayyata da shi kawai mantawa nake da wasu matansa ko wani hali na gidansa." Ta mi e ta gyara gyalenta tace "Zan tafi akwai inda zan je dama shigowa nayi mu gaisa kwana biyu ba a ha u ba." Tana maganar tana tafiya don haka bata damu da kiran da Bilkisun ke yi mata ba kawai tafiya take abinta tana murmushi. Yana zaune ya sauya kaya sai amshin nan nashi yake ya cika ko'ina da amshi suka dubi juna suka saki murmushi. "Wow! Prince kaga yadda kai kyau kuwa?" Tai maganar tana kallonsa ta ri e bakinta. Sai ya yi murmushi ya ce, "Ban yadda ba Princess domin ke ce kikai kyau har ma naji kishi ya kamani kada ki wuce wani ya ganki ya ji yana sonki." Sai gardama ta kaure a tsakaninsu kowa na cewa kowa yafi shi kyau har suka auki lokaci mai tsawo suna gardamar har Bilkisu ta fito ta kalle su ta shige gidan Mustapha in ba a jima ba sai ga yaran gidan suna le owa aya bayan aya. Ganin haka yasa Jiddah cewa su tafi time na urewa don za su je yawon soyayya daga can. Suna tafiya suna firar duniya suna ta nisha i gwanin da i, har suka isa inda za su. aramin mamaki mutanen gun su kai ba ganin Barista Hawwa'u Bishir (Dawa)ce zata kara da Barista Alawiyya Bello Gareji ba , nan da nan sai ga an jarida sun rufe su wai ya take ganin wannan shari'ar zata kaya a tsakaninsu kuwa, ko sun manta su in Aminan juna ne wasu ma cewa suke gidansu guda amma zasu yi shari'a tare matsayin kowa da wanda yake karewa?" Dariya tai tace, "Ku dai ku zuba ido ku sha mamaki amma tabbas gobe zamu bayyana don karawa." Daga can suka wuce wajen sha atawa suka dinga yawo kawai cikin gari haka kawai sai wajen goman dare suka koma gida. Da uwar siyayyarsa da ya yi mata, tana kula komai ya sai mata zai siyi wani daban, taji da in hakan don tasan na gidansa ne ya siya ko bai fa a mata ba. Ko da suka dawo sun jima suna fira sannan su kai bankwana tana jaddada mai ya dinga cin abinci don ta gaji da ganinsa a rame ko da yaushe sai ba i yake alamar bai da natsuwa da kwanciyar hankali. Washegari tunda safe ta kira Alawiyya tace ta zo ta auke ta idan zata Kotun. Haka kuwa akai sai ga Alawiyya cikin shirinta itama daman ta shirya suka auki hanyar Kotun suna ma juna dariyar kowa zai nasara? Suna isa suka iske Kotun cike da mutane kowa ya zo don ganin wannan Shari'a ta Aminan juna kuma abokan juna sannan an'uwan juna. Nan da nan an jarida su ka yi masu caaa! Kowa da abin da yake son ji daga bakinsu amma su kai tsit sai murmushi kawai da suke saki. Abubakar ganinsu tare sai da gabansa ya fa i ya tabbatar da cewa ya yi wauta na zuwa gun wadda ya yaudara ya yi ma butulci neman taimako. Bai san cewa bakinsu guda ba ai da bai je ba sam, amma ya mi a komai ga Allah shi ne kawai zai bayyana gaskiyar lamari, sannan ko da ace an yanke mai hukuncin kisa ba zai damu sosai ba tunda Jiddah ta yafe mai kuma yasan yabar baya. Kotu Bayan Al ali ya zauna kotu ta natsu aka sake koro bayanin laifin Abubakar aka tambaye shi ko yana da Lauya? Sai Barista Hawwa'u Bishir (Dawa) ta mi e tsaye ta gabatar da kanta a matsayinta na wadda ke kare wanda ake tuhuma. Barista Alawiyya Bello Gareji ta mi e tsaye ta gabatar da kanta a matsayin Lauyar wadda aka kashe. Shi kanshi Al alin ya jima yana nazarinsu musamman Barista Jiddah domin kowane Al ali yasan yadda ta gurfanar da babban Al ali ara kotun Allah Ya Isa ta ci galaba kansa wanda yanzu haka yake tsare. Yasan Barista Alawiyya Bello Gareji kuma farin sani, wadda bata amsar shari'a ta fa i tunda take shari'a bata ta a fa uwa ba. Mutane kuma sun yi zugum don ganin yadda shari'ar zata kwashe . an jaridu, masu gidan talabijin duk sun hallara don samun abin yaya awa. Barista Alawiyya ce ta dubi Abubakar tace, "Kotu na son ka takaita mata wahala ta hanyar bayyana gaskiyar yadda kai ka kashe ar aikin matarka Aminatu saboda kai mata ciki baka son asirinka ya tonu." Abubakar ya sadda kansa asa yana jin wani aci na damunsa a duk lokacin da akai mai wannan tambayar ji yake inama ace shima ya mutu ya huta da wannan ba ar rayuwar da yake yi?" Barista Alawiyya"Taya kotu na tambayarka amma kai kunnen uwar shegu da ita?" Barista Jiddah "Saboda shi ma yana cikin neman nashi ha in ne da aka tauye kuma yana son wannan kotun tai mai adalci wajen nema mai nashi ha in a cikin wannan shari'ar da ake tabkawa mai cike da son kai da nuna izza da ta amar dukiya." Cikin Al ali ya juya, kar dai Barista Hawwa'u tasan an ku in da A'isha ta maka mai ne yasa take sakar mai magana cikin hikima?" Barista Alawiyya "Ya kamata Lauya tasan inda take ba wajen ka-ce-na-ce bane ba gurine mai girma inda ake ladabtar da wanda ya kamata." Barista Jiddah "Tabbas na gamsu da wannan zance amma ina son Lauya ta sani ban sauka daga hurumin wannan shari'ar ba sai ma ara komawa da nayi cikinta tsundum, don haka ina neman kotu taban damar tambayar A'isha matar Abubakar wanda ake tuhuma." ali, "Kotu ta baki dama za ki iya tambayarta, idan tana kusa sai ta matso." Barista Jiddah, "Na gode." A'isha jin an ambaci sunanta sai da cikinta ya katsa domin duk shari'ar da ake bata ta a tsayawa gaban kanta ba don amsa tambaya saboda bata iyawa wannan na cikin abin da ta gayama Al alin ta ba shi ku i na musamman wanda zai hana ta fita cikin mutane ko da an kira ta, amma ji yanda yai mirsisi ya ce ta bayyana. Haka nan dai ta fita tana cika tana batsewa zuwa inda ake nemanta. Aka gabato da Alkur'ani mai girma aka ce tai rantsuwa zata fa i gaskiyar duk tambayar da akai mata. Tai shiru ta kasa yin rantsuwar sai kawai Barista Jiddah tace a yale ta tambaya ce kawai zatai mata ba shaida ce ba ai. Barista Jiddah ta matsa kusa da A'isha dake tsaye ta ci uban ado har da su unshi ga kitson gashin doshi fal a kanta tace mata, "Ya kike da wadda aka kashe ne?" A'isha cikin yamutsa fuska, " ar aikina ce man." Barista Jiddah, "Shi kuma wanda kike ara waye a gunki?" A'isha cikin nuna gazawa da maganar Barista Jiddah tace, "Mijina ne shi." Barista Jiddah, "A gabanki ya kashe ta ko sai bayan ya kashe ta kika iske gawarta?" A'isha tai shiru kamar bata ji me aka ce ba. Barista Jiddah, "Na fahimce ki ga alama baki wajen bayan ya kashe ta ne kika je gun kenan?" Barista Alawiyya, "Ya mai girma Al ali bai kamata ba Lauya ta dinga jefa mata magana ba a baki wannan babu shi a tsarin shari'a." ali cikin yamutsawar ciki ya dube su duka yaga yadda Barista Jiddah ke wani sakin murmushi sai ya ce a an dake "Barista ki dinga gyara kalamanki kina bakin aiki ne nan." Barista Alawiyya, "Na gode." Barista Jiddah, "Insha Allah zan kiyaye amma ya mai girma mai Shari'a ina son ne naji da bakinta domin ance wa a daga bakin mai ita tafi da ali, "Kotu ta baki dama za ki iya cigaba daga inda kika tsaya." Barista Jiddah ta kalli A'isha dake ta son Al alin ta kalli inda take ya i tace mata, "Kince ma kotu ciki ya yi mata don haka ya kashe ta, to ina shaidar Likita daya bada na akwai cikin Abubakar a jikin Aminatu? Sannan cikin wata nawa ne? Kuma ke da kike matarsa kuma matar gida kina ina har mai aikinki ta samu damar yin lalata da mijinki har ciki ya shiga jikinta?" Sai kotu ta auki ananan maganganun domin wannan ma abin duba ne abin tambaya ne kuma. A'isha cikin masifa tace, "Dalla Malama dakata! Nawa aka biyaki ne da za ki ritsani da wasu banzayen tambayoyi naki marassa kan gado?" Barista Jiddah cikin murmushinta tace, "Suma na lura baki da amsar su, to ina son ki gaya min watan baya kina a wace asar kuma dawa kika je asar me ki