← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 133

Sashe 48

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 28 Cikin matu ar farin ciki maigidan ya ce, "Allah Ya amince cewar Fatima ciki ne da ita, tabbas da nafi kowa farin ciki da jin da i. Maza Fatima tashi mu je asibiti, yi sauri ki shirya." Kasa oye acin ransu su kai, don haka kowacce tace, "Wallahi ba dai ciki a gidan nan ba, idan kuwa ya bayyana sai dai ace a jikina ehe." Shi dai ya kama ni muka nufi sashena, yana ta jera min sannu. Muna zuwa asibitin akai mana maraba, saboda sun san shi sosai ga dukkan alama, nan da nan akai min duk abin da ya kamata, aka ce mu jira minti biyar za a fitar da sakamakon awon da akai min. "Congratulations Alh. Ina taya ka murna, domin Hajiya na auke da ciki na tsawon wata uku." "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Sai da Alhaji ya jera sau uku sannan ya yi sujjada ya ara gode wa Ubangiji, sai kuma ya shiga fito da duk abin da ke aljihunsa yana ba Likitan kyauta. Ni kaina naji da in jin ina auke da ciki duk da cewar ina tantama daman can naga kamar akwai kamar babu saboda nasan yana son haihuwar yasa ban gaya mai ba, kada na sa mai rai akan abin da ban da tabbacin sa. Muna komawa gida muka iske su Hajiya Turai zaune a babban falon gidan, sun yi jigum-jigum kamar masu zaman takaba ko gaisuwar mutuwa. Cikin farin ciki ya dinga aga su aya bayan aya yana masu albishir da an kusa jin kukan yaro ko yarinya a cikin gidan nan Insha Allah. Ba tare da sun ce ala ba kowacce ta fincike daga jikinsa ta shige akinta ta banko ofa da arfin gaske. Bai damu ba, shi kawai ta Ni yake, nan da nan ya ce na shirya mu je na siyo abin da nake son ci da sha, kafin na ji yunwa, bai san ina amai ko da wasa don kada na girgiza mai abin da ke cikina. Tabbas naga farin ciki da gata gun Alh har ya dinga tunamin lokacin da nake da cikin Alawiyya yadda Babanta ya dinga murna yana oki komai ya siyo ya kawo min. Na fakaici idonsa na share hawayen tunawa da Baban Alawiyya da ita kanta Alawiyya da nayi. Amma tabbas idan Allah Ya sauke Ni lafiya zan je na gano Alawiyya na kai masu abin da na haifa. Insha Allah Ni ma zan sake gina zuri'a ba zamu are ba kenan da yardar Allah sai mun fi baya yawa, domin a baya Yayyena hu u duk maza, to insha Allah zan maida su kaf kuma na maida mahaifiyata da mahaifina tare da Ni karin kaina, nasan mu haka kawai zamu taru mu sake tara zuri'a mai yawan gaske. ananan kaya Alh ya kwaso min ba, har fa a nake mai ya bari amma kamar ara tunzura shi nake haka yake nunawa sai da nace mu tafi gida yunwa nake ji sannan ya ha ura da loda kaya mu ka koma gidan. Ba kamar yadda na zata ba, na auka zamu sake iske matan gidan a falo sai naga ba kowa, naji da in hakan don nasan da suna gun dole ai tashin hankalin kayan daya jibgo min. Cikin sauri na fa a sashena ina jin farin ciki, tabbas Yau naji na fara rage damuwa sosai daga cikin tarin damuyoyina. Da kanshi ya girka min abinci mai da i, ya yi min da i kau, don ba ka an na ci ba. Cikin kwana biyu naga tsantsar kulawa daga maigidan kamar yadda naga muguwar tsana daga gun kishiyoyina. A lokacin ne na soma muggan mafarkai masu tsoratarwa da saka razana. Ranar da na fara mafarkin ban mantawa wai ina zaune tsakar gida sai ga wani ba in maciji ya taho da wani irin gudu kuma Ni ya nufo bakinsa a bu e. Ko da naga hakan sai na ruga amma abin mamakin shi ma sai ya biyo ni da gudun, na samu na fa a falo na afka akina kawai sai na iske ba in macijin nan kwance gefen gadona bakinsa bu e idonsa na tsiyayar hawaye bai numfashi. Washegari da zazza i na tashi mai zafin gaske ga ciwon ciki kamar abin da ke cikin zai fito don azabar ciwo. Mafarki na biyu kuma ina,zaune a falo sai ga ba in macijin ya fito daga akin Hajiya Turai da gudu ya nufo Ni jini na zuba a jikinsa, na ruga akina ina shiga na ganshi sai wulle-wulle yake har ya daina motsi. Wannan mafarkin sai da na kwanta asibiti domin ciwon ciki na dinga yi har da zubar jini, ba aramin razana maigidan ya yi ba, don har ya fini jin zafin ciwon ga alama yadda nan da nan ya rame ya fa a kamar wanda ya yi wata yana jinya. Kwana biyu nayi a asibitin amma an kasa gane asalin inda damuwar take komai lafiya a jikina amma jini yana fita wanda an rasa ko na miye jinin. arshe suka bamu shawarar mu koma mu yi na Islamic zai fi tunda su basu fahimci komai ba. Haka kuwa akai daga can ya wuce da Ni gun wani mai maganin Islamic ya yi mai bayani, ya yi min tambayoyi sannan ya ha a mun magunguna ya gaya min yadda zan yi amfani da su muka wuce gida. Masu gidan na zaune kowacce fuska ba yabo ba fallasa muka iske su, sun zube kaji da lemuka kala-kala gabansu suna ci amma ba wani nisha i a fuskarsu tamkar ma dole akai masu na zama cin abincin. Sallamar da mukai ce tasa duk suka watso mana idanuwa, tamkar masu neman wani abu, ganin an cikina daya fara tasowa yasa tare suka ja tsaki suka bar gun ba wadda ta juyo. "Allah Ya kyauta maku Yasa ku yi hankali." Cewar maigidan kenan yana mun wajen zama bisa kujera. Cikin Ikon Allah ina fara amfani da magungunan sai jinin ya auke kuma na daina muggan mafarkan da nake duk dare. Cikina na wata bakwai babu abin da Alh bai siyo min ba duk na asar waje, haihuwar kawai yake jira. Kullum ce min yake so yake na haifi mai kama da Ni, zai farin ciki sosai da hakan. Cikina na wata takwas wata rana ina zaune ina shan mangwaro Alh bai nan an tura shi Lagos wani aiki na kwana uku, babu yadda ban yi da shi ba kan ya je da Ni amma ya ce sam. Na bari sai na haihu sai na je na kai abin da na haifa amma zai je gun su Inna zai kira Ni a kan wayar gidan mu gaisa. Kamar jiran ya tafi matan gidan ke yi, suka dinga shigowa har sashena suna ci mun mutunci suna gaya min ba zan ta a haihuwa ba a cikin gidan nan, idan kuma na matsa to tabbas zan ga abin da zai faru daga Ni har shi abin da zan haifa hatta maigidan zai gane kurensa. Ina zaune ina ta jiran wayar Alh don mu gaisa da su Inna amma shiru sai ga su Hajiya Turai sun fa o, ba aramar razana ba nayi da ganinsu, domin sirinjin allura ne (injection) cire da ruwan magani a hannun Hajiya Turai, gadan-gadan suka nufo Ni , kafin nayi wani yun uri sun taushe Ni Hajiya Turai ta tsira min allurar nan, sai da ta juye ruwan tas sannan suka sake Ni, suka kama dungure min kai suna cewa, "Don uwarki sai ki haihun mu gani ai, ko ba haihuwa ba, to haihun mu amsar maki ita, shegiya mai suffar matsiyatan India." Nan suka fice suna ta shewa suka bar Ni kwance, kafin minti biyu har cikina ya fara yamutsa, nan da nan na fice hayyacina, naku a ta taho min da gasken-gaske, sai kawai naga jini na bin afafuwa na, nishi ya taho da gaske kawai sai jin fa owar abin da ke cikina nayi, kamar a mafarki naji kukan jariri, cikin farin ciki na saka hannu na auki jararin ashe namiji ne, hakan ya yi daidai da sake shigowar su Hajiya Turai akin. Tamkar sunga mugun abu haka suka kwartsa uban ihu har suna rige-rigen zuwa inda nake tsugunne da yaron. Kawai ji nayi an wafce yaron daga hannu na har cibiyar ta tsinke ba shiri ya kuwa yi wani kuka sai aya numfashinsa ya auke. "Ai wallahi ba dai nan gidan ba zaka rayu ba,yaro kai kyan kai da ka koma inda ka fito, don ko zan yawo tsirara sai ka mutu zan samu sa'ida a rayuwata kambu! Cewar Hajiya Tani kenan tana jijjiga yaron don ta gani ko bai idasa mutuwa ba. "Ai ke Hajiya Tani gwara ke da sauran imaninki, to Ni na rantse da Allah duk sanda ta sake aukar ciki a gidan nan ta auki ajalinta sai dai ta haihu a lahira." Cewar Hajiya Turai tana ti a min dundu a bayana, wanda yasa mahaifa fa owa ba shiri. Tsabar rashin tausayi haka suka jefar da yaron gabana suka fice suna shewar jin da i. Daidai nan wayar gidan tai ara alamar ana kira. Da sauri Hajiya Turai ta aga kiran cikin muryar kuka tace, "Wayyo Allah Alh! Fatima ta haifi bakwaini amma babu rai, kuma wallahi Alh namiji ne ta haifa ya koma." Ta cigaba da rera kukanta kamar gaske. Ban san abin da ya ce mata ba, dai naji tace, "Yanzu haka tana wanka Hajiya Tani nayi mata, lafiyarta lau yanzu za a rufo yaron don ya yi kuka." Kalmar kuka da ta ambata tasa nima na ji kukan ya zo min, tabbas kisan kai ne wannan,amma wa zan gaya mawa? Waye gare Ni da zai iya bi min ha ina? Yau ga ranar iyayena da dangina, tabbas da muna tare sai sun bi min ha ina kan wannan zalunci nasan ko shakka babu ba zasu kashe banza ba. Haka suka barni ina ta kuka suka fice, da yar na samu na kai kaina toilet na ha a ruwan zafi ina jin ciwo ina komai na fara wanka na gama na shiga cikin ruwan zafin ina jin tamkar na fice don azaba amma na daure . Bayan na gama wankan na fita na iske su zaune a akin ko su gyara min, haka na
Chapter 48 · 0% Book details