Sashe 25
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ji kukan Haidar ya yi yawa. Haka muka dawo gida jikina sanyi alau ina tuna haihuwar farko da nayi ta Haidar, yanzu abin ya wuce wancan karon ma tunda yanzu tsakanina da shi sai idan yana da bu ata ta ya kawo min ruwan Lipton da biredin naira ari kawai da dare na sha ya biya bu atar shi da Ni ya kwanta sai kuma ranar da wata bu atar ta motsa zai sake kawo min ruwan Lipton da biredin. Shi ma da haka kawai yake zuwa sai da na dinga cewa ban iyawa yunwa nake ji idan ya neme Ni yasa yake kawo min Lipton da biredin. To yanzu ga wani cikin Ni Jiddah ya zan da rayuwata? Haka kullum na kasance cikin ciwo Yau lafiya gobe ciwo. Ga cikin sai ya saka min cin abinci amma ba abincin dole tasa na fara bin gidajen ma wabtana da sunan zuwa a gaisa amma har a zuciyata abinci nake nema idan sun yi an ban in amsa. Ban dai iya zuwa ro on abinci kai tsaye don ina jin matu ar kunya da nauyi. BAYAN WATA TARA*** Cikina ya isa haihuwa, amma ban da kayan jarirai na gwanjo da na samu na siya gun wata ma wabciya ba abin da na tanada, haka gidanma ba komai na ci irin fannin abinci komai babu, haka nake ta rarrakawa har dai cikin ya kai wata tara ban aje ba haka ban ba wani ajiya ba, maigidan kuwa tunda na ba shi takarda ta gwajin cikin da akai min bai min magana ba, ko yace ashe ciki gareki ko ya yi min sannu idan ina amai ko zazza i bai ta a ba, don haka nima na kawo idanu na saka mai kawai muke tafiya a hakan. Ba wata magana ko hira balle wasa da dariya tsakanina da shi sai idan bu atar shi ta motsa kawai zai neme Ni. Ba don nasan cewa ba idan na hana shi kaina ba ina da tarin zunubi ba da ba abin da zai sa na yarda da shi, saboda dama kwata-kwata ban san da in abin ba, kawai ina biye mai ne don na hana shi yawace-yawace, saboda yadda na tsani zina a raina yasa duk rintsi ban hana shi kaina. To tun da na gane yana kula wasu matan sai abin ya ida kubce min baki aya na tsani harkar ban sha'awa ban jin da i haka sai nayi kuka duk bayan ya kusance Ni, sau tari ma yana cikin yi ina kuka saboda baki aya tsanarsa da tsanar harkar ke yawo a jinin jikina. Ranar Talata ina zaune naji cikina ya fara mur awa kafin kace me? Marata itama ta amsa na rasa inda zan sa kaina. Ba zan iya misalta irin ciwon da nake ji ba, ina cikin halin Binta tai sallama da gudu ta koma ba a jima ba sai gata da Mamar Khairat sun shigo. Ganin halin da nake ciki yasa Maman Khairat kiran mijinta da yake yana da mota, kai tsaye asibitin ku i ya nufa da Ni. Awon farko suka ce haihuwa ce amma jinina ya hau sosai ba zan haihu yanzu ba. Mijin Maman Khairat ya je ya nemi Abban Haidar ya gaya mai ban lafiya ina asibiti ya gaya mai sunan asibitin haka aka aika gun Mama aka gaya mata, har Yayarta ta zo amma ba Deeni ba labarinsa sam bai zo ba haka daga gidansu ba wanda ya zo. Har na kwana biyu asibitin ba Deeni ba an gidansu, sai ana ukku na haihu yara biyu duk mata. Cikin ikon Allah sai hawan jinin ya sauka aka sallame mu. Mijin Maman Khairat ya dube ni yace "Gidanki zan kai ki ko gidan iyayenki?" Hawaye suka zubo min. Tabbas da ace ina da gata gidan iyayena ya kamata na nufa tunda aka kaini asibiti kwana biyu banga idon Deeni ba haka ba wani daga gidansu da ya zo dubani amma bayan can ina ne zan nufa? Sai nace a kaini gidansu Babana tunda can ne dole ne Mamana itama yanzu Babanta ya aura mata abokinsa ba jin da in zaman gidan aurenta take ba, duk da bata gayamin amma ina lura da yadda duk ta lalace ta rame ta fita hayyacinta baki aya tamkar ba ita ba. Idan na je ma ha uri zata ban kawai tace na koma akina don haka gwara gidan Babanmu idan suka koran sai na koma gidana... "Fito mun zo." Cewar Maman Khairat kenan bayan mun je ofar gidansu Babana. Yana zaune matasa kewaye da shi, suna ta labari, rabona da shi tun ranar da Hajjo ta kawo Ni daga Kano sai Yau. Har asa na du a na gaida shi, ya amsa ya dubi yaran dake zaune gunsa yace, "Wacece wannan in da take gaidani?" Cikin tsananin tashin hankali na ago na kalli mahaifina ido cikin ido wai nice bai gane ba, nice yake tambayar wacece? aya daga cikin yaran yace, "Jiddah ce fa arka Oga baka gane ta bane?" Cikin ko'in kula yace, "Ai wai Jiddah ce daman? Daga ina haka to? Dama an gaya min kin yi ku i ba a san inda kika samo su ba ma kin kama sana'a ko?" Kasa magana nayi domin ban zaci hakan daga mahaifina ba duk da nasan cewar bai sona amma ban san rashin son har ya kai hakan ba ai. Don haka bance komai ba na mi e da yar ina share hawayena na nufi cikin gidan nabar Mamar Khairat na mi a ma shi yaran na gaya mai haihuwa nayi. Ban san ya suka are ba na shige jikina sanyi alau. Kakata na zaune na shiga tana cin zogale amsa sallamar tai kanta na du e ta ago muka ha a ido, nan da nan ta ha e rai ta cigaba da abin da take, hakan yasa na gaidata ina shirin tafiya Mayman Khairat ta shigo rumgume da yarinya guda Babana auke da guda. Yana washe baki ya mi awa Innarsa jaririyar, "Ashe Jiddah haihuwa tai yanzu daga asibiti suke Inna yara biyu ta haifa duk mata." A kan fuskarsa na fahimci ya ji da in haihuwar don sai fara'a yake, sai a lokacin na an ji dama-dama a raina. Maman Khairat ta gaida Kakar ta cigaba da kora masu jawabin na kwana biyu asibiti ban lafiya an gayama Deeni amma bai je ba haka wani na shi bai je ba, don haka dana haihu nace a kawo Ni nan gidan... "La ila ha illallahu! To idan an kawo ta nan gidan wani abu za ai mata ko ai ma shi ne?" Cewar Kaka data katse Maman Khairat daga maganar da take. Cike da gadara Kakar tace, "Mun ga yara Allah Ya raya amma maza ku tashi ki nufi gidanki akinki idan kin i kuwa ki lalace a banza. Yo wai zaman me za ki zo ma ki yi a cikin gidan nan nace?" Ganin tana ta masifa yasa na mi e hawaye na zuba na kalli Maman Khairat nace mu je kawai. Haka ta biyo ni baya muka fita na shiga motar na ida sakin kuka mai cin rai. Tun yanzu kenan ina ga can gaba? Me yasa wai ban da sa'ar rayuwa ne Ni? Me yasa komai nawa ya fita daban da saura? Har muja je gidana ba wanda ya yi wa wani magana sai mijinta kawai da yace, "Allah Ya sawa e! Bamu jima da zuwa gidan ba mutane su kai ta zuwa ganin jarirai. Maman Khairat ta ban ku i Naira dubu goma tace In ji Babana. Naji da in ku in tunda ban da su haka akwai bu atar su don haka nace ta ri e gunta tai duk abin da ya kamata da su. Ta fice kenan sai ga Abban Haidar ya shigo nasan tunda ya ga mutane ranshi ya ba shi an haihu ne. Ina zaune kan gado ya shigo ina kallonshi ya tsaya yana arewa yaran kallo, amma tsabar girman kai yasa ya kasa furta ko da kalma guda ce gare Ni. "Sannu da zuwa Abban Haidar." Ina dubansa amma sai ya yi shiru kawai, arshe ma sai ya wuce ya auki yarinya aya yana kallo sai kuma ya aje ya auki ayar, ina kallonsa ya fito da waya yana ta aukar su hoto yana murmushi. Ya gama ya sake kaya ya fice ina jinsa yana waya yana cewa matarsa ta haihu an samu yara biyu duk mata. Bai jima da fita ba aka ce min motar icce ta zo, yara su ka dinga shigo da icce nasa ma shi ne ya siyo har naji dama-dama a raina,sai ga Maman Khairat da kaya ni i-ni i yara na biye da ita. Bayan nai mata sannu ta jani inda ba mutane tace, "Jiddah ku in da Babanki ya bada ne na siyo icce na siyo maki kayan abinci wanda za ki ci kafin bakwai sai madarar jarirai don nono kawai ba isar su zai ba nasan." Sai jikina ya yi sanyi kuma, kenan ba daga gun Deeni iccen yake ba ? Tabdijam kenan wannan ma haihuwar kamar waccan zata kasance? Na girgiza kaina ina jin cewar insha Allah na gama haihuwa a gidan Deeni har abada zan are rayuwata da yarana uku. Sai yamma lis an gidansu Deeni suka zo min barka, ban damu ba, domin ba tasu nake ba, dangin mahaifiyata da mutanen unguwa da wanda nake abin arzi i da su tuni sun cika min gida ana ta harkar arzi i. Yayarshi ta ware Ni gefe guda take tambayar wai dame-dame Deeni ya kawo gidan? Nai murmushi nace ban san me zai kawo ba tukun tunda Yau akai haihuwar. Ta fiddo ido waje, "Kai amma Deeni bai ji da in halinsa ba, tunin duniya fa yace ya gama ha a komai ke kawai yake jira ki haihu." Cike da takaici a asan zuciyata nace, "Ba mamaki suna can gidan naku ya aje amma nan bai aje min komai ba." Gabana taita maganganu marassa da i kan Deeni Ni dai ban tanka ba, saboda zuciyata ta riga ta dake yanzu ban jiran komai daga kowa na fawwala Allah lamurrana duka nasan shi ne kawai zai min maganin duk wata damuwata . Cikin dare Mamarsa ta zo taita fa a