← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 133

Sashe 53

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

bakin ofar gidan ya fuskanci akwai matsala. Cikin sauri ya shiga yana waige-waige ya fito da bindigarsa ya ri e yana tsammanin ko da yaushe ana iya kawo mai hari, sai dai har ya shiga cikin akin ba kowa bai ga alamar kowa ba, ya bu akin da yake ajiye mutane ya ga wayam ba kowa ya fasa ihu yana dukan bango. Firgigit ya yi kamar wanda ya dawo daga duniyar tunani, "Ina masoyiya take?" Da gudu ya koma akinta bata nan cikin sauri ya fito da wayarsa ya fara kiran ta, ta jima tana ringing sannan aka auka, cikin ka uwa ya ce, "Masoyiya me ke faruwa ne? Kina ina? Waye ya shigo mana gida?" Wata dariya ya ji wadda ya kasa gane inda yasan muryar, sannan aka ce, "Kai in baka da zarra balle nasara haka zalika dai baka da warin gwiwar yin jayayya da Ni, waye kai a duniyar tantiranci? Wane kambu ka amsa na karramawar kai in shai ani ne? Wa yasan da zamanka a duniyar Ibilisai?" Zufa ta yanko mai, kamar muryar mace kamar muryar namiji wai me ke faruwa da shi ne? Babu wanda yasan gidansa na dajin nan amma an shigo an yi mai arna an tafi da masoyiyarsa har ana masa barazana?" Cike da takaici yake magana a wannan karon, "Ba wani dogon bayani nake nema ba, kamar yadda ba zan lamunci aramin abu ya samu masoyiyata ba, kawai so nake naji waye kai? Wace takun sa a ce a tsakanina da kai da har ka zo gidana na sirri kai min haka? Ina so ka sani ba zan ta a yafe maka ba, kamar yadda ba zan auki wannan tozarcin da kai min ba na shigowa har gidana ka tafi da rabin raina ba... "Sauran yaranka guda biyar ma suna wajena ai Dauda." Aka ara mai bayani daga can angaren. Jagwab ya zauna ya dafe kansa, ya kasa ko da cewa ala daga can ya ji ance bari na baka masoyiyar taka ka ji muryarta ba mamaki ka fi aminta da cewa wannan karon ka shiga inda bai kamata ba ka shiga, ka jefa kanka inda baka iya fitowa, ma'ana kana jayayya da inda ba a yinta kana hauka a inda hankali ke aiki." Cikin kuka Jennifer ke cewa, "Don Allah masoyi kai masu abin da suke so su yale Ni wallahi sun iya mugunta don Allah ka cece Ni ka cece jaririnka dake cikin cikina masoyi." Wani uban ihu ya saka yana cewa, "Don Allah mun zama iyaye masoyiya? Da gaske na kusa zama uba nima?" "Babu tabbas in hakan idan ba bin doka ta kai ba, ka sani a yanzu baki aya a hannuna kake don haka ka natsu ka ji me zan gaya ma, ina son ka gayamin ina yaran Alh. Aliyu suke?" Kamar mai maganar na gabansa haka ya zaro idanuwa, "Yaran gidan Alh.Aliyu ! Tabbas akwai matsala domin an riga an ba da su ga dodon tsafi ba mamaki ma sun gama da shafin yaran tunda jiya aka amshe su." Maganar zuciyarsa kenan. Daga cikin wayar aka sake cewa"Kana iya yin duk abin da za kai na tsawon kwanakin da za ai ana Shari'a amma ina so ka sani duk ranar da ka sake kirana kai min burga tabbas sai na nuna maka wacece Barista Alawiyya a zahirin gaske." Kit ta kashe wayar. Dama haka Barista Alawiyya take? Daman da wannan ce yake waya? Tabbas zai nuna mata namiji yafi mace nesa ba kusa ba, sai yasa ta yi gudun ceton ranta bayan ya hamba e mata duk wani jigo da gata nata. Ta masu karatu ya zata kaya kenan? Taku a kullum Haupha [8/19, 5:53 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 53 · 0% Book details