Sashe 71
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 35 Cike da araji yake fa in, "Wallahi ita ce ! Tabbas ita ce, matata ce Jiddah ita na fito nema, waye ya bata ikon yin wata shari'a?" Mutanen motar sai suka auka ko mahaukaci ne dai, domin tun da ya shigo yake wasu abubuwa kamar na zararre. Shi dai mai waya ya samu ya amshi wayarsa kar da ya jefar mai da ita ya ja mai asara haka kawai don bai ga alamar zai samu ko da rabin ku in wayar ba a gunsa. Wani da yafi kowa son jin kwa ya dubi Deeni ya ce, "Shin bawan Allah da gaske matarka ce Barista Jiddah? Amma kuma kana nan tana Kaduna taya ake zaman aure haka?" Deeni ya ce, cikin muryar kuka-kuka , "Matata ce Jiddah sai dai tsautsayi ne yasa na sake ta, yanzu haka Kano nake da niyyar zuwa don na maidata akinta amma sai na ganta a waya wai ta zama lauya." Wani ya ce mai, "Amma da gani dai baku ta a haihuwa ba ko? Don ba alamar ta ta a haihuwa ma wannan yarinyar." Deeni ya cije le ensa ya ce, "Haihuwarta biyu gidana ta biyun ma an biyu ta haifa duk mata, yanzu haka suna gidansu gun mahaifiyarta ko Yau na gansu da zan taho." Wanda ke gefensa ya ce, "Amma dai kai baka duba ma kanka ba, ai Malam ba a rabuwa da irin wa annan matan duk gumu duk wahala ha uri ake da su saboda su in na daban ne, yanzu ba don ka fa i ba wa zai yadda cewar ta ta a aure?" Deeni ya sadda kansa asa yana jin hawaye na zubowa daga idonsa, tabbas ya zama marar rabo ya tabka uban kuskure wanda yanzu yake son gyarawa amma bai san ta ya zai gyara shi ba sam. Wani saurayi da tun da ya shigo motar bai tanka ba sai yanzu ya ago kai ya dubi Deeni ya yi murmushi ya ce, "Ashe akwai ranar da zaka iya zubar da hawaye akan Jiddah? Ashe akwai ranar da zaka iya tuna Jiddah har ka ji tai maka rana Deeni? To idan mafarki kake ka farka domin Jiddah tafi arfin ka a yanzu ta gama zaman unci da takaici da zaman hawan jini a gidanka. Deeni ina son nayi maka albishir in cewa Jiddah ta zama babbar mace wadda tafi arfin irinka ko ada ba ajinka bace ba Jiddah kawai addara ce da rabon yaran dake tsakaninku yasa aka baka aurenta. Yau Deeni ina ta ama da gadarar da kake nunawa Jiddah? Ina hantara da muguntar da kake nunawa Jiddah? Duk sun wuce nasan yanzu haka Jiddah ta jima da manta anyi ruwanka a duniyar ma." Deeni ya fashe da kukan gaske yana kallon Likitan dake duba Jiddah duk lokacin da hawan jininta ya tashi, daman ya sha ba shi shawara kan yadda yake tafiyar da rayuwarsa da Jiddah amma sai ya taka mai burki ya ce mai kada ya sake shiga cikin rayuwar aurensa ya tsaya matsayinsa kawai. Cike da takaici Likitan ya dinga ba mutanen cikin motar labarin Deeni da Jiddah wanda ya sani da wanda ya ji mutane na fa i. Nan take akai ma Deeni caa a cikin motar har wasu na cewa sakayya ce ke damunsa Allah Ya ara Yasa ma Jiddah albarka Ya bi mata ha inta kan shi, yanzu ya fara ganin bala'in rayuwa ma sai nan can gaba zai tantance miye rayuwa. Wani tsoho ya ce, "Ka gode wa Allah yaro tunda ka haihu da ita darajar yaran ta dinga taimaka maka kai ma ka lashi arzi in yaranka." Likitan ya yi karaf ya ce, "Sai dai idan bai da kunya amma shi da ya dinga fa a gaban kowa bai iya ri e mata yaran tunda ta haifa ta ji da abin ta?" Mazan motar suka saka Salati baki aya suna kallon Deeni daya gama muzanta a cikin motar. Likitan ya jawo wayarsa ya ce, "Bari ku ji ina waya da ita Ni saboda ina duba yaranta da Mamarta idan basu lafiya." Ya are maganar yana danna kira a wayarsa. Da yake handsfree ya saka wayar kowa na iya jin arar ringing in wayar. Kamar zata katse ta aga kiran, "Assalamu alaikum Likita bokan Turai." Yana kallon Deeni ya ce mata, "A kune manya yanzu ai, don yanzu naga wani labari ashe daman da babbar Lauya muke tare ba bayani?" Suna jin sautin dariyarta a hankali tana cewa, "Kai haba ai duk wasu manya bayan Likitoci suke muna bayanku dai mu." Deeni sai ya ji muryarta ta ara wani tarr sai ya ji tamkar busar sarewa haka yake jin muryarta na dokar dodon kunnensa, ashe haka Jiddah ke da murya mai sanyi da za i bai ta a ankara ba duk zaman da ya yi da ita ba sai yanzu. Likita ya ce mata yana duban Deeni, "Sai kuma na samu labarin za ki koma gidan Deeni, nace to bari na kira ki nayi maki Allah Yasa alheri duk da ba a gaya mana ba, mun tsinta a gari ai har ga shi mun kira." Ta ja wata siririyar dariya tace, "Likita kana magana ne kan wa kenan? Ka sa na shiga tunanin inda nasan sunan ma Ni kai tsaye, ko dai kaine za kai aure kake min ta an birni ne?" Deeni ya zaro idanuwa waje, wai kardai ace Jiddah da gaske ta manta da shi a rayuwarta? Shi ya auka tana can tana jiran shi ya je ya ce ya maidata akinta ashe ba haka bane ba? "Kar da ki min haka Jiddah wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba." arfi yake maganar don haka hatta ita ta ji sai dai ko da alama bata auki Muryar mai maganar ba, haka bata ma auka da ita ake ba, don haka tai dariya tace, "Likita afuwan zan an gana da wani bawan Allah ga shi nan yana jirana zan kira ka idan na gama, don Allah ka gaida min su Mama idan ka je gidan." Ya kashe wayar yana cewa "To babbar Lauya ki huta lafiya sai mun yi waya." Nan take sai wasu suka amince da maganar Likitan don haka sai suka ga miye abin tausayawa wanda bai san ciwon kansa ba? Sai kawai kowa ya ja bakinsa ya yi shiru akai banza da Deeni dake ta rizgar kuka kamar aramin yaro. Suna isa Kano kowa ya watse , Deeni ya tsaida abin hawa ya gaya mai unguwar da Mama tai mai kwatance nan ne gidan Hajjo, suka tafi yana ji a ransa ko kwantawa ne ya yi asa zai yi gun ba Hajjo ha uri indai zata ha ura ta saka baki Jiddah ta koma gidansa. Hajjo na zaune tana waya da Mustapha yana bata labarin abin da ya faru, Hajjo kamar tai tsalle don murna wai Jiddah ce gaban jama'a tana matsayin Lauya tana kare wata matsayinta na Lauya! Tabbas Allah ba azzalumin Sarki ba ne ba, daman tana ji a jikinta wata rana Jiddah zata zama abar kwatance kamar yadda ta zama a baya sai dai wannan kwatancen ya sha bambam dana baya domin wannan na alheri ne bana damuwa ba irin wancan ba. Cike da farin ciki Hajjo ke cewa "Yanzu nan Jiddah da kanta ta tsaya gaban Al ali tai magana? Gaskiyar magana zan so ganin wannan rana da idona wadda Auta ya so gani Allah bai nufa ba, ko da yaushe burin Auta Jiddah ta zama wani abu Yau ga shi ta zama bai raye! Hawaye suka zubo mata ta goge don tasan Allah mai iko ne akan komai shi ne ya bata shi ne ya amsa. Shi kanshi Mustapha ya ji ba da i sosai da tuno Salim amma ya za su yi haka Allah Ya nufa sai su gode ma shi kawai. Suna gama wayar akai sallama ta amsa tana ta ara kakka in abin na sauyar Jiddah zuwa Lauya lokaci guda kwatsam. Umarnin shigowa ta bada, don haka Deeni ya shiga yana sake maimaita wata sallamar. "A'uzubillahi minasshai anin rajim! Cewar Hajjo tana kallon Deeni tana ara neman tsari daga shai ani. Cike da masifa ta nuna mai inda ya shigo tace, "Maza-maza ka juya ka koma inda ka fito kafin nasa ai maka shegen duka wallahi. Haka kawai muna cikin farin ciki zaka bayyana gare mu? To Li'ilafi kuraish, wallahi aniyarka ta bika ja'irin yaro insha Allah Jiddah ta gama ba in ciki a rayuwarta." Deeni ya tsugunna asa idonsa na zubar hawaye ya ce, "Don Allah Hajjo ki yi ha uri ki gafarta min laifukan da nayi maki ki saka baki Jiddah ta koma akinta wallahi na sauya halayena yanzu na kimtsu na koma mutumin kirki kamar kowa... "Kai rufe min baki, tsohon munafukin Allah ta'ala! Watau ka ji labarin yarinya ta yi gaba ta samu matsayar arzi i a rayuwarta shi ne zaka kwaso tsumman jiki ka zo da maganar ta koma akinta, to nace Uwaka kai da akin. Tun kafin na kira iyayenta su zo su iske ka suima halinka na rashin mutunci gwara ka bar gidan nan tunda ba naka bane haka ba aika maka akai ba ka zo." Deeni sai kuka yake yana ba Hajjo ha uri abin da ya tunzura ta kenan ta kira Mustapha da suka gama waya yanzu tana cewa "Bari na kira maka ita ka ji daga bakinta tunda Ni ka raina Ni." Mustapha ya aga wayar yana tunanin ko mantuwa Hajjo tai sai kuma ya ji tana cewa, "Kai Mustapha ha a Ni da Jiddah na gaya mata ga tsohon mijinta nan ya zo ya tasa Ni gaba wai ya maidata akinta." Cike da tashin hankali Mustapha ke cewa, "Kamar ya kenan Hajjo me ya kawo maganar maidata akinta a nan kamar bata gama idda ba?" Hajjo tace cikin gatse, "E man ya maidata a matsayin ubanta wanda bai san takan addini ba ko." Cikin damuwa Mustapha ya ce, "Hajjo maza yabar gidan nan kafin nasa a zo a fitar da shi, ko dai yana shaye-shaye ne ya sha ta gaya mai arya