← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 133

Sashe 11

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

don an ce ita zatai min ba su ba. Buki da kwana hu u aka kawo min kayan lefe na daga gidansu Babana wanda ana tafiya na kira Safiya nace ta zo ta za i duk abin da take so a cikin lefen. Bayan ta za a na rufe na aje. Zamana da Deni kadaran-kadahan ban da wayon da zan musa masa ko yi masa ba daidai ba, komi yace ban kaucewa don haka ko da yaushe yake kaini gidansu ko gidanmu yace na yini sai dare zai zo mu tafi gida. Ba yadda Mamana batai ba amma sam ta i daina kaini gidan tace na dinga zama akina amma yace ai shi ke kai ni duk inda na je don haka ba laifi bane ba, kawai bu atarsa idan zan fita ko makwabta ne na ba da ajiyar makullin gidan a aje ma shi. Wata biyar da aurena Allah Ya yiwa Inna rasuwa, tabbas naji rasuwarta sosai domin ita ka ai ce ta ri e ni babu tsana babu hantara balle tsangwama har muka rabu. Damuwa ta farko dana fara cin karo da ita sace kayan lefe na duka aka kwashe atamfofin aka tsince min kayan kicin irinsu kuloli da sauran tarkace, ban damu ba nace Allah Ya kyauta gaba haka ma Mamana tace itama. Ban jima ba na samu ciki, sai dai irin mai wahala ne ko da yaushe cikin amai nake ga ciwo kala-kala ina fama, hakan yasa ban fashin zuwa gun awo duk ranar Talata nake zuwa da cikina ya tsufa amma da farko bayan sati hu u nake zuwa awon. Har zuwa yanzu Safiyya ita ka aice awata abokiyar shawara ta, kullum na fita na dawo sai na iske hijabinta ko gyalenta ko takalmanta ta aje ta auki nawa a tunanina biyowa take idan zata wuce take aje wa tana aukar nawa. Ban ta a kawo ma raina cewar Safiyya cin amanata take da mijina ba sam. Sai ga shi jiya da idanuna na kamata tana cin amanata a cikin gidana ta manta yadda na auke ta da matsayi na fifita ta akan sauran awayena na makaranta na maidata ar'uwata ta jini mahaifiyarta kallon mahaifiyata nake mata, ashe ban sani ba zan wayi gari nayi mugun gani tsakaninta da mijina... "Jiddah don Allah ki daina wannan tunanin ba abin da zai saki sai matu ar damuwa, ki barshi da Allah tabbas zai saka maki domin ya zalunce ki, ita ma zata ga sakayya ai yanzu tun a duniya ake fara ganin sakayya." Maganar Gaje ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin dana afka don haka na share hawayena nace mata zan tafi gida na gaji da zama gidan nan tunda dai gari ya waye rana ta fito. Itama tace tafiya za tai duk da ba yadda ba tai da Ni ba na ci abinci ko na sha koko na iya ba, domin babu abin da zan iya ci ko sha yanzu Ni. Bayan na dawo gida sai abin ya zame min biyu kawai naji ina kewar awata Alawiyya ko tana ina yanzu? Ko itama an mata auren dolen ne? Ko tana can tana karatunta? arshe nayi mata addu'ar Allah Yasa tana cikin aminci a duk inda take. Sai can yamma Deeni ya shigo gidan ko sallama daman bata dame shi ba sai sa'a yake yin sallama, kai tsaye uryar aki ya wuce ko kallo ban ishe shi ba, ya an jima sai kuma ya fito ya sake ficewa ba tare da ya kalli inda nake tule ba da uban cikina ba, wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo min, wace irin rayuwa ce ke tunkara ta? Miye laifina a zaman aurena? Deeni bai ta a nemana na juya mai baya ba, haka Deeni bai ta a sakani abu na tsaya ata lokaci ba, komai ina yi daidai arfina sau tari ma ina ure kaina amma ban nuna damuwa, kawai burina na zauna lafiya da mijina, so nake na samu gatan da na rasa daga iyayena, so nake na samu ancin dana rasa daga iyayena. Tunda akai aurena ban saka Babana a idona ba, haka babu wanda ya zo daga wajensa daga ni sai dangin mahaifiyata kawai nake rayuwata, ina jin ciwon yadda nake rayuwa tamkar marainiya tamkar ban da Uba amma ya zan yi? Wannan yasa nake da burin zaman aurena ya zama shi ne farin cikina mijina ya zama mai share min hawayena mijina ya zama silar dariya a fuskata ko da yaushe, amma taya kenan? Tun asalima daman kallon marar wayau na kula yake min, domin abubuwa da dama idan ya yi min kallonsa kawai nake na kauda kaina ba don ban san cuta ta ya yi ba ko untata min ba, a'a sai don zaman lafiya kawai nake so mu yi, sannan ban da kowa sai shi, shi ne kawai gatana sai mahaifiyata da sauran danginta to su kuma kowa ta kanshi yake babu mai arfi a cikinsu, dama ban saka dangin mahaifina domin su in basu san da zamana ba, ko gidan naje ban jin da in yadda ake nuna min halin ko in kula gabana ake fifita yaran anin Babanmu da Yayyensa hakan na mun ciwo don haka na daina zuwa nake rayuwata cike da tausayin kaina. Yanzu ya zan yi kenan? Tabbas Ina gab da fa awa cikin tashin hankali wanda yafi na baya ga dukkan alama... Sallamar yaron makwabtan Mamarmu ya dawo dani daga tunanin da nake. "Ance a gaya maki Allah Ya yiwa mijin Mamarku rasuwa yanzu." "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Kasa kuka nayi shike nan, tawa ta sake samuna, yanzu Mamana zata shiga cikin unci na gaske kenan tunda mijinta mutum ne mai tsoron Allah yana bakin arinsa kanta har da Ni, ya sha zuwa guna mu gaisa ya ban ku e ya sha kawo min kayan abinci. Allah Sarki ni Jiddah na sake rasa wata damar kenan. Bayan yaron ya tafi na le a don ganin ko zan ga Deeni na gaya mai amma ban ganshi ba, ga shi ina son tafiya kafin a kai shi gidansa na gaskiya, hakan yasa kukana ara yawaita naita zagaye gidan tamkar ina awafi amma ban samu mafita ba, domin dai nasan babu kyau mace ta fita gidan mijinta bai sani ba. Na fi awa uku a cikin tashin hankali sai ga shi ya shigo kunnensa ma ale da abin jin ki a har rausayar da kansa yake alamar kidan da yake sha yana mai da Bayan ya shiga aki na bishi duk da kukana ya kasa tsayawa nace mai, "An aiko daga can gidanmu mijin Mamarmu ya rasu azun daman jiranka nake ka zo sai na tafi." Wani banzan kallo ya watsa min ya ta e bakinsa ya aga kafa a ya wuce ni tsugunne ina tsiyayar da walla. Jikina sanyi alau na tashi na zari hijabina na rufe gidan na tafi gidan gaisuwar ina cike da tunani kala-kala a zuciyata. Lokacin da naje har an rufo shi an dawo, da yar na gaisa da mutane na shige uryar akin Mamana na kwanta na cigaba da rera kukana. Ana gama sallar magrib Mamana ta shigo inda nake ta ta a jikina taji zafi rau, tace, "Ki tashi ki tafi gida kar dare ya yi sosai kinga bake ka ai bace ba, kuma ba a san ana kai wa dare kin ji?" Allah Sarki Mamana ban san tana ina zan kama ba ko da naje gidan dama kin barni na kwana a nan. Haka zuciyata ke gayamin domin ni lamarin Deeni ya wuce sanina ma yanzu abin nashi gaba ya yi madadin ya ban ha uri sai ma ya fito da sabon hali mai wuyar gaske. Ganin ban da mafita na tashi da yar na shirya zan tafi Mama ta aika aka siyo min fura da nono tace na dama nasha kafin na kwanta. Tun daga nesa na hango Deeni tsaye ofar gidan fuska a aure ya tsira min ido tun daga nesa yana are min kallo. Gabana ya fa i cikina ya yamutse kawai naji ban iya aga ko da afata guda don haka na tsugunne a gun cikin mawuyacin hali. Shi kuma Deeni ganin haka sai ya auka wani sabon rainin hankali ne ta zo da shi daga kawai ta iske shi yana har kar gabansa uban miye na ta auki damuwa ta ora ma kanta har ma take wani kukan munafurci zata gane kurenta don ba zai bari ta raina shi ba, ai ba da ku in ubanta yake neman matan ba, idan tace zata kawo mai rainin hankali ita ce a ruwa ba shi ba. Don haka a fusace ya nufi inda take tsugunne rai ace. Mu ha e a page na gaba don jin yadda rayuwar auren Jiddah ta koma. Taku a kullum Haupha [7/16, 4:43 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 11 · 0% Book details