← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 133

Sashe 65

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gare su, ka zama tamkar aramin yaro wanda komai zai yi sai da shawararsu,amma kai ka kasa fahimtar hakan. Musty dole ne idan kana son farin ciki gidanka kaima ka zama farin cikin ma'ana ko da yaushe ka kasance a cikin farin ciki to dole ne ko ya ya kaima zaka samu daga gare su. Mata basu san nuna masu gadara da girman kai,domin tambarin su ne hakan su kawai suka lamunce idan sun yi maka ba komai amma kai kana yi masu za a samu matsala. Don Allah ka dinga ha uri ka daina shiga damuwa insha Allah wata rana zaka samu wadda tai daidai da raayinka tabbas zaka samu ko da bamu tare a lokacin mun yi nisa zaka tuna da na gaya maka, domin ina ji a jikina zakai rayuwar aure tamkar ta India." A hankali ya goge hawayensa ya kalli Jiddah cikin ransa ya ce, "Tabbas ka fa i gaskiya an'uwa, Jiddah ita ce zata goge min damuwata nima ina jin hakan a jiki da zuciyata." Jiddah ta kalle shi sai hankalinta ya koma kanshi tai mamakin ganin yana kuka, ba dai don tana kuka yake kuka ba? Kai ba zai yiyu ba, da dai abin da akai ko kuma wani waro ne ya fa a mai a ido yasa hawaye zubowa daga idonsa, don Hausawa na cewa ido bai son ba i. Da wannan tunanin tai na'am da wani abu ya shigar mai a ido yasa shi hawaye. Ta dube shi a hankali tace, "Sannu, miye ya fa a ma a idon?" Girgiza kanshi ya yi kawai ya share hawayensa bai ce mata komai ba. Har suka isa Kaduna kowa da tunaninsa . Tunda Alawiyya ta kama budurwar Oga Dauda tare da wasu daga yaransa sai ta kira amintattun yaranta ta dam a masu su, sai ta koma gun su Daddy domin tasan komai na iya faruwa da su, saboda ya yadda da hatsabibancin su Hajiya Turai sosai tasan cewa za su iya komai kan lamarin, musamman da suka kasance matsafa to tabbas bibiyarta a gare su ba wani aiki bane. Da sauri ta kira islamiyyar data bu e tace a sauke mata Alqur'ani kuma ai mata addu'a kan shari'ar dake gabanta domin abin ya shafi tsafi. Cikin warin gwiwa shugaban makarantar ya yi mata addu'a ya kuma bata wasu addu'o'in ya ce ta lazumci karanta su ko da yaushe tabbas babu tsafin da zai tasiri kan ta. Safiya tayi tana zaune tana duba sa onnin wayarta ta ci karo da sa on daya sa ta tashi zumbur sai kuma ta fashe da kuka, har su Daddy suka taso kanta domin sun auka ko Mamar ce ma ta mutu, sai dai cikin kukan take cewa, "Alhamdulillah! Allah na gode maka ka ida cika mun burina duka na ha u da Jiddah Daddy." Duk da cewar basu san Jiddah a fili ba amma sun san Jiddah a labarin Alawiyya don haka sai suka samu kansu da jin farin ciki su ma sosai, domin sun san kukan Alawiyya ya are tun da ta ha u da muhimman mutane biyu da take nema ido rufe a duniyar ta. Cikin farin ciki ta fara karanta sa on da Jiddah ta turo mata. "Ban san da wane irin zance zan fara ba, amma ina so ki sani na sha wahala kan nemanki na yi matu ar kewarki na shiga nau'in rayuwa sosai bayan mun rabu. Sai dai na manta komai lokacin dana ganki a duniyar Gizo tabbas Alawiyya nayi farin ciki ganin kin samu cigaba a rayuwarki har kin kai babban matsayi tabbas na ji da i sosai! Sai dai na koka sosai dana ga labarin abin da ya faru ga Mama. Yaushe duniya tai lalacewar da ake ora ma mutum irin wannan azafin Alawiyya? Tabbas na kai arar mai laifin gun mai duka don nasan shi ne kawai zai saka mata ya bi mata ha inta kan abin da akai mata. Daga arshe ina maki albishir da zuwana a Yau in nan domin naga Yau ne za a fara zaman kotu. Sai ince sai mun ha u a can. Zumbur ta mi e "Tabbas Yau ne za a fara zaman kotu sai dai bata da babbar shedar da take bu ata a hannunta, amma ba damuwa kowa ya ci tuwo da ita miya ya sha. Tana hawaye ta maida mata amsar. "A rubutun waya bai isa ki gane yanda nayi matu ar kewarki ba, na neme ki tamkar yarinyar data ace, na sha wahala tamkar ba zan rayu ba, amma daga arshe na ci alwashin cika mana al awarinmu na zama Lauya don kauda arna a doron duniya, don watarwa yara irinmu ha insu, don samawa yara anci a gun iyayensu. Ina nan ina dakon zuwanki ar'uwata." Cikin sauri suka shirya don zuwa kotun. Ba su wani au lokaci ba sai gasu kan titin da zai kai su inda Kotun take. Sai dai harbe tayar motar da suke ciki ne yasa kan motar ta wace daga hannunta kai tsaye motar ta je ta bugi wata bishiya. Cikin zafin nama Alawiyya ta latsa wata ar waya dake hannunta sannan ta samu ta bu e marfin motar ta fice daga cikin ta, a hankali su Daddy suka fito, cikin ikon Allah babu wanda ya samu ko da kujewa. Ganin wata ba ar mota ta nufo su yasa Alawiyya saurin janye su da gudu suka shiga dajin. Ba a jima ba sai ga wasu motoci sun iso gun da gudun tsiya guda biyu suma, sun bu ewa waccan motar dake binsu Alawiyya. Wata motar ce ta iso cikin hanzari Alawiyya ta saka su Daddy tace su isa kotun zata iso ba da jimawa ba ita ma. Haka suka tafi duk sun ru e saboda arar harbin dake ta tashi a gun. Sai da Alawiyya taga motar su Daddy tabar wajen sannan ita ma ta fiddo aramar bindigarta ta fara auki ba da i da mutanen cikin ba ar motar. Motocin da suka zo kuwa yaranta ne ta kira suka zo don haka nan da nan suka ure ba ar motar ga alama harsashin masu motar ya are don haka suka daina harbin. Cikin jarumta Alawiyya ta isa gun motar ta bu e sai dai ashe an harbe mutanen dake motar guda biyu. Waya ce ta fara ringing don haka sai ta auka, muryar Oga Dauda ce ra au cikin wayar yana cewa, "Ina fatan kun kama min ita, kuma baku kashe ta ba? Babanta da mijinta kawai nake son ku harbe ban da ita saboda masoyiyata na gunta da yarana." Cike da acin rai tace, "Ka makara domin sun tafi inda ba a dawowa sai dai ka turo wasu muna inda suka iske mu." Ta kashe wayar ta jef a aljihu ta nufi gun yaranta. Cikin sauri suka tada mota suka nufi gidan data oye yaran Oga Dauda da budurwarsa. Tunda ta kama b durwar Oga Dauda da yaransa, sai ta oye su wani gidanta dake gab da kotun wanda ba kowa zai auka akwai mutane a cikinsa ba, domin ko da yaushe a rufe yake ba wanda zai ce ya ta a ganinsa a bu Babu irin tambayar da batai masu ba amma sun i bata ha in kai, hakan yasa ta fara gana masu azaba ita da amintattun yaranta guda uku wa anda suka iya aiki suka san makamar aiki, ba ta ha a su aiki lokaci guda domin kowane guda daga cikin su gayya ne shi ka ai, ba aramin mamaki su kai ba lokacin da ta kira su kan aiki guda su duka, amma da suka fahimci aikin sai suka gane cewar lamarin babba ne, kuma akwai abin da take nufi da hakan. Lokacin da suka gidanne Oga Dauda ya kira wayar Alawiyya ya ce mata ya amince zai yadda su ha u amma da shara in idan ya kaita gidan matsafan da aka kai yaran zata sakar mai yara da budurwa musamman da ya ji cewar akwai ciki jikin masoyiyar ta shi sai yake jin zai iya komai don tsirar da rayuwar gudan jininsa da masoyiyarsa. Hakan yasa Alawiyya kai tsaye ta nufi inda su kai da Oga Dauda za su ha u tare da yaranta dake bin ta a oye ko da zata neme su cikin gaggawa. Tana isa gun ta hango motar Oga Dauda, don haka ta tsaya nesa da shi ta kira shi a waya, cike da samun nasara ya aga wayar ya kwashe da dariyar da yake ganin ta mugunta ce ko wayau da ya yi mata. Yasan cewa duk karfin da take ta ama da shi bata kai shi ba, domin shi in irin mazan nan ne arfafa kuma ba haka nan yake zaune lokaci zuwa lokaci yana zuwa gun training yana motsa jiki don ara samun lafiya da arfi saboda zuwan irin wannan ranar. Hakan yasa ya ce cike da yarda da kansa, " Ina so mu yi fa a da ke, idan har ki ka ci galaba kaina to nayi maki al awarin kai ki gidan da yaran suke , idan kuwa Ni na ci galaba kanki to tabbas za ki ban masoyiyata ki sakar min yarana kuma ki je ki nemo yaran da kanki." Murmushi tai tamkar yana gabanta tace, "Idan har zaka zama mai cika al awarin nan to na yadda zan fa a da kai idan ka ci galaba ta na janye daga shari'ar ma baki aya wannan al awari ne." Kashe wayar tai tana jin sautin dariyarsa. Tare suka fito daga motocinsu, ba aramin mamaki Oga Dauda ya yi ba, ganin shigar dake jikin Barista Alawiyya ba, ba don yasan tabbas da ita ya yi waya ba, haka yana da tabbacin ita ce tai magana kuma ya ga ita ka ai ce a motar da cewa zai namiji ne ta turo mai, domin baki aya tayi shigar jarumai ta rufe fuskarta. Kallon-kallo aka fara a tsakaninsu kowa na hangen inda zai samu galabar abokin fa an sa. Sai kuma suka fara kaiwa juna farmaki abin da ya ba Oga Dauda mamaki yadda Barista Alawiyya tasan fa a sosai take kare kanta daga dukansa amma shi a mamakinsa ya kasa kare duk dukan da take mai. Cikin lokaci alilan Oga Dauda ya fahimci ruwa ba sa'an kwando
Chapter 65 · 0% Book details