← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 133

Sashe 55

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zata gaida shi wayarta tai ara don haka sai ta aga kiran cikin natsuwa. Daga can angaren aka ce "Kina magana da Abubakar ne wanda kuka shigo mota azun, dama kira nayi in maki ya gajiyar hanya?" Kamar yana gabanta haka tai an jim kana tace, "Ai naga sunanka kuma ban da shi a waya sai na tuna da kai ka kasa da kanka, na iso lafiya kaima fatan ka isa lafiya?" Mustapha ya ji wani ba in takaici ya sauka kan ahon zuciyarsa ji yake tamkar ya tashi ya fice, amma hakan ba zai samu ba, duk wani gefen na zuciyarsa ya yi murna da gane cewa bata da aure tun da har ta iya ba wani wayarta ya saka lamba da sunansa na banza. Jiddah ta gyara ri on wayarta sosai a kunne tace, "A'a na gode ba sai ka zo ba, ai ba damuwa ban fita zance Ni." Hajjo tai tsaki tace, " aryar banza kenan, baki zance to haka za ki zauna ba za ki yi aure ba kike nufi? To tun wuri ma ki bar wannan shirmen ki fitar da miji ki yi aurenki nasan dai yanzu ai kin kusan gama karatunki ai." Daga can Abubakar ya ce, "Haba Hawwy baki ji me ake ce maki ba, kawai ki ban damar gwada sa'ata ba mamaki ni ne mai rabon." Jiddah ta langa ar da kanta gefe kamar zatai kuka tace, "Baka san halin Hajjo bane ba, tsokanata take wane irin aure kuma yanzu?" Abubakar ya ce, "Ni dai don Allah aban damar zuwa na sake tozali da kyakkyawar fuskar nan taki mai saukar da natsuwa ." Kasa magana tai kawai ta bi shi da murmushi. Mustapha dake zaune ya kasa ha uri ya kalli Hajjo ya ce, "Bata da aure ne yanzu Hajjo kike mata fa an aure tana waya da masoyinta?" Hajjo tace, "Kai dai bari kawai Mustapha wallahi tun lokacin rasuwar Salim mijin ya sake ta amma shi ne ta i fitar da miji tai aure har an doshi shekaru biyu ana niyyar shiga ta uku." Wani irin farin ciki ya ziyarci fuskarsa ya ji tamkar albishir da warwarewar matsalarsa Hajjo tai mai ya kalli Hajjo dake ri e da waya ta kasa cewa komai jin maganar Hajjo. Abubakar ya ce, "Na lura yanzu baki da lokaci don haka anjima zan kira ki." Ta aje wayar tana ajiyar zuciya sai kuma ta kalli Mustapha dake kallonta ba yabo ba fallasa ta gaida shi. Ya amsa ba tare da gane abin da amsar ke nufi ba ya mi e yana ma Hajjo bankwana ya fice. Jiddah ta saka hijabinta ta nufi gidan awarta Bilkisu tun daga zaure take sallama dan tasan ta sha a mata haushi yadda take ta kiranta bata amsa kiran ba kuma bata shiga gidan ba. Bilkisu ta kauda kai tana cewa, "Nayi fushi ai dama kin koma." Jiddah tai dariya ta aga yaron Bilkinsun tana mai wasa ta isa akin tana cewa, "Ke fa da ina dake kenan baki ma mutum uzuri sam." Mustapha yana zaune akinsa yana jin tamkar wani albishir akai mai da kujerar Makkah. Jiddah bata da aure tabbas kwanakin nan yana yawan mafarkinta suna cikin soyayya da faranta ran juna, kowa cikin annashuwa da fara'a ashe kenan hakan zai faru? Allah na gode maka da ka nuna min ranar da naji labarin da na jima ina neman ji. Ya juya yana hasko yadda ta zuba mai ido tana gaida shi fararen idanunta suka sauka a cikin idanunsa. Kamar a lokacin ne haka ya ji wani yarrr baki aya jikinsa ya yi. Tabbas yana ji a jikinsa arshen damuwarsa ta zo, domin yana tuna yadda Salim ke yawan yabon yarinyar ko da yaushe bakinsa na kan Jiddah nada ha uri tasan abin da take, tabbas ita ce daidai da shi ba zai sake wani ya yi mai shigar sauri ba kuma wannan karon kamar aurenta na farko da sai dai ya ji labarin tai aure kawai. Yaron shi ya shigo akin da sallama ya ce, "Mama tace zaka ci abinci na kawo maka?" Wani acin rai ya ziyarci fuskarsa wai ace kana da mata amma ba zata iya kawo maka abinci ba da kanta ta zauna gabanka ko bata cin abincin da kai ai ta zauna ta kula da kai idan kana ci, amma shi duk wannan bai samun shi ga duk matan uku daya ajiye. Cikin za uwa yaron ya sake cewa, "Baba a kawo maka abinci?" Cikin acin rai ya ce, "Ka ce ban ci." Yaron ya juya ya fice ya koma ya gayama Mamarsa abin da Babansa ya ce, bata damu ba sai ta sake gyara zamanta kawai tace a ranta ("Kai ka sani wallahi ya ara yawa ma) ta cigaba da harkar gabanta hankalinta kwance domin ba Yau bane karon farko da maigidan ya i cin abincinsa ba, ita ba zata iya ma shegen iyayinsa ba, mutum kamar wata mace sai shegen son tarairayata ga son girma kamar wani gyambo, ta sake ta e bakinta ta ja tsaki tace a fili wannan karon, "Bar shi ya je ya ci na titi ai ya ware daman shi ya sani dai." Yaron ya ce, "Mama mu ki ara mana daman ban oshi ba Ni azun." Ta dubi yaron tace, "Kambu! Duk abincin da ku ka ci zaka ce baka oshi ba? To ai saika auko na zuba ma, kana gamawa ka zo kai wanka na gayama tun jiya nake fama da kai kan wankan nan sai na gayama Babanku Yau idan bakai wankan nan ba." Ya ruga ya auko abincin ya kawo mata ta zuba mai, suma sauran yaran suka taso sai an ara masu, ta juye masu sauran abincin duka tana cewa "Ai sai ku cinye ku fini iba ku da baku da taus ayina." Karaf kishiyarta ta fito tana huci ta warce kular abincin tace, "Ai ba yaranki bane kawai yara a gidan akwai sauran masu ha i a cikin abincin a gidan don haka sai a basu ha insu ai abincin ubansu ne ba daga wani gida aka kawo shi ba ehe." Maryam ta zaburo ita ma cike da masifa tace, "Dakata Malama! Ina ruwanki da abincin ranar girkina? Ko kinga ina kula ki ranar girkinki ne? Ai ba don ban san bai cin abincin ba sai don a zauna lafiya kawai, don haka tun wuri ki aje abincin nan kafin a ji kanmu yanzu." Hafsat ta zaburo ita ma cike da masifa tace, "Ai ba hanaki zuwa nayi ki iba ba, don haka ruwanki ne kuma wannan abincin ko dawa kike yawo ba zan barma yaranki shi ba, shegun yara masu shegen cin tsiya kawai." Maryam ta finciko kular abincin tana cewa, "Ban haifi shegu ba sai dai ke kika haifi shegu abinci kuma sai dai ya zube ayi asarar shi da matsiyatan yaran can naki su ci shi, ko da yake ai ba su ka ai kike ci dawa da abincin gidan nan ba ina da labarin wanda kike sata kina kaiwa gida tsoffi na zubawa a tukunya ai... Bata kai arshen maganar ba, Hafsat ta kai mata duka suka watsar da abincin suka kama dambe yara na kallonsu sun yi tsuru-tsuru da su, ganin da gaske suke an babban ya ruga akin Mustapha ya gaya mai su Mama na fa a saboda abincin shi. Wani takaici ne ya sake ziyarar zuciyarsa don haka yai banza da yaron ya cigaba da jin acin da ransa ke ma shi, bai ankara ba hawaye suka zuba mai, ya dinga jin karayar zuciyarsa na ara hauhawa tabbas bai dacen mata ba sam, ya zai yi haka tashi addarar take dole ya jure ko da kuwa hakan zai sa hawan jini kama shi ko ciwon zuciya. Haka ya dinga kuka kamar aramin yaro yana jiyo tashin muryar matan nashi da kowacce ke zagin ar'uwarta suna aibata juna gaban yaransu abin takaici da ban haushi. Kamar ya yale su sai kuma ya mi e jikinsa sanyi alau ya nufi sashen matan nashi yana jin kamar zuciyarsa zata fice don acin rai. Ko kunya basu ji sun dage sai dambe su ke ga abincin nan a watse asa yaran kuma suna zaune suna kallonsu. Daka masu tsawa ya yi amma sun yi nisa ba mai jin shi don haka ya sake aga murya sosai ya ce, "Wai wane irin jahilci ne wannan kuke da girmanku a gaban yaranku? Kuna abu sam babu mutunci babu tunani a gaban yaranku kuke zubar ma juna ku da daraja." Sai a lokacin suka san da zaman maigidan a gun, amma ba su jin za su saurara ma fa an don yanzu ma abin yake a kai, domin kowace ta tona asirin abin ayar ke yi na cikin gidan. Yaran ya daka ma tsawa, kowane ya nufi akin uwarsa yana waigen Uban. Matan ya sake daka ma tsawar da tafi ta farko dole kowacce ta nufi akinta tana zagin ar'uwarta. A nan ya samu waje ya zauna yana kallon abincin da suka watsar asa. Wayarsa ce tai ara yana dubawa gabansa ya fa i, ita kuma bai san me zata ce ba, amma sai ya aga kawai yana sauraren da wadda ta kira shi yanzu kuma. "Nasan dai kana jina amma saboda ba in hali da girman kan tsiya kai banza ka yale Ni, to hakan bai dame ni ba dama kiranka nayi na gayama ban da lafiya kuma naje asibiti na ci ku i masu dama dan haka ka aiko min da ku ina ba sai ka zo ba domin ba bu atar ganinka nake ba ku in kawai nake bu ata." Kasa cewa komai ya yi sai gya a kanshi da ya yi kawai don abin ya fi arfinsa. "Yawwa na manta na gayama ina da ciki amma kar kai murna don ba lallai bane ya zo duniyar ba, kasan dai ina neman saki ba zan bari ciki ya gitta min ba a lamarina ba." Kit ta kashe wayar ba tare da ya ce ko da ala ba. "Sallamu alaikum." Sallamar data maido ma shi da tunaninsa kenan ya zuba mata ido yana kallonta nan take ya ji tamkar an watsa mai ruwan sanyi a zuciyarsa. Jiddah ce ta shigo cikin gidan, yana kallon yadda take are ma abincin
Chapter 55 · 0% Book details