← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 133

Sashe 129

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

da aka kai Jiddah gidansa ba, "Mustapha ina son na tayaka murna sannan na gayama wasu abubuwan da baka sani ba ko kuma baka fahimta ba. Ni da Jiddah tamkar Hassana da Hussaina muke don haka ba wadda zata lamunci a takura ko cutar wata daga cikinmu ba. Mustapha ga Jiddah nan a gunka matsayin matarka nasan matanka sarai nayi bincike kan matanka kaima na yi bincike sosai kan halinka don haka ka sani ba zan bari ko da wasa ba kai ko su wata ta sake tada ma Jiddah hawan jini ba ko a saka ta a cikin damuwa ba. Mustapha kar ka sake na ji ko na gani a zaman Jiddah a gidanka, domin cikin maza dubu Jiddah ta za e ka ta kauda kai daga manyan masu ku i da manyan an siyasa da manyan Malamai tace sai kai, to kar kai kuka da kowa kai kuka da kanka a duk lokacin da wani abu ya samu Jiddah na rantse da Allah sai na yamutsa maka rayuwar iyali ba ruwana... arar wayar ce ta sa ya dawo hayyacinsa dole don haka ya tsira ma wayar ido kamar mai karanta wani abu jikinta ya kasa agawa. Ko ya kenan idan Alawiyya tasan me ke faruwa? Wane irin mataki ne Jiddah ta auka? Ya ya Hafsat za tai kenan ga alama ta sha Ku yi ha uri dai insha Allah zan gama maku labarin nan cikin lokaci . Taku Haupha IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 129 · 0% Book details