← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 133

Sashe 23

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sallah na kwanta barci mai nauyi ya auke Ni. Da rana ina zaune ina tunanin me zan dafa mana ban da komai ga Haidar sai kuka yake, na bu e gidan na fita naje gidan Binta ta ara min ku i ko fura na sai ma Haidar nasan kukan yunwa yake . Ta kuwa ban aron Naira ari, bayan na dawo ta zubo abinci mai yawan gaske ta bada aka kawo min lokacin ina dama furar da na siyo. Gama cin abincin ke da wuya Haidar nata wasansa Safiya tai sallama gidan. Na amsa mata ina daga inda nake zaune... Ko shigowa bata ida yi ba ta fara maganar "Yanzu ke Jiddah kin kyauta wa rayuwarki dukan miji? Tun da nake ban ta a jin labari ko ganin wadda ta bugi miji har ta tsugunnar da shi ba sai ke." Na dube ta nace, "Zagina ya yi fa, kuma don na rama ya mare ni." Ta dube ni cike da haushi tace, "To dama duk mace ai bata wuce duka da zagi gun mijinta ba, ko sai ke shafaffa da mai? Jiddah ban san ki da wannan mugun halin ba sam, kuma nasan dai ba kishin Deeni kike ba balle ki ce kishi ne yasa ki kai mai haka ba. Nafi kowa sanin cewa baki son Deeni domin ba shi ne burin ki ba, kawai kin auri Deeni ne don za in iyayenki ba wai za in zuciyarki ba. Don haka yasa ban damu da ala ar dake tsakanina da shi ba Jiddah... Kawai kaina naji na juyawa ban san ya akai ba sai bu e idona nayi naga mutane kewaye da Ni, sun yi tsuru-tsuru ga wani uban auri daya turnuke akin baki aya. "Yawwa ta dawo hayyacinta, ita ce yanzu." Abin da naji ana cewa kenan, kaina ke ciwo sosai don haka na rufe idona ina jin kukan Haidar na tashi amma ban iya bu e idona don azabar ciwon da yake min. Sannu kawai ake jera min. Ina jinsu amma bakina ya datse ban iya amsawa sai dai a cikin zuciyata nake amsawa. Mutane sun jima zaune suna ta min sannu amma abin mamakin bakina sam bai bu ewa, dole na ha ura kawai nayi lamo har barci yak kwashe ni. Ban farka ba sai can na tashi naga ba kowa sai wata Maman Khairat zaune tana cin abinci Haidar na zaune shima yana cin abincin. "Kin tashi? Sannu tashi ki kuskure bakinki ki ci abinci. Maman Kahairat can asan layinmu take saboda ansar aron littafin Hausa na santa ta sanni. Na mi e jikina sanyi alau kamar an mun duka na tashi ina cije baki na kuskure bakina ta mi o min shinkafa da miya har da nama, na amsa na ci iyakar ci na ta ban ruwa na sha, sai naji na dawo daidai kamar ba Ni ba, sai ciwon kan ka an -ka an shima. Ta dube ni tace, "Me ya ha a ki da awar taki har rai ya aci ki ka fita hayyacinki ki kai mata wannan uban duka Jiddah? Kin ga yadda kika sauya mata kamanni kuwa? Ba yadda ba ai ba a kama ki amma da kin fasa ara sai ki zubar da mutanen da suka ri e ki, tana can sai dai aka auke ta a mota aka nufi gidansu da ita, don nasan duk kwanakin nan ba zata iya hassala ma kanta komai ba, idan ma Allah Ya taimaka baki ji mata ciwon cikin jiki ba, a na wajen kawai ya tsaya." Nace ina dubanta, "Ni dai ban da ta cewa domin dai nasan na ji tana ta min magana kan na yi fa a da Deeni kaina ya fara sarawa na dinga jin amon muryarta na amsa amo a cikin kaina kamar zata fasamin kunne,daga nan ban san abin da ya sake faruwa ba, sai ganin mutane nayi kewaye da Ni... Sallamar Binta tasa nayi shiru domin daman na kai arshen maganata Ni. "Sannu Jiddah, Yau dai wallahi na ji da i, ke ana zagin aljanu amma Ni Yau na shiwa naki albarka. Na rantse da Allah tun ranar da kika iske ta naso ki ha a su duka ki maganinsu amma sai kika tsaya kukan zuci, wanda hakan yasa ta samu damar dawowa har tana maki magana don bata da kunya, ai yanzu sai ta yi hankali idan zata yi idan baya yi kuma ta sake dawowa na rantse da Allah babu mai cetonta duk nan unguwar." Mamarsu Khairat ta dubi Binta, "To wai me ya ha a su ne?" Kamar daman jira take, ta kwashe komai ta gaya mata. Ta kwashe da dariya tace, "Amma fa ba arya ta jibgu,mu fa ihu muka dinga ji muka rasa daga ina ne, saboda ba wanda ya kawo gidan Jiddah ne, to ita da miji ma yana can yana girbar abin da ya shuka wa zai tsammanin faruwar wani abu a gidanta? Sai da mu ka ji abin ya yi yawa sannan fa muka nufo nan gidan, Safiya ta yi laushi har ta kasa ihun sai numfashi take idanunta sun firfito tul kamar an jefa fulawa a man zafi (fanke) wallahi da yar muka samu aka wace ta, daga hannun Jiddah. Ashe Jiddah nada aljanu? Wallahi bamu ta a sani ba, ko da naji ashe shi yasa tai ma Deeni munafikin duka har ya tsage ashi?" Ni dai sai kuka ya wace min wane irin aljanu kuma gare Ni? Yaushe na same su? Ina na ha u da su? Me yasa jarabtar rayuwata ara yawa take madadin raguwa? To mu bi Haupha don jin dalilin hakan. Shin yaushe Deeni zai dawo gidansa? Wane mataki zai auka idan ya ji an gabji Safiya? Taku a kullum Haupha [8/3, 10:43 AM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 23 · 0% Book details