Sashe 50
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
shaida cewar da gaske kun yi mana komai yadda mu ke bu ata." aya daga cikinsu ya ce, "Kin gane ko Hajiya wannan duk ba wani abin ji bane ba, kawai ku fara bamu kaso biyar cikin goma da za ku bamu don komai ya tsaya mana." Hajiya Tani ta gyara zama tace, "Kai Dauda kar da ka kawo mana rainin hankali man, ko ka manta miliyan biyar muka baku ranar da kuka auki yaran? To bari ka ji na gayama mun fi ku son ku i domin akan ku i muka shiga ungiyar asiri har muka bada iyayenmu da wayayenmu kyauta ga dodon tsafi muka za i mu rayu ba 'ya'ya mu tara dukiya shi ne za ka zo kana maganar ku i kamar ku ne kuka bamu su ?" Hajiya Turai ta amshe tace, "Gaya masu dai, tsabar son ku i yasa muka ha ura da ganin anmu na yawo a doron duniya don haka kuwa babu sakarkarun da zamu kwashe dukiya mu ba." Cikin alamar rashin gaskiya attin suka mi e tsaye suna tafiyar mashaya suna cewa, "No wahala Hajiyoyi sai mun ha e a ganin gaba mun barku lafiya." Suka fice daga falon. Kuka ya wace mai ya fito ba kowa falon ya shigo akina ya kama hannuna muka koma akinsa ya ce, "Fatima duk da baki gani amma nasan kina ji don haka saurara ki ji abin da su Turai suka aikata min,duk abin da nake masu bai sa sun tausaya min ba sun bar min yarana biyu da Allah Ya azurta Ni da su ba, so suke su kashe min su kamar yadda suke kashe nasu kamar yadda suka kashe maki idanuwa tabbas sai nayi Shari'a mai girman gaske tsakanina da su Fatima." Ni da shi baki aya kuka muke ba mai iya lallashin kowa. A haka su Hajiya Turai suka iske mu akin, suka kwashe da dariya suka tafa suka ce, FATIMA ki gode wa Allah da Yasa ba kowane asiri ke tasiri kan ki ba, ki sani duk cikinki da ya zube a gidan nan mu ne nan ke zubar da shi ta hanya ba Dr. ma udan ku e tunda ke tsafi bai kama cikinki yasa muka ha a baki da shi duk lokacin da kike awon ciki yake zubar da shi kafin ya yi wari. Shima wannan cikin na yaran nan tsautsai ne yasa muka yanke shawarar mu yi maki sharri ga maigidan kan cewa ke ce ke zubar da duk wani cikin da yake zubewa saboda baki son shi. Cikin nasara kuwa ya yadda da sharrin mu ya juya maki baya har kika samu cikin yaran nan bamu farga ba, lokacin da muka farga kuma ba yadda ba mu yi ba amma cikin ya i zubewa dole muka yanke shawarar idan an kai ki asibiti gun haihuwa Dr ya kashe ko miye ya ce ma Alh kin kashe abin ki gun haihuwa. Da yake munafukan yaran sai sun zo duniya sai ranar haihuwar ta zo mana a bazata kuma sai ba can asibitin ba aka kai ki shi ne yasa har ku ka dawo da yaran a raye. Amma a Yau za a yita ta are a tsakaninmu da ku, za mu kashe yaran mu kashe uban yaran ke kuma mu ora alhakin a kanki , yadda duniya zata shekara tana tsine maki albarka mutanen cikinta na Allah wadai da halinki, mu kuma mu cigaba da cin dukiyar Alh da tsinke hankali kwance... Shigowar attin nan tasa Alh saurin rarumo inda yake ajiyar bindigarsa amma bata gun. Ban san ya akai ba na dai ji lokacin da suke ta kokowa har naji kakarin Alh sai kuma naji an kama hannuna an saka min wu a a ciki an tura Ni kan jikin mutum. Ina ta lalube na gane Alh ne kwance kuma jini na zuba daga cikinsa, ina a haka na ji ihun su Hajiya Turai suna cewa na kashe Alhaji a taimaka masu. Sai ji nayi an kama Ni an amshe wu ar an tasani gaba wanda na fahimci an sanda ne. Sai jiya bayan fitarku an zo har nan an ja min kunne kan idan ban hana iyata Alawiyya kare Ni a kotu ba za a kashe ta kuma su ma yaran nawa za su kashe su domin har yanzu wai yaran na raye ba abin da ya same su domin jikinsu wu a da bindiga duk basu kama su. Wannan shi ne asalin abin da ya faru bayan rabuwarmu da ku Alawiyya." Cewar Fatima cikin goge hawayen idonta. Gandurobar data kawo Fatima ce ta dawo tace, "Ranku ya da e lokaci ya yi na komawarta ciki." Ba tare da Barista Alawiyya ta dube ta ba ta kama hannun Fatima ta mi ar da ita tsaye tace, "Mama ku je ki kwanta Yau ki yi barci ki huta indai da gaske Ni in ke kika haifeni kuma ta hanya mai inganci to ko sama da asa za su ha e sai na watar maki ancinki haka sai na nemo annena duk duniyar da suke. Tabbas wu a da bindiga basu tasiri a jikin zuri'arki domin ko Ni nan basu kama Ni ba arya su kai ba." Ta fice ba tare da ta sake waigen kowa ba a gun. Fitar su ke da wuya sai maigadin gidan ya fito da waya ya kira wata lamba ya yi magana ya kashe ya koma ya zauna yana tsira ma motocindu ido kamar mai yin nazari. To fa ya kenan jama'a? Ana wata ga wata fa! Taku a kullum Haupha [8/17, 4:38 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa