Sashe 61
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Page 32 Ta jima ba numfashi har Allah Ya kawo awarta ta iske ta a halin, da farko ta auka aljanunta ne suka tashi sai kuma ta fahimci suma tai, cikin sauri ta yayyafa mata ruwa sai ga shi kuwa ta farfa o tana ajiyar zuciya, sai kuma ta fashe da kuka mai ciwon gaske. A'isha Yusuf ta ru e ta dinga tambayarta abin da akai mata take kuka amma ba amsa kukanta kawai take don haka A'isha ta auki wayar Jiddah da zummar kiran Abubakar tasan shi ne kawai zai iya jin damuwar Jiddah ya bata ha uri ko shawarar da zata natsu. Sai dai me? A'isha na aukar wayar ta fasa ara tace, "Na shiga uku na lalace Ni A'isha me zan gani haka? E gaskiya ne kuka ya ganki Jiddah bu e bakinki ki yi kuka kar da ki bar komai a ranki maida kuka ya zama hanyar wanke takaicinki tabbas ba zan hanaki yin wannan kukan ba... Ita ma kuma ya ci arfinta ta rungume Jiddah su kai ta kuka, har gwara Jiddah bata iya ko furta kalma guda amma ita A'isha kukan take tana tsinewa Abubakar har da iyayensa. A haka sauran awayenta suka zo kowacce taga hotunan sai ta dafe irji ta ambaci ta shiga uku me zata gani haka? Cikin lokaci ka an wajen ya kacame da koke-koke tamkar gidan mutuwa, baki aya sun tausayawa Jiddah yadda ta auki so da auna ta dam a ma Abubakar amma shi ne ya saka mata da wannan muguwar sakayyar, tabbas ba arya ake ba da akace wasu mazan babu tsoron Allah a tare da su kuma sun cika munafukai na gaske a shafin soyayya. Har suka taso daga makarantar Jiddah bata furta ko da kalma guda ba, sai dai kukan da take rerawa kawai kamar wadda akai ma mutuwa. Ko da ta isa gida kasa biyawa tai ta auki yaranta kawai wuce wa tai ta shige akinta ta dasa wani kukan, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama akan Abubakar, shin me yasa yai mata haka? Dama akwai yaudara a tsakaninsu? Me tai mai wanda zai sa ya yi mata wannan hukuncin? Ashe dama ba zata daina ganin ba in cikin a namiji ba? Me yasa maza su ke mata haka ne? Akan me take wahala a rayuwarta da maza? A fili tace, "Ya Allah kaga halin da nake ciki ka bi min ha ina ka saka mun Ni da Abubakar duk wanda ya cuci wani Allah ka sakama wanda aka cuta. Tabbas ban yafe maka ba Abubakar! Haka ta kwana bata aikin komai sai kuka da tunanin abin da yasa Abubakar ya yaudareta. Wasa-wasa ta shafe sati bata je makaranta ba, domin ciwon hawan jininta ya tashi sosa i, kamar zata mutu, har sai da aka kwantar da ita asibiti tai kwana biyar jininta ya i sauka. Babu yadda Yayar Mamanta dake jinyar ta ba tai da ita ba, kan ta gaya mata damuwarta ba amma bata magana sai hawaye kawai lokaci zuwa lokaci da take zubarwa. Ga shi duk lokacin da aka aunata jinin bai sauka sai ara sama yake, abin da ya ba likitocin mamaki kenan suka dinga mata fa a kan ta cire damuwar dake ranta idan ba haka ba tabbas hawan jini zai mata muguwar illa. Kaf awayenta na makaranta sai da suka zo dubata, tabbas ta basu mamaki sun ci alwashin duk ranar da Abubakar ya dawo makarantar sai sun yi ma shi mafiyin abin da ya yi ma Jiddah. Sai da shafe kwanaki goma cur a asibitin sannan jininta ya daidaita aka sallameta, ta koma gida tai wata irin rama tai fayau duk wanda ya ganta yasan ta sha jinyar ciwo mai zafin gaske. Tun daga lokacin sai Jiddah ta koma shiru-shiru bata magana haka bata tankawa duk wani namiji balle a samu wanda zai ce yana sonta. Ta saka a ranta cewar babu ita ba sauran soyayya ta gama ta, domin ta amince da cewar duk maza halinsu guda basu da amana haka sun ware da cutar da zuciyar mace. Abubakar kuwa, ya kira tura mata message ya ce, "Sweetheart don Allah ki yi ha uri za ki ji Ni kwana biyu shiru, kin san ban da waya kuma ga tafiya bikin anwata da aka ri e Niger ya zo don haka za mu tafi can sai na dawo zan yi matu ar kewarki koma ince ina cikin kewarki sosai abar aunata." Kuka ya wace mata sosai, tabbas akwai abin da Abubakar ya auke ta da yake wasa da hankalinta yake mata yawo da zuciya, shin wane fage ko fanni take a zuciyarsa? Tabbas ta jima tana jin labarin mayaudara amma bata ta a ha uwa da mayaudari irin Abubakar ba, tsabar yaudara ka yi auren ma sai ka ci-gaba da yaudara? Sai da tai da gaske ta tura mai reply da "Na gode Allah Ya tsare hanya." Tun daga lokacin bai sake kiranta ba, haka bai sake yi mata message ba, sai da aka fi sati biyu sannan ya turo mata message in ya dawo Nigeria. Zuwa yanzu ta dake ma zuciyarta so take taga iyakar gudun ruwansa don haka duk lokacin daya turo mata sa on soyayya tana danne zuciyarta ta maida mai ko ba yawa. So take su ha u ido da ido ta nuna mai hotunan aurensa don taga me zai yi kuma me zai ce mata, don haka take biye mai duk da akwai sauyi sosai a tsakaninsu yanzu waya ba sosai ba text ma ba sosai ba, amma duk ta share shi hatta orafin ya daina kulawa da ita ta daina mai. A da kuwa komin dare idan aya daga cikinsu ya farka daga barci sai ya tada ayan haka wayarsu ce arshen barcin kowane haka suna tashi asuba kafin su yi alwala sai sun waya haka idan suka gama sai sun waya, amma ban da yanzu waya zuwa karfe takwas sun gama na dare bai kiranta da asuba ko da sassafe duk wayarsa a rufe take ma. Ranar Litinin ya ce mata zai dawo makaranta don haka ta gayama awarta A'isha Yusuf cikin ba in ciki A'ishar tace, "To ina ruwana da zuwan shi? Matsiyaci wallahi ya yi asarar da ba zai ta a maida irinta ba." Bayan sun fito class sai ga kiran Abubakar suna zaune bayan class suna hutawa , ta gaya mai inda take sai ga shi kuwa ya sha sabuwar shadda sai washe baki yake ya yi gwanin kyau abin sa alamar angonci na kai mai karo yadda ya kamata. A'isha kamar ta tashi sai kuma taga rashin dacewar tashinta don haka ta gyara zamanta sosai ta tsira mai ido yana nufo su ji take tamkar ta rufe shi da duka yana kawowa inda suke. Da sallamarsa ya iso gun ya le a fuskar Jiddah ya ce, "Wow ! Na ji da in ganinki wallahi na shiga tashin hankali da muguwar kewarki sosai Jiddata." Jiddah dai ta sadda kanta asa kawai tana murmushi mai cike da takaici bata ce mai komai ba. Ya amshi wayarta dake hannunta yana dubawa ya ce, "Mu ga sabbin hotunan da akai min da ban nan naga kin ara haske da kyau kamar ba ki yi kewa ta ba." Karaf A'isha Yusuf tace, "Ciki gare ai kaga dole tai haske da kyau ai." Cikin murmushin wasa ya ce, "Haba Aisha kar da ki shiga tsakanina da matata man daga zuwa na ki bari na bata ha urin rashin gani na da bata yi na barkatai man." A'isha tai dariya tace, "Daman ina fa zata ganka tunda ka yi naka wajen?" Yana bu e wajen hotuna ya ci karo da hotunan bikinsa kawai gani mu kai ya yi tsuru-tsuru ya kasa ha a ido da Aisha ma balle Jiddah. Amma da yake an duniya ne sai ya wayance ya ce, "Jiddah naga sai wani ha e rai kike yi kamar baki amshi tuban da nayi maki ba? Kin san dai ina sonki ba zan iya barinki ba duk rintsi... "Kai dakata Malam! Kada ka rainawa mutane hankali a karo na barkatai mana, kana nufin yanzu ma duk da kaga hotunan aurenka a wayarta ba zaka sararama yaudararta ba? Tabbas ka ci uwar rainin wayau rai Ni kai kam." Tsugunnawa ya yi asa ya ce, "Don Allah ku fahimce ni wallahi ina son Jiddah amma lokacin dana ha u da ita akwai maganar wata a kaina sai dai sonta ya rufe min ido na kasa gaya mata gaskiya kawai nasa a raina idan nayi aurena zan dawo na aure ta ita ma a ta biyu." "To ai hakan ba zai yiyu ba Abubakar Yau ta zama ranar arshe a tsakanina da kai ka manta da Ni kamar yadda na manta da kai." Cewar Jiddah kenan ta bar gun bayan ta fisge wayarta a gun shi. Ya dinga kwa a mata kira amma ko waigen inda yake ba tai ba tai tafiyarsa. A'isha ta dube shi tace, "Ka dai ji kunya wallahi kuma ka aje a ranka sai ka yi nadamar abin da kai ma Jiddah insha Allah ba zaka ta a jin da in rayuwar aurenka ba tunda ka yaudari awata." Ita ma ta wuce ta bar shi gun a tsugunne. Tun daga lokacin ko da yaushe sai Abubakar ya kira wayar Jiddah amma bata agawa haka idan ya turo mata sa o bata maida mai reply. Ya takura mata a makaranta duk inda tai yana biye da ita yana bata ha uri amma ita bata yi mai magana, takan kalle shi sau guda ta kauda kanta. Hakan yasa ya tsare ta yana kuka ya ce idan ta amince zai saki matarsa ya aureta indai zata yafe mai ta amince da shi da soyayyarsa. Ita kuma sai ta ji ya ara bata haushi domin duk namijin da zai iya sakin matarsa ta gida don ta waje tabbas ita ma wata rana haka zai sake ta don ya auro wata. Sai kawai tai blocking na number shi da duk wani account na chat inta da shi. Ta dinga saka li ab a makarantar don haka sai ta samu sau in shi sosai. Wata rana da ya gane ita ce ke saka nikab ya tare ta zai fara magiyar da ya saba yi mata ta