Sashe 128
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wa Deeni sosai ya daina kula ni ya daina saurarata ya dinga gani na marar amfani a gare shi ya auka da ni da babu ni duk aya ne arshe don ki nuna min matsayinki da iyakar ki ke ce kika za i sunayen yaran dana haifa saboda ban da gata gun Deeni kece mai gatan kin kasa tunawa da cewa ke matar wani ce kuma duk daren da ewa sai anyi maki abin da ki kai min. Safiya ki fice min daga gida ki barni na ji da abin da ke damuna ba take nake ba na barki da Allah shi ne zai saka min duk wata cuta da shiga ha ina da ku kai ke da sauran mutane duk na barku ga Allah." Ta koma ta kwanta tana dafe da kanta hawaye na zubowa daga idonta, ga gani tana cikin tsananin azabar ciwo ko damuwa. Safiya ta sake rushewa da kuka tace, "Tabbas Jiddah na cancanci duk wani hukunci daga gareki amma don Allah ki yi min koma miye amma kar da ki barni da Allah ko yanzu na gane Allah aya ne ai duba ga yadda na koma kamar ba Ni ba, ban da lafiya ga tarin damuwa ga yarana duk shegu ne gasu su ma duk ba na kirki komai ya are min har ta kaiga na rasa idona guda da hannu guda da bara nake samun abinci saboda yaran sun daina kulawa da Ni sam, duk nasan alhakinki ne ke bibiyata Jiddah don Allah ki yafe min don Allah." Jiddah ta bu e idonta da yar tace, "Safiya ki je na yafe maki, amma don Allah kada ki sake zuwa min gida ki manta da Ni ki saka a ranki baki ta a rayuwa da Ni ba." Sosai Safiya ke kuka tana gode mata sosai ta tashi jikinta sanyi alau ya nufi ofar fita, sai kuma Jiddah ta kwa a mata kira ta tsaya cak. Jiddah ta fashe da kuka ta sauko daga kan kujerar ta rarrafa ta isa gun Safiya ta dafa ta tace, "Ba zan iya manta ki ba haka ba zan iya barin ki a damuwa ba safiya aunar gaskiya da gaskiya nake duk lokacin da na za i mutum to na za e shi ne da zuciya aya don haka kema na yafe maki da zuciya aya Safiya ki manta komai ki cigaba da addu'a da neman yafiyar Allah kan abin da ki kai don shi mai yafiya ne yana yafe mana duk wasu laifuka namu." Safiya ta rungume Jiddah sai kuma tai saurin sakinta ta zaro ido waje da arfi tace, "Me ke damunki Jiddah wane irin zafi ne jikinki ya yi haka?" Jiddah tai murmushi da yar tace, "Ba komai ban lafiya ne, amma da sau i bari na baki sa o sai ki tafi asibiti zan je daman." "Jiddah na sanki sani na gaske na sanki idan kina cikin damuwa nakan fahimci ba in cikinki da farin cikinki shin me yasa ke kika kasa fahimtar rayuwar nan ne? Me yasa kika cika sanyi ne bayan addini ya amince da mai da raddi ga duk wanda ya yi maka abu, har ma idan baka iya maida wa ka kai ara don a fitar maka da ha inka? Gaskiyar magana Jiddah ha urin ki na ban haushi yana sawa kina rasa abubuwa da dama, shin ba ji nayi ance amarci kike ci ba ne ? Jiddah baki yi kama da amarya mai farin ciki ba sam, kada ki ce min wannan karon ma irin Deeni kika aura wanda bai san daraja da kimarki ba balle ya saka ki farin ciki ya mantar dake tarin takaicin da muka taru muka saka ki a baya ba? Jiddah yadda naji ana yabonki a wajen aikinku bai kamata ba ace kin kasa daidaita rayuwarki ba ta aure kin bari ana ta gara ki ba kamar wata jahila ba wadda bata san kanta ba balle tasan na wani ba. Jiddah ki tashi tsaye ki aje wani kawaici da nauyi ko kunya ki nemarwa kanki anci a duk inda kike ba ancin mutane kawai za ki dinga nemar masu ba ke naki ancin na cikin keji a kulle ba. Zan tafi dama na zo ne don na nemi yafiyarki ko na samu sau in ganin bala'i a rayuwata amma don Allah ki duba maganata ya kamata yanzu ace maza sun daina baki tsoro ko razana ki Jiddah, wane irin ba in hali ne baki gani ba daga gun Deeni ba? Ya kamata ki aje babin maza a rayuwarki ki rayu ke ka ai cikin farin ciki Jiddah ba sai kin kashe aurenki ba amma dai ina so ki natsu kisan me kike yi su maza basu da tabbas ko'ina haka suke sunansu aya ne don haka ki daina wahal da kanki a kan rashin dalcinsu ke dai watarwa kanki anci kawai sai ki zauna lafiya." Ta share hawayenta ta fice tana ji a ranta wannan karon ba don duniyar ta juya mata baya da da kanta zata watarwa Jiddah anci gun koma waye mijin nata amma dai zata taya ta da addu'a Allah Ya bata mafita. Mustapha ya koma akinsa a hankali domin wayarsa na haske alamar kira ne ya shigo, yana dubawa ya ga Hafsat ce kamar kar da ya auka sai kuma ya auka don jin ko ta shirya komawa gidan na shi ya je ya maida ta. Sai dai ba wata maganar komawa sai jan shi da labari take wanda duk tsogumi ne da gulma a cikin labarin, hakan yasa ya ji haushin ta sosai a ransa amma bai isa ya nuna mata ba. amshi ya dinga ji na dukan hancinsa ko bai tambaya ba yasan girkin da Princess ke yi ne, sai dai a yanzu haka wata irin kunya yake ji ta ta, da wane ido zai kalle ta bayan ya gama saka ta cikin matsala da ba ar damuwa me kuma zai mata? Kan shi ya ji yana juyawa, tabbas yasan yana da aramar zuciya wadda take saurin karewa kuma bai iya auke tashin hankali, babban abin da yasa yake biye ma, Hafsat kada ace daga aurenshi ya juya wa matarshi baya don haka yake jin bai samun natsuwa ko kwanciyar hankali sai Hafsat in ta koma gidansa. Yasan Princess bata da taurin kai kuma tana da saurin fahimta ba zai sha wahala ba gun shawo kanta ba ta yafe mai abin da ya yi mata ba a cikin amarcinta ba, ya kasa samun lokacinta ya kasa bata kulawa ya kasa ko cin abincin da take girka mai. Sai da ya tabbatar da bata ganshi ba ya fice da sauri don kunyarta yake ji da gaske. Ita kuma tana kallonsa fahimtar bai san ta ganshi yasa tai kamar bata ganshi ba. Zuwa yanzu ta daina kuka ta dake ta cire komai a ranta, hakan yasa ta sha maganinta tai wanka ta fito ta zauna ta ci abincinta ta oshi ta dinga tunano asalin rayuwarta har zuwa yanzu. Ta gode wa Allah sosai da ta dinga hasko yadda ta ga Safiyya sai ta samu kanta da ara yi ma kanta fa a kan yadda shai an ya so ya kai ta ya baro. Tabbas zata tashi tsaye ta waci kanta gun mijinta sai yanzu ta fahimci ma ba laifinsa ba ne, laifinta ne me yasa bata narke mai ba da ya dawo ta yi amfani da ta ta kissar ita ma ta janye ra'ayinsa kamar yadda matar tashi ke yi ? Ai daman ya kamata ace tasan da cewa zata ga abubuwa iri-iri a gidan Prince inta wanda ita ce zata saita su ta gyara komai yadda yai mata. Tsam ta tashi ta koma akinta ta kwanta bisa gado ta jawo wayarta cike da addu'ar ya auka ta kira shi. A lokacin Mustapha na zaune gaban Hafsat tana mai lissafin ku en kayan da ta sai ma yara na fitar biki bai biya ba, bayan yasan da kan shi ya sai ma yaran komai amma don a zauna lafiya ya amsa zai bata. Wayarshi tai ara kuma yasan Princess ce sai ya samu kanshi da amsa wayar amma ya kasa cewa komai. Hafsat ta fusata don ta hango hotonsu a jikin wayar ta kuwa buga tsaki tace, "Wai wane irin iskanci ne wannan sai ta rasa lokacin kira sai kana tare da iyalinsa?" Karaf sai a kunnen Jiddah don haka ta fashe da kukan kissa tace, "Prince ka taimaka min zan mutu ban lafiya! Prince zan mutu! Sai dai kawai Hafsat ta ga Mustapha ya mi e tsaye yana cewa, "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Princess ga Ni nan zuwa yanzu don Allah ki yi ha uri kin ji." Bai ko waiga ba ya fice daga gidansu Hafsat tana ta kwa a mai kira amma ko waigowa bai ba ya haye motarsa ya fizge ta yabar harabar gun mutane nata kallonsa. Jiddah kuwa cikin lokaci ka an ta koma kalar marassa lafiya, ta lafe kan gado tana nishi sama-sama. Kamar an jeho shi haka ya fa akin ya rungume ta yana kiran sunanta cikin tashin hankali da ru ewa. Da yake ta san matakan kissar bi-da-bi sai ya ji jikinta zafi rau saboda ta ci albasa anya ga idanunta hawaye sun kasa daina zubowa . Sai kawai ya fashe da kuka ya rungume ta yana cewa, "Don Allah ki yafe min, tabbas ban cika al awari ba, na rasa me zan ce maki amma don Allah ki yafe min Princess don Allah ki yi min ha uri nasan Ni na saka ki a damuwa har ciwo ya kamaki don Allah ki yafe min matata." Ita dai sai ara arfin nishinta take tana lumshe idanuwa tamkar zata sume baki aya abin da ya haukata shi kenan ya auke ta ya fice cikin tsananin tashin hankali da ru ewa. Kai tsaye wani asibitin ku i ya kai ta wanda sai wane da wane ke zuwa, cikin kulawa aka auke ta bisa gadon marassa lafiya aka nufi emergency room da ita. Zaman an bori Mustapha ya yi ya dafe kansa, a daidai lokacin kiran Barista Alawiyya ya shigo wayarsa. Baki aya sai ya rasa inda yake saboda yasan wacece Alawiyya yasan me zata iya aikata wa akan Jiddah. Bai manta kiran da tai mai ba a ranar