Sashe 114
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kar uwa ba daga gareki ba, bayan na gama bin dangi da abokaina na bayyana masu ke a matsayin abokiyar rayuwata." Ajiyar zuciya tai, shi kam fes da shi gwanin sha'awa, amma sam kalamansa basu birgeta, ita a kalaman da ake fa a indai na soyayya ne to na bakin Prince ne kawai ke birgeta sune kawai ke saka ta nisha i, amma darga ba bakinsa ba duk wanda zai gaya mata kalaman auna ranta aci yake sam bata jin ko da i suna yi mata, yanzu ta ji ta gundura da zama kusa da mutum indai ya fara yi mata maganar soyayya yanzu ta ji ta tsani magana da mutum. Don haka ta tsuke fuska tai shiru bata ce mai komai ba sai shi ka ai ke zuba kamar Kanyar da babu da A nashi angaren ma mamakin kansa yake da kansa wai Yau shi ne a gaban mace yake ta magana ko kallo ga alama bai isheta ba, ya fahimci baki aya ta takura da zamansa a gun don haka ta kasa ko furta mai kalma guda irin wadda yake furta mata. Maimakon ya ji haushi ko ya ji cewar bata kyauta mai ba, sai ya sake ji har a asan zuciyarsa cewa ya yi mata, yanzu ne aurenshi ya zo, domin yanzu ne ya samu irin macen da yake ta lalube shekara da shekaru bai samu ba. Yana son macen da tasan kanta, tasan martabar ta da ajinta mai tsare gida ko da yaushe, sannan wadda bata son abin duniya bai dame ta ba sam, tun da ya ganta yake bibiyarta don kawai ya fahimci halayenta, ya sha mamakin gaske lokacin daya tattara jawabai kanta, bai sake mamaki ba sai Yau da ya zo ya iske kyawawan yaranta suka tabbatar mai da cewa ita in mahaifiyarsu ce, ko a jikinta ba a gane cewar ta ta a aure, lallai ya yi masifar samun dacen matar aure mai matu ar tsada da wahala a wannan arnin da ake ciki. Jiddah kuwa ganin ya tasa ta gaba sai wasu surutai yake wa anda ba abin da suke saka ta sai ciwon kai ta dube shi ta an muskuta tace, "Ranka ya da e naga sa on ka na yi matu ar farin ciki, ina addu'ar Allah Ya saka maka da alheri Ya baka abin da kake nema." Murmushi ya yi, ko shakka babu ya ji da in addu'ar da tai mai, hakan ma wata alama ce ta bayyana cewar ya samu Mar'atussaliha. Yana dubanta kamar kar ta daina magana saboda yadda muryarta ke saka shi nisha i. Da yar ya samu ya ce mata, "Kar da ki samu damuwa Special komai nawa naki ne, don haka ba godiya a tsakaninmu." Jin ya ambace ta da suna Special sai da ta ja tsaki a cikin zuciyarta, sai ta ji sunan ba wani da i haka zalika bai ma bada wata ma'ana ta azo a gani ba. "Special ina so don Allah ki taimake Ni kar da ki barni, idan kika barni tabbas kin ida kashe bishiyar da ta fara bushewa daman samuwarki ce tasa ta fara yabanya." Kanta na a asa ko kallonsa bata iya yi, saboda Prince ne kawai take iya jure kallo ko da za su kwana su yini ba zata ji ta gaji ba, haka zalika ana yawan cewa idan aka cika kallon mutum ana ganin muninsa to ita dai duk lokacin da take kallon Prince ara mata kyau yake sosai ta ji yana bala'in birgeta har bata iya auke ido daga kallonsa, mafi yawan lokuta ba san lokacin da take tambayarsa ba shin yasan yana da kyau kuwa? Tabbas da gaske take yana matu ar yi mata kyau na gasken-gaske. Ganin ya jefa ta a tunani yasa ya mi e tsaye yana kallon fuskarta ya ce, "To Special Ni zan wuce ina fatan zan ji kyakkyawan labari daga zuciyarki ta hanyar bakinki ko rubutunki?" Sai taji wasai da ya tashi zai tafi har ta saki murmushin jin da in tafiyarsa, wanda shi kuma sai ya auka na abin da ya ce ne yasa ta murmushin wanda hakan na nufin zai ji abin kirki kenan. Tana kallonsa ya isa gun motarsa, da hanzari wani ya taso ya bu e mai gidan baya ya shige sai kuma ta ga mutumin ya fito da akwati biyu ya nufi inda take. Kamar ta shige cikin gidan haka taji, don ta tsani kyautar soyayya indai bata Prince inta bace ba. Kamar ya sani sai taga ya wuce ta ya nufi cikin gidan kai tsaye da kayan, don haka sai ta bishi baya kawai. Yana kallonta yana kallon yadda ta ata rai ganin an fito da kayan, sai abin ya sashi murmushi, da gani ta ware a shagwa a yarinyar. ofar akinta ta nuna mai ya aje mata, ya juya, ita ma ta shige akinta ko kallon kayan ba tai ba, wanka tai kai tsaye ta fito ta saka doguwar riga marar nauyi ta janyo wayarta don ta ga ko Prince ya kira ta ko ya turo mata sa Ilai kuwa kira goma sha biyar na shi sai kira biyu na Alawiyya sai kira aya na Mama kira biyu na Maryam awarta ta Kano ma wabciyar Prince ko tace awa ga matar Prince. Tai mamakin kiran Maryam don sun jima ba su yi waya ba, amma sai ta fara kiran Prince don kiransa duk yafi na sauran yawa. Yana auka kamar ya fashe da kuka ya ce, "Haba Princess don Allah ki dinga jin tausayina mana, don Allah ki daina azabtar da Ni haka nan wallahi ji nake tamkar na mutu idan na kira ki baki auka ba sai na ji tamkar wani ne ya zo ki ka je kika manta da Ni." Murmushi tai, don ta saba yanzu duk lokacin da wani ya kira ta a waya ko ya tsaida ta ya yi mata maganar yana sonta sai Prince ya yi mata orafi ya ce mata ya ji alamar wani na sonta. Don haka sai ta share tace mai, "No Prince wallahi ba haka bane ba, ina can gun Alawiyya zata tafi gida,muna bankwana shi ne fa sai yanzu suka tafi na dawo cikin gida na shigo aki na iske miss call in." Tana jin ajiyar zuciyarsa alamar ya samu kwanciyar hankali jin kalamanta, don haka sai ya ce, "Kwantar da Ni kawai za ki yi Princess ai nasan daman ba za ki ta a bari na kama ki da laifi ba, amma ke kin iya kama mutane da laifi." Cikin dariyar samun nasara kanshi tace, "Amma dai Prince kasan cewa kafin na kwantar da kai, ai kai ka jima da halakar da Ni ko?" Shima cikin shagwa ar ya ce, "Princess shike nan naji amma dai ki sani nafi ki kulawa da aunar nan tamu, don nasan da za a fiddo su duka a auna to tabbas tawa sai ta fi taki yawa nesa ba kusa ba." Har tana diddira afa gun magana alamar shagwa ar tai nisa tace, "Ni... Ni... Ni...ba zan yadda da wannan maganar ba, ta ya ma za ai kace wai ka fini bayan ko da yaushe nice mai magana kan baka min waya akan lokaci baka turamin sa o a kan lokaci to shi ne za ka ce wani taka ta tafi tawa yawa?" Cike da nisha i yake sauraren muryarta ji yake tamkar ya fito da ita daga wayar tsabar son ganinta da yake, muryarta na saukar ma shi da kasala jin barcin nisha i yake duk lokacin da take mai irin wannan shagwa Anya kuwa akwai mazan da su kai dacen da ya yi ma samun mata kamar Jiddah? Gata da natsuwa gata da hankali sannan tasan abin da take, mafi yawan lokuta ita ke ba shi shawara idan wani abu ya faru haka zalika tana matu ar son cigabansa ko da yaushe tunaninta idan kai kaza kai kaza Prince za a aru don Allah ka jaraba yi man. Duk acin ran da yake fuskanta mantawa yake yanzu daya tuna da yana da yana da Jiddah sai ya ji komai za ai mai ba komai ya manta ma sam. Haka yanzu ya kawo idanu ya zubama matansa duk abin da suke bai tanka masu ko kallo basu ishe shi ba, shi dai yasan yana fita duk wani ha insu don haka duk abin da suke yanzu bai ata mai rai, ko ranshi ya aci ma yana kiranta a waya sai ta saka shi cikin farin ciki don haka shi yanzu ta auren su kawai yake bata haukan da suke zuba mai ba a cikin gida. Duk yana sane da yadda suke zuwa suna mai arya gun mutane suna zubar mai da mutunci duk yana sane amma yasan dai cewa Allah shi ne shaida kan abin da ke faruwa a gidansa don haka duk masu zaginsa da masu cewa bai ri on aure duk ya barsu da Allah , saboda shi ne kawai wanda zai saka mai kan ananan maganganun da ake binshi da su, duk da yasan hada laifin matan nasa amma ai mutane ya kamata su yi mai adalci su dinga tunawa da cewa duk macen da take zaune gidan mijinta kuma tana i irarin yana zaluntar ta arya take tunda ba aure ta ya yi ba, haka zalika ai babu yadda za ai ace namiji ne kawai mai laifi ban da mace a zaman aure. Jin ya tafi duniyar tunanin da tasan ba makawa na iyalanshi ne yasa ta sauya firar zuwa ta tsokana tace, "Yawwa Prince ba jiya kaban labarin yarinyar da tace tana sonka ba? To har zuwa yanzu ban gama tsinewa idanunta albarka ba da suka hango mata kai, don da ace zan ganta ba shakka sai naji dalilin da yasa take sonka ana zaman lafiya kawai." Magana take ba alamar wasa da jin muryar yasan bata fara'a take maganar sai ya ji ya ru e baki aya don haka ya sake gyara kwanciyarsa bai damu da Hafsat dake tsaye kansa ba tana ta jan tsaki ba, tana cewa wane dare ne Jemage bai gani ba." Cikin lallashinta ya ce, "Princess don Allah ki manta da wancan shirmen yarinyar na rantse maki da Allah ban bari ma an jima ba a nan gun nace mata ta nemi daidai