← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 133

Sashe 75

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an'uwa a Kanon ya je gunsu. Haka yai ta yawo ga yunwa ga ishirwa na azabtar da shi, ganin ba Sarki sai Allah yasa ya fito da an ku insa ya nemi abinci ya ci ya sha ruwa ya kwanta asan wata rumfa don ya huta gajiyar dake jikinsa. Nan da nan barci ya kwashe shi. Ashe rumfar wata mahaukaciya ce ya kwanta yana barci bai sani ba, ita kuma ta tafi neman yarinyarta da wani mutum ya wace mata, kun san mahaukata da son ansu, don haka tana dawowa taga Deeni kwance wajenta sai taga kamar wanda ya wace mata yarta ne, don haka ta samu aton dutsenta ta sauke mai shi a fuska. Kawai azabar zafi ya ji wadda bai san ko ta miye ba da farko sai daga baya sai ya fahimci ashe ransa ne ke niyyar fita, domin ance mai duk lokacin da rai zai fita ciwo na musamman ke ziyarar mutum wanda bai ta a jin irinsa ba. Hakan yasa ya auka ajalinsa ne kawai ya zo, don haka ya sada ar kawai. Ita kuma mahaukaciyar ganin ya i tashi ya ruga kamar yadda duk wanda ta jefa yake rugawa sai ta auka ko wani abun zai sake wace mata don haka ta sake aukar wani tsohon kwano dake aje cikin tarkacen kayanta ta buga mai shi. Tabbas daman yasan shi da shiga aljanna sai Jiddah ta yafe mai, domin Allah bai yafe ha in wani akan wani daman ya sha ji gun Malamai. Mutane ne suka lura da abin dake faruwa, suka yi hanzarin shiga tsakaninsu suka wace shi lokacin duk Deeni ya gama galabaita sosai jini duk ya ata mai jiki, a haka ne wani ya samu damar auke sauran ku in dake jikin Deeni. Bayan kowa ya watse daga gun ne Deeni ya lalla a ya tashi ya isa gefen wani gajeri da mutane ke ta gyare-gyaren motoci, mashina, yana isa ya nemi taimakon abin da zai ci, da yake sun ri e da yadda mai shagon ke son taimakon mutane hakan yasa suka ba shi abinci da ruwa suka kawo an canji suka ba shi , ya yi godiya sosai ya kama hanyar komawa gidan Hajjo. Hajjo ta auka Deeni ya tafi don haka ta zauna tana ta jajanta lamarin har tana cewa ba mamaki ba ko wani mugun abin ya unso ya kawo wa Jiddah Allah Ya addara bata nan don mugun nufinsa ya koma kansa. Jin sallamarsa yasa Hajjo zabura ba kamar data ganshi cikin mayuwacin hali duk jini a jikinsa. Cike da tashin hankali take cewa, "Yau naga ikon Allah! Wata masifar ka je ka kwaso ka dawo min nan kuma? To wallahi na rantse da Allah ka zo ka fice min daga gida kafin na kira a zo a fitar min da kai daga gidana kafin ka haifar min da wata tsiyar, domin kai duk inda kake ba a saka ran ganin alheri ka zama abin da ka zama, don haka ba dai gidana ba wallahi can ka je ka nemi inda matar taka take ku daidaita amma ba dai nan gidan ba." Deeni ya tsugunna hawaye na zubowa kamar ba Deeni ba, ya dinga ba Hajjo ha uri, yana cewa, "Don Allah ki yi ha uri Hajjo ki ban dama na zauna a nan na jira zuwan matata, sai mu tafi tare don Allah ki min wannan alfarmar don Allah." Hajjo ta zaro idanuwa waje tana are mai kallon mamaki, kamar kuma na tsoro tace, "La La La! Wallahi ba zan lamunce ba, ka manta lokacin da Jiddah ta haihu muka je suna wula ancin daka zuba mana ne? Kiri - iri ka dinga tsallake mutane don azabar rashin kunya da nuna mana kai tataccen marar mutunci ne ka dinga kwana cikin akin yarinyar jego ka hana uwarta kwana da ita cikin gata da mutunci kamar yadda ake ma kowace yarinya?" Deeni ya sake sadda kansa asa yana cewa, "Wallahi duk sharrin shaidan ne Hajjo, amma yanzu mun rabu insha Allah ba zan sake hakan ba, idan ma kin ce ta dinga dawowa nan gunki tai wankan jegon wallahi da kaina zan kawo maki ita na rantse maki da Allah Hajjo ba zan karya al awarin nan ba." Hajjo ta sake ha e rai sosai ta dube shi tace, "Wai ni kam ko kaima ka fara an shaye-shayen nan ne Deeni? To idan ba an shaye-shaye ba waye zai maganar da kai? Allah na tuba ko miji Jiddah ta rasa ai gwara ta are rayuwarta tana gadin masallaci da dai ta koma gidanka." Deeni ya dubi Hajjo ya ce, "To don Allah ki kira min ita a waya naji me zata ce, sai na tafi idan tace na tafi, duk da nasan da wahalar gaske JIDDAHH ta ji na zo har Kano gunta batai farin ciki ba." Hajjo ta ta e baki ta fito da wayarta ta kira wayar Jiddar sai dai har ta tsinke bata aga ba, don haka ta kira ta Mustapha tana shiga kuwa ya auka. "Yawwa, don Allah ka ba Jiddah wayar nan na kira layinta bata auka ba, tai ma Deeni magana ya bar min gida wai zai jiranta har ta dawo a nan gidan su tafi tare Ni kuma ba zan yadda da hakan ba." Duk lokacin da aka ambaci sunan Deeni tafasa zuciyarsa ke yi, duk lokacin da akai maganar Deeni jin tsanarsa yake ara ji, duk lokacin da ya tuna shig r saurin da Deeni ya yi mai haushi yake ji ba kamar da ya aure ta ya kasa yi mata adalci abin yafi yi mai ciwo sosai. Hajjo tace, "Kana jina kuwa Mustapha?" Deeni ya dubi Hajjo da alamar damuwa fal a fuskarsa ya ce, "Wai waye wannan Mustapha da yake tare da ita ne? Ko rannan fa shi kika kira madadinta, wa ya bata ikon tafiya da wani ato har wani gari?" Hajjo dai bata tanka mai ba, amma da yake wayar a amsa kuwwa take Mustapha ya ji abin da Deeni ya ce, shi ma a matu ar fusace ya ce, "Kai Sakarai tsaya matsayinka ba ruwanka da harkata, idan ka sake ka ce zaka yi min sakarci tabbas Ni ba irin Salim bane ba tsab zan koya maka hankali. Kuma daga yanzu kada ka sake ambatar sunan Jiddah balle nawa a bakinka, domin daga Ni har Jiddah babu sa'anka, shawara guda zan baka ita ce ka ruga ka oye domin gatan Jiddah ya bayyana ta ko'ina wanda yana gab da yi ma hukunci iyakar abin da ya shuka mata. Kuma ka sani Jiddah ta barka kamar yadda tabar cikin mahaifiyarta don haka kai ta kanka kafin lokaci ya ure maka." Hajjo ta amshe, "Yo shima ai yasan arya ce ace Jiddah zata koma gidansa, ta koma ya ida kashe ta ko? Ban ta a ganin mugun miji macuci ba irin shi ba, shi ne yanzu zai kwaso jiki duk dau a wai ya zo maida Jiddah. To wannan karon ko ubanta bai isa ya ce zai iko da ita ba ya maida ta gidanka ba, idan kuwa ya ce zai maidata to kotu ce zata raba mu da shi." Duk Mustapha najin me tace, don haka ya ara da cewa, "Hajjo maza ya bar gidan nan kuma kada ki sake kirana don Allah kan shi." Ya kashe wayarsa yana jin matu ar takaicin Deenin. Jiddah na tsaye yake wayar da farko ta auka da iyalinsa yake wayar sai kuma ta fahimci a kan ta yake wayar, kawai ta yi mamaki da taji ya ambaci Deeni ba dai Deeni ne ya dawo maidata ba? Tabbas wannan lokacin zata ba iyayenta mamaki idan har suka ce za su maidata gidan Deeni. Lokacin ya sauya, ya kamata ta fara watarwa kanta anci tun a gun iyayenta kafin ta je ga kowa, waye Deeni? Ita daman can ba don shi take ba, kawai tayi biyayya ne ta aure shi don kawai ta zauna lafiya da iyayenta, duk da cewar akwai za in ranta a zuciyarta amma haka ta manta da shi sai dai a mafarki kawai take ganin soyayya ba a zahiri ba. Juya wa tai ta koma ba tare da ta ce komai ba, da kallo Mustapha ya bita kafin shi ma ya koma cikin falon don suna zaune ne aka kira shi, yasan jin ya ambaci sunan Hajjo yasa ta biyo shi. Hajjo ta dubi Deeni tace, "kunnenka ya jiye maka abin da aka ce, don haka ka ga shigewa ta akina idan ka so ka tafi idan ka so ka zauna nan tun da taurin kai zaka nuna min irin yadda kake nuna ma jiddar." Ta shige akinta ta turo ta bar shi zaune a nan ya rasa mafita, jiki a sanyaye ya tashi ya fice daga gidan yana jin matu ar takaicin rayuwarsa. Bai san inda za shi ba haka bai da ko sisi balle ya nufi tashar mota, abin ya yi mai yawa shege da hauka. arshe ya nufi kasuwa ga jikinsa ba arfi ya dinga neman dako yana yi ya samu ya tara ku in mota ya koma gida ya jira zuwan Jiddar yasan ta tana da ha uri kuma tunda take da shi bata ta a neman ya sake ta ba, don haka yasan idan ya maidata zata koma cikin farin ciki. Sai da ya yi sati uku sannan ya ha a ku in motar a tasha yake kwana shi ma da yar ya samu aka bar shi yake kwana a tashar. Ranar da zai tafi sai da ya dinga zubar da hawaye, duk ya yi ba i ya rame ya fice hayyacinsa ba lallai bane ka gane shi farat aya ba, saboda ya sauya talauci ya ce mai salamu alaika ga alama kuma ya amsa sallamar. Cikin mota haka ya dinga hawaye har aka sauka, kai tsaye gidansa ya nufa ya iske wani tashin hankalin domin aki guda ya fa a kuma an sace ofofin an auke mai abubuwa da yawa hadda katifarsa da sauran abubuwan amfaninsa. Sai kukan ya tsaya kawai ya zauna ya yi shiru yana kaf rayuwarsa da Jiddah a cikin gidan, kenan dai alhakin Jiddah ne ke bibiyarsa? Kenan Jiddah bata yafe mai ba shi yasa bala'i ke tunkararsa ko da yaushe? Yanzu ina zai ga
Chapter 75 · 0% Book details