Sashe 113
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na gaji da iskancin da take min. Mun yi sati guda ana wannan bala'i kwatsam! Rannan sai jin ihun Aminatu nayi ina zuwa na iske A'isha ta caka mata wu a a ciki , tsabar ru ewa tasa na fisge wu ar daga cikin Aminatu sai kawai jin an sanda nayi a baya na suna cewa "Kar ka matsa daga inda kake ." A kotu ne naji daga bakin Lauyar A'isha wai ta shigar da Ni ara na nayi wa mai aikinta ciki kuma na kashe ta. Nasha ba ar wahala gun shari'ar domin ta auki babbar lauya wadda kowa yasan ta haka sauran Lauyoyi ke shayin buga shari'a da ita watau Barista Alawiyya Bello Gareji, sai da komai nawa ya are amma har yanzu ba a gama shari'ar ba, don Allah ki taimake Ni Jiddah domin naga hotonku ke da Barista Alawiyya ki yi min ari ki fahimtar da ita cewar alhakin ki ke ya kama Ni ban kashe kowa ba." Tun da ya fara bata labarin kanta ke asa har ya gama. Lallai yana cikin matsala ko bai fa a ba jikinsa ya bayyana, kuma insha Allah zatai arin watar mai ha insa. Ta kalle shi tai murmushi tace, "Kar ka damu a wane gari kuke shari'ar ne? Yaushe za ku koma kotun ne?" Cike da farin ciki ya sanar da ita a Kano suke shari'ar Yau saura sati guda su koma Kotun. Tai mai al awarin zata taimaka mai, ko waya bai da ita sai ta zare sim card inta ta ba shi aya daga wayoyinta tace ya ri e zata aiko mai da sabon sim card yanzu idan ta shiga gida don su dinga waya tana jin abubuwan dake faruwa kafin zuwan ranar . Nan ta bar shi yana kallonta irin kallon nadama da mamakin yadda ta koma kamar ba ita ba. Bata jima ba sai ga wata ar aiki ta kawo mai sa on cikin ba ar leda ba aramin mamaki ya bayyana a kan fuskar Abubakar ba ganin iyayen ku i a cikin ledar tare da sim card in sai wata ar takarda da ta rubuta. "Ka je ka samu kaya masu kyau, kuma ka kula da kanka kafin na shigo Kano in." Tana komawa ta iske miss call in Prince dana Yusuf Matashi sai ta fara bin kiran Prince domin yana cikin ranta daman, tana son ta dawo ta kira shi ta ji ko ya tafi inda ya ce mata an tura shi aiki. Kiran farko ya aga kiran har da ajiyar zuciya. "Haba Princess anya kuwa kina jin yadda nake ji kuwa?" ar dariya tai tace, "Ai Prince na fi ka ma jin abin da kake nufi kana ji indai ana so da aunarka ne." "Haba Princess ban ga alama ba, don ko da yaushe Ni ke cikin tararrabin kar ki ku uce min." "La,la,la, Prince haka ma zaka ce yanzu? Duk yadda sonka ya yi min kamun kazar Kuku kace min wai ban kai ka ba? Ni fa na auka ma son da nake maka ya ninninka wanda kake min domin Ni duk abin da nake kana cikin raina." "To ai Princess ban ce baki sona ba, kawai dai na ce nawa yafi naki yawa son." Tasan ko za su shekara ba zai amince da cewar tafi shi son ba don haka ta aje maganar ta je wata. "Yawwa Prince, zan shigo Kano nan da kwana shida insha Allah kan wata shari'a da zan yi." Tana jiyo saukar numfashinsa, ya ce cikin farin ciki, "Ban mu kashe Princess, har kin sakani cikin nisha i da jin da i, duk da ban gari amma zan koma kafin ranar dama na tsara daga nan gun ki nayo kawai na kwashi auna, na ganki naga kyakkyawar fuskarki nai tozali da kwalliyarki mai imauta Ni." Itama cikin farin cikin tace mai, "Ai baka kaini farin ciki ba kan hakan, domin ina son naga na tasa ka a gaba ina ta kallonka ina kallon dogon hancinka, ina kallon fararen idanunka, kana halakar da Ni da murmushinka mai ara jefa min aunarka a sassan jikina." Duk lokacin da Jiddah ke bu e baki tana gaya mai irin kalaman nan sai ya dinga jin tamkar ya bu e ido ya ganshi a bayyanar jama'a ana mai Allah sa alheri an aura masu aure. Yana son soyayya, Jiddah ta iya soyayya, yana son kulawa Jiddah ta iya ba shi kulawa, yana son shagwa a Jiddah ta ware da iya shagwa a don haka duk bayan sakan yake mutuwa yana dawowa kan soyayyarta. "Prince shi ne za kai banza da Ni ka yale Ni ina ta yi maka magana?" Cike da shagwa a take maganar, abin dake ara zuzutar da shi kenan idan yana jinta. Shima cikin nashi salon shagwa ar ya ce mata, "Afuwan Princess ina can ina tunaninki ne shi yasa kin san ko da muna tare a waya indai ba gani ga ki ba sam ban daina tunaninki." Farin ciki ya sake mamaye zuciyarta don haka ta sake gyara kwanciyarta cike da nisha i tace, "Ni kuma ko da yaushe addu'a nake, fata nake so nake Allah Ya ara aukaka min kai, Ya ara maka bu i Ya baka duk abin da kake nema Yasa ka gama lafiya Prince, arshe Ya azurta Ni da samun damar zama mata a gareka." Baki aya sai ya dinga jin wani barcin nisha i nason kwashe shi, Jiddah na matu ar saka shi a farin ciki da nisha i, tasan duk kalaman da yake so tasan duk abin da yake bu ata wanda zai saka shi a farin ciki. Tana ganin kiran Yusuf Matashi tun da suka fara wayar amma bata jin zata iya amsa mai ko tace ma Prince in ana kiranta zata aga kiran,sai ma ta dinga jin haushi. Alawiyya ta shigo cikin shirinta da gani tafiya zatai, ta dubi yadda Jiddah ta saki baki cike da fara'a tana waya tana ta keta dariya sai taji ba zata iya datse mata wayar ba, don da gani tana sakata cikin farin ciki ko da jin yadda take dariyar. Ta gefe guda kuma ji take inama ace ita ce ke da halayen Jiddah gun soyayya? Ina ma ace yadda Jiddah ke zuba soyayya da Prince inta haka ita ma take zubawa da Babansu Anam? Tabbas tana son gwada abubuwa da yawa da Jiddah ke yi ma Prince amma sai taji sam bata iya yadda take yi. Ganin Jiddah bata iya daina wayar ga shi tafiya za su yi sai ta dafa kafa arta tace, "Princess ta Prince za mu wuce mu domin ina da shari'ar da nake yi nan da sati guda." Jiddah tace ma Prince inta "Don Allah ka cigaba da zabga tunanina kafin nayi sallama da Sahibata za su tafi gida yanzu." Yar dariyar da i kashe Ni ya yi ya ce mata, "Ko baki ce ba, ko da yaushe cikin tunaninki nake da kewarki ga begenki dake awainiya da ni ba dare ba rana balle safiya. Ki sallame ta ina jiranki Princess baki da damuwa." Jiddah ta dubi Alawiyya ta kwashe da dariya bayan ta kashe wayar tace, "Ya naganki da shirin tafiya har komai ya daidaita kenan?" Alawiyya ta ata fuska tace, "Ban san iskanci miye na dariya kuma?" Jiddah ta kasa daina dariyarta tace, "Ni fa ba cewa nayi ba ya zo biko ya samu nasara kenan ba, cewa nayi har za ku koma anyi daidaito?" Alawiyya tsab ta fahimci Jiddah so take ta yi mata shegantaka don haka sai ta juya tai ficewarta ba tare da tace mata komai ba. Da sauri Jiddah ta diro daga kan gadon ta bi bayan ta tana bata ha uri. Har sun fice suna ta fara'a tai sauri ta bu e wa Alawiyya ofar motar tace, "Ranki ya da e Allah Ya tsare Ya kiyaye hanya, sauka lafiya mata ga Dr. Uwa ga su Afnah." Duk sun fahimci tsiya take masu, don haka sukai tsit kawai suka wuce, sai da ya tada motar ya le o ya ce mata, "Mu zamu wuce, a gaida mana da Yarima idan ya kira." Da gudu Jiddah ta koma tana dariya, suma suna dariyar suka wuce. Yusuf Matashi shi ne sunan dake kara e kunnuwanta bayan ta aga kiran, sai dai tayi mamakin jin cewar yana ofar gida yana jiranta. Kamar ba zata fita ba, sai kuma ta zari gyalenta ta fice tana jin fa uwar gaba sosai. Tun daga nesa ta hango su Afnah na wasa suna tsalle suna ihu irin abin nayi masu da in nan. auka Baba maigadi ne ke wasa da su, sai da ta fita fili sannan ta hango shi, ya biye masu sai tsere suke a harabar gidan, su ruga bayan waccan motar su koma bayan waccan motar suna ta dariya. Ta jima tsaye tana kallonsu kafin ta ida isa inda suke, suna hango ta kuwa suka rugo inda take suna dariya. Shi kuma ya yi tsaye yana kallonsu cikin farin ciki fal a kan fuskarsa. Yaran ta tura cikin gida ita kuma ta nufi inda take ganawa da ba in ta, saboda bata ta a shigar da ba on ta cikin gidan ba sai dai a harabar gidan, Prince ne kawai yake shiga cikin gidan. A hankali ta isa inda yake zaune yana kallonta, yana sakin murmushi, ji yake tamkar ya ruga ya rungume ta don ta yi bala'in birgeshi, bai tsammaci da gaske ta ta a aure ba, sai da yaran ke fa a mai ita ce Mamansu sannan ya lura da suna kwasar kama da juna. Cikin siririyar murya tai mai sallama ta ja kujera ta zauna, ta sadda kanta asa domin shi ne karon farko da ta fara ha uwa da shi. Kallonta yake yana son fahimtar wane yanayi take amma sam ta i ba shi wannan damar, ta sadda kanta asa ya kasa ganin ko idanunta sai bakinta kawai yake kallo wanda ya sha man baki da gani zai taushi. Cikin natsuwa take gaida shi wanda sai ya ji tamkar a fili muryarta tafi cikin waya da i da za Ganin tai shiru daga gaisuwa ya gyara zamansa yana kallonta ya ce, "Jiddah naga kamar ba ki yi murna da zuwana ba, don Allah kada ki sa naji a raina ban samu