Sashe 132
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta zama a gareni. Ina ganinsa ya kasa shirya wa sai da na taimaka masa da kaina na kira Yayarsa Likita na gaya mata Jiddah bata lafiya tana gidanta kuma ba kowa gidan, nayi hakan ne don nasan tafi kusa da gidan Jiddah akan mu nan, ina zaton kafin ya isa ita ta fara isa kuma zata iya taimaka mata tun da aikinta ne hakan. Har yakai bakin ofa naji ban iya barinsa ya tafi gunta a yadda naji muryarta tabbas tana cikin yanayi gabana ya fa i ban nemi yafiyarta ba kan abubuwan da nayi mata da dama a baya ba don haka nace mai ina zuwa bai musa min ba na bishi muka tafi tare ba wanda ke ma wani magana kowa da abin da ke ransa na damuwa. Muna isa muka iske gidan a bu e naga motar Yayarsa naji sanyi don nasan tana ciki ta rigamu zuwa kamar yadda na yi tsammani. Muna shiga har rige-rigen shiga muke saboda yadda muka jiyo numfashin Jiddah na fita da arfin gaske abin tashin hankali, ita kansa Yayar hawaye take tana danna irjin Jiddah tana son numfashinta ya daidaita amma abin ya ci tura. Ban dakatar da Mustapha ba daga kukan da yake don Ni ma kukan nake sosai na ganin halin da Jiddah ke ciki. Kafin ki ce me Yaya ta kira babban Likita ya iso gidan shi ne ya yi dabarunsu na Likitoci da taimakon Allah numfashinta ya koma daidai amma kallo guda zaka fahimci tana cikin ciwon gaske. Haka muka tasa ta a gaba kowa na kallonta yana addu'a a ranshi, a cikin daren surukaina suka isa gidan abin ya ban mamaki yadda duk da dare ne dangin Mustapha suka cika gidan Jiddah kowa na yabon halayenta sosai jikina ya yi sanyi don nasan Jiddah tai min fintinkau ta ko'ina ba zan ta a kamo ta sai dai nayi koyi da halayenta kawai zan samu rabin yabonta. Mustapha kau nan take shi ma sai da aka saka mai ruwa dan ko mi ewa tsaye ya kasa bai iyawa bakinsa ya datse hannunta kawai yake ri e da shi yana kallonta zuciyarsa na suya. A nan naji labarin cewa Jiddah na auke da aramin ciki wanda shi ne ke bata wahala, wallahi har a raina nayi farin ciki domin nasan abin farin ciki ne samun aruwar zuri'a da Jiddah. Sai asuba sannan Jiddah ta dawo hayyacinta sosai sanan dangin Mustapha suka dinga tafiya su na jera min godiya sosai har kunya ta kamani don ban san godiyar ta mecece ba suke ta jera min irin haka ba, sai naji kamar an sauke min wani dutsi da ya tokare min ahon zuciyata ganin mun shirya da dangin mijina sun sakar min fuska har da wa anda ba mu magana ranar sun yi min magana har da godiya. Bayan sun t afi ne na tashi da nufin girka mata abinci don ance zata bu ata idan ta farka na shiga kicin in ta nai tsaye ina kallon ikon Allah komai tsab wai kicin har da amshi sai naji a raina ina son naga asalin akin Jiddah nasan sai na suma don mamaki, haka na dafa abinci na nufi falon ganin Mustapha na barci ita ma Jiddar sai na wuce kai tsaye akinta a nan fa naga abin da ake kira aljannar duniya don ko a indiya nasan ba kowace mace bace zata iya tsara akinta yadda Jiddah ta tsara nata akinta ba duk da ba wasu tarkace a ciki amma wallahi ya yi min kyau sosai sannan amshin akin daban dana kicin in ta. Tabbas Jiddah bata jerin den mata tana cikin jerin masu tsabtar mata ajin farko, haka nayi ta dube-dube kamar arauniya na wuce toilet nan ma naga ikon Allah don shima amshi na daban yake da sauran da na ji. Na yi alwala don an fara kiran sallah na fito na nufi gun sallar dana ga ta aje farduma da hijabi na auka wallahi amshin hijabin sai da yasa na kasa kabbara sallar don amshin na da matu ar da in sha a sosai, ina gama sallar na nufi gudan akin nasan shi ne na Mustapha tsaye nayi kamar gunki yadda naga ta awa ta akin da kayan ado fiye da nata akin ga amshi mai da in gaske sai na hasko yadda akinsa yake na gidana komai a hargitse a azance wallahi yaban tausai mai kwana a wannan akin yake iya jure kwana a akin gidana sosai naji kunyar kaina da kaina don ban yi ma akina ba ma balle nayi ma nashi akin gyara. Jikina sanyi alau na dawo falon na zauna na zuba masu ido ina kallon su na ara aminta da cewar nayi saken da ba zan ta a gyara shi ba tun da na kasa ri e mijina tun farko duk da nasan me yake so amma sai nake ga kamar iskanci ne da neman ya maida Ni baiwa yasa yake da tsirfar masifar wai yana son soyayya yana son rayuwar jin da i a lokacin baya aukar hakan ne da sunan zai iya raina Ni idan na bari yana samun duk abin da yake so daga gare Ni zai iya maida Ni baiwa ya auka cewar yafi arfina ne. Ashe ba haka bane ba nayi ma kaina sakiyar da ba ruwa sai na samu kaina da goge hawayen nadama a lokacin ne kuma mu kai ido hu u da Jiddah ta tashi cikin yanayin ciwo ta mi o min hannunta na isa inda take na kama hannun ina mata sannu ta tashi da yar ta kalle Ni tace, "Na gode sosai Maman yara Allah Ya saka da alheri, don Allah idan na ta ata maki rai ki gafarta min ba don halayena ba sai don Allah." Wallahi sai na fashe da kuka na rungume ta sosai ina cewa ba ki yi min komai ba Auntyn Yara tun da nake da ke alheri kawai kike nufo Ni da shi na gode na gode sosai Auntyn Yara me za a kawo maki?" Tai murmushi tace "Duk abin da ya samu ina ci Maman Yara." Ashe Mustapha ya tashi sai ji mu kai ya rungume me mu baki aya yana gode wa Allah. In takaita maki labari tun daga ranar komai ya wuce Ni da Jiddah sai alheri yanzu haka ta ban kayan saidawa na ku e masu daraja ta fitar min da ribata mai tsoka ina cikin farin ciki ke da kanki za ki iya shaida hakan ta hanyar kallon gidana da jikina baki aya kin san na samu kwanciyar hankali da natsuwa." Tun da Maryam ta fara ba Hafsat labari sai tai zuru tana kallon Maryam ta bu e baki kenan za tai magana ta ga wata mace ha iyar gaske tare da wasu mata sun shigo amshi ya kaure falon kai tsaye ta nuna Hafsat tace "Ga ta can ku kama ta mu je." Hafsat ta zaro ido waje tana mamakin kamun me za ai mata kuma? Barista Alawiyya tace cikin murmushi "Zan kama ki ne saboda kin je gidan matar aure mai juna biyu kin ci ma mijinta mutunci kuma kin nemi bugun matar gidan duk da cewar tana auke da ciki jikanta, don haka za mu je da ke kotu ki amsa tambayoyi." Maryam tai murmushi sai yanzu ta fahimci abin da ke faruwa, watau daga gidan Jiddah take yanzu haka kuma wannan dukan aikin Jiddah ne bana kowa ba yanzu kuma awar Jiddah za tai nata aikin kenan, lallai ta gode wa Allah da yasa bata da rabon fige kazar wahala ita kam da ta gane gaskiya komai ya wuce. Alawiyya suka gaisa da Maryam cikin mutunci suka fice da Hafsat tana ta hayagaga sai ga Mustapha zai shiga gidan ita kuma Jiddah ta nufi gidan Hajjo, tamkar bata san komai ba haka Jiddah ta nuna tai shivewarta gidan Hajjo Mustapha ya girgiza kai yasan ita ce tasa Alawiyya ta kama Hafsat don yana jin tana waya har tada jijiyar wuya take idan Alawiyya bata watarwa mijinta ha insa ba na taka doka da Hafsat tai ba ita zata zauna kotun da kanta duk da cewar tana cikin kwaikwan ciki mai wahalar gaske. Maryam ta taso da sauri ta shige jikin Mustapha tana mai sannu da zuwa tana wasa da gemunsa ya amsa yana jin kamar ba shi ne ba ke da mata har biyu kyawawan gaske ga su duk su na nuna mai kulawa da natsuwa cike da soyayyar da yake mafarkin samu a mafarki yau ya same ta a zahiri daga dukkan matansa. Jiddah kuwa ta sha yininta gidan Hajjo har yara suka dawo daga makaranta suka shigo gunta abin cike da birgewa Hajjo baki ya i rufuwa yau Jiddah na rayuwar aure cike da farin ciki ba ba in cikin miji balle na kishiya dangin mijinta kowa sonta yake. Wani yaro ya shigo ya ce ana sallama da maigidan in ji wani dattijo a nan ofar gida. Hajjo ta kalli Jiddah sai kuma ta auki hijabinta tace "Kada na tura ki ban sani ba ko arayin mutane ne mijinki ya baje Ni nan ya ce da sa hannuna don naga yana iya kaiwa kowa duka a kan ki." Jiddah tai dariya tana cigaba da shan faten tsakin da Hajjo tai mata mai daddawa. Ba a jima ba sai ga Hajjo ta dawo wani tsoho na bayanta kallo guda Jiddah tai mai ta sadda kanta asa hawaye suka cika mata ido har dai suka fara gangarowa kan kumatunta. Baban Jiddah ya kalleta da kyau ya fashe da kuka sosai yana ambatar sunanta, "Hawwa'u ke ce nan nake gani haka? Don Allah ki yafe min ki gafarta min abin da nayi maki don Allah Hawwa'u... Kuka ya ci karfinsa sosai ya kasa magana sai tashin kukansa. Mustapha ya shigo gidan kai tsaye idonsa kan matarsa ya sauka ya ganta tana kuka hadda shessheka ya kuwa daka tsalle ya isa gabanta yana tambayar me akai mata? Me ke mata ciwo? A zafafe ya kalli Hajjo ya ce, "Ba zata sake zuwa gidan nan ba tun da kuka kike saka ta insha Allah ina son farin cikin matata fiye dana kowa wallahi." Hajjo tai murmushi tace "To mai mata ba Ni na sa ta kuka ba Babanta ne