← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 133

Sashe 85

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

taka a hankali ta kalli Fatima tace, "Kotu nasan jin asalin labarinki domin ta ji ta inda kika ha u da Marigayin bayan ke a Lagos kike shi kuma yana Kaduna." Kotu tai tsit bayan Fatima ta gama bayyana asalin labarinta baki aya, nan take aka ga Al ali ya fice zuwa akinsa na hutu ya rufo bai ce komai ba. Jama'a da dama kuke suke suna arawa da suka ji irin wahalar da Fatima ta sha a rayuwarta, sai kuma aka dinga tambayar ina su kishiyoyin nata su ke? Tabbas ko makaho yasan cewa ba Fatima bace ta kashe mijinta ba su ne suka kashe mata miji don rashin tausayi suka auke mata yara anana. Tunda ya shige yake goge zufa ya dawo goge hawaye masu zafin gaske da suke zuba mai. Wace irin rayuwa ce wannan zai kashe anwarsa da kansa don kawai abin duniya? Ashe dama Fatima anwarsa ce da hatsarin mota ya raba su? Ashe daman Fatima na raye sun auka ta mutu ai. Ya tashi da sauri ya jawo wayarsa ya kira wata lamba, ana agawa ya ce cikin muryar kuka, "Dada kun ga shari'ar Yau da ake gudanarwa kuwa?" Tsohuwar cikin kuka tace "Tabbas naga Auta ta Muntasir na gane ta ashe dama ban gaya maku ba tana raye bata mutu ba? Daman ban sha cewa ku nemo min Auta ta ba ina yawan mafarkinta ba? Don Allah kai maza ka kawo min Auta ta ko Ni na zo da kaina kotun yanzu." Cike da farin gane anwarsa yake gaya ma mahaifiyarsa ta zauna yanzu zai kawo mata iyarta har gida ba sai ta zo ba. Can kotu kuma ganin Al ali ya tashi ya shige bai magana ba sai abin ya ba kowa mamaki, mutane da dama kuma suka auka tsabar tausayin Fatima ne yasa Al ali kuka don haka ya kauce wa idanun mutane don ya koka mata lamarin rayuwar tata. Barista Alawiyya ta dubi Jiddah a an ru e tace, "Ban fa gane abin da ke faruwa ba Jiddah yi min bayani." Barista Jiddah ta dubi Alawiyyar ita ma tace, "Tabbas wani abu zai faru amma ban san ko miye ba, sai dai mu jira kawai." Fitowar Al ali ce tasa kowa ya natsu aka cigaba da gwabzawa. ali ya dubi Fatima, "Shin yanzu ina kishiyoyin naki su ke?" Fatima cikin natsuwa tai kwatancen unguwarsu don tasan ba inda za su je suna gida. ali ya bada umarnin a je a zo da su yanzu. Barista Jiddah ta dubi Al ali tace, "Zan gabatar da hujjojina wanda nake fatan daga su kotu zata huta daga wannan kai da kawowar da ake ana wahalar da baiwar Allah da bata ji bata gani ba, ta dubi wasu an sanda tace masu, "Kuna iya shigowa da su yanzu kotu nada bukatar su a nan." Nan take sai ga su Oga Dauda an shigo da su ga yaran suma an kawo su amma har zuwa yanzu barcin dai su ke na sihiri. Barista Jiddah ta matsa gaban Oga Dauda tace, "Kotu nasan jin ta bakinka akan mutuwar mijin waccan baiwar Allah mai suna Fatima." Oga Dauda ya gyara tsayuwarsa bayan an ba shi Alkur'ani ya rantse ya zayyana komai ya sani har da rana da lokacin da suka kashe shi sai da ya fa Kotu ta auki kabbara baki aya. Daidai lokacin aka shigo da su Hajiya Turai sai zare idanuwa suke. Ana tsaida su gaban Al ali suka fara zayyana duk abin da sukai, suna gamawa suka fara ihu suna dariya alamar sun haukace. Kotu ta bada umarnin a kaisu gidan mahaukata ai masu magani sai ai masu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Shi kuma Oga Dauda aka yanke mai hukuncin zaman gidan yari na har arshen rayuwarsa shi da mutanensa. Ya kalli Barista Alawiyya ya ce, "Don Allah ki yi min alfarma guda ki kula min da abin da ke cikin masoyiyata idan ta haihu ko miye na baki shi karda ki bari ya yi halina don Allah ya zama mutumin kirki ko na samu sau in azabar kabari idan yana min addu'a." Barista Alawiyya ta amince mai, aka wuce da shi yana yi mata godiya sosai. Bayan kotu ta watse Al ali ya dubi Fatima sosai ya ce, "Shin za ki iya tuna wata rayuwa a wata asa a wani bigire a wani babban gida mai auke da mata da miji da yaransu hu u maza da mace guda wa anda fa an boko haram ya tarwatsa su yasa suka bar asar su zuwa asar Maradi a can ma basu tsira ba sai da suka sake yin gudun hijira zuwa Nigeria akan hanyarsu motar tai hatsari... Sai Fatima ta fashe da kuka sosai ta mi e tsaye tana nuna shi da yatsa tace, "Kana nufin Yaya Mansur ne kai? Ashe daman baka mutu ba kaima kana raye?" Ya kama hannunta ya ri e gam yana kuka ya ce, "Ba Ni ka ai ba duk muna raye ku biyu kawai muka rasa a ranar ke da iyar Yaya Amadu Hafsat ku ka ai muka nema muka rasa sai aka ce mana kun one don haka muka ha ura amma Dada bata yarda da hakan ba tana yawan cewa tana mafarkinki kina raye ashe kuwa da gaskiyarta kina raye Fatima." Nan da nan Alawiyya ta rungume Mamarta tana tayata murnar gane ahalinta, tsohuwa ma sai kukan da i take jin ahalin Fatima na raye har ga Yayanta. Daga nan suka tattara baki aya suka nufi gidansu Fatima, a unguwar Malamai gida mai girman gaske wanda kana gani kasan masu shi sun tara abin duniya iyakar tarawa. Suna shiga suka iske baki aya dangi sun ha u ana jiran zuwan Fatima. Bayan an gama koke-koke ne Fatima ta sake basu labarinta ta nuna masu Alawiyya da mahaifinta. Ita ma Alawiyya ta basu labarinta dana Baba Hassu nan take kowa ya kama kukan rashin Hafsat iyar babban Ya ansu Fatima. Daga nan sai aka koma kan Jiddah ba wanda bai tausayawa rayuwarta ba ita ma, don har babban Ya ansu Fatima ya ce, "Tunda Babanki bai sonki Ni ina sonki don haka na auke ki matsayin Hafsat kuma za ki cigaba da zama a wajena ni ne zan auradda ke." Sosai Alawiyya ta ji da in lamarin ban da Dr Faisal da Mustapha don sun hango wani babban alubale na shiga tsakaninsu da ita kuma Al ali ya samu wata babbar damar mallakar ta cikin sau Kowa ya watse aka bar Fatima da mahaifiyarta don su gana. Abin da ya ta a zuciyar Jiddah kenan ganin yadda Alawiyya ke cikin farin ciki tare da iyayenta suna sonta ita kau bata ma san inda nata mahaifin yake ba ta kama kuka. Mustapha ma a akinsa sai cakusawa yake da Maryam sai ruwan bala'i take mai ta gaji da zaman kishi da Hafsah sai dai ya zo ya za i guda a cikinsu kawai. Shi kam abin ma ya yi mai yawa, yanzu kam ji yake komai ya ara yi mai girma, ada ya fara mantawa da matsalar iyalinsa da yana tare da Jiddah ko da kiransa su kai sukai mai halin nasu yana aje wayar yake mantawa ba kamar idan ya kalli akin jiddar sai ya ji ba komai su suka sani sui ta yi ma koma miye ya daina damuwa shi da zai mallaki kamar Jiddah miye nashi na nuna damuwa da lamarin su? Hakan yasa ya ara iba ya yi haske kamar ba shi ba, yanzu kuma ga shi yana hango wani tarna i na niyyar gitta wa a tsakaninsa da farin cikinsa da Jiddah. Tabbas ba zai iya barin Jiddah ta su uce mai ba ko da kuwa zai rasa komai yasan idan ya dace da Jiddah a hankali zai maida komai nasa har ma ya samu cigaba. ali kuwa yana komawa gidansa matarsa ta nufe shi da jarida cike da acin rai ta wurga mai tace, "Ita kuma wannan daga wane jirgin ka kwaso ta? Kai yanzu ko kunya baka ji kake soyayya da sa'ar iyarka?" auka ya duba sai ga hoton Jiddah lokacin da take kashe shi da murmushin nan a kotu, sai ya ji kamar lokacin take mai murmushin bai san lokacin da ya saki nashi murmushin ba ya manta da gaban matarsa yake ma. Ta kuwa fisge jaridar ta yaga ta shige akinta tana cewa "An dai ji kunya idan an san ta, sai kuma ka yi mu gani idan tusa na kunna wuta." Shi kam farin ciki yasa shi zama a gun yana ara hasko fuskar Jiddah a idanunsa. Alawiyya ta iske Jiddah nata kuka tai ta lallashinta ko bata tambaya ba tasan kukan mahaifinta take sai ta sake jin cewar ya kamata ta gano duk inda yake domin ta tunatar da shi darajar a a rayuwarsa. Sai da su kai sati guda cif sannan aka maida auren Fatima da Baban Alawiyya suka taho baki aya Kano da danginta don zuwa su ga inda ar'uwarsu zata zauna, yaranta kuwa su Hassan tuni aka kai su gun wani Malami ya yi masu addu'a sai ga su sun tashi daga barcin da su ke cike da oshin lafiya.
Chapter 85 · 0% Book details