← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 133

Sashe 17

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 14 Ganin na afe gun, bakina ya kasa ko motsawa ya daka min tsawa da muryar takaici yace, "To wallahi ba zan iya bar maki nawa ku in ba, kuma ni ba an aike bane balle ki tasani gaba da aikenki wacece ke? Idan za ki ban ku i duka ki ban kawai na gaya maki ban da ku i ne da ina da su me zan ci da Naira ari biyar in ki in banza." Ganin dai idan ba da gaske nayi ba tabbas ba zan samu ari biyar in tashi ba nima tawa ta shige don haka nace cikin muryar son yi kuka nace, "Don Allah ka rufa min asiri karka amshe ku in nan duka, domin kaga mutane zaune tsabar gida, suna jiran a basu aiki kuma babu abin da aka samu aka basu, don Allah ka taimaka ka ara min taka ari biyar in gobe idan na samu sai na maido maka abinka." Wani kallon galala ya bini da shi, kamar ya kife ni da mari yace, "Ke amma dai kin ci kai ko? Ni nace daman ki tara mutanen? Ban da shegiyar gulma daman miye na tara min mutane cikin gida kamar uban wani yaban ajiyar abin da zan ba su? To tun kafin ranki ya aci ma ki je ki cewa kowace magulmaciyar mace ta fice min daga gida babu abin da zan kawo na aiki Ni, idan kuma ki kai shiru ke za ki ji kunya cikin mutane." Hawaye suka zubo min ban ha ura ba nace, "Don girman Allah kai ha uri ka bar min nawa ku in to sai na samu ko ruwa ne na siya kafin muga me anjima zatai don Allah." Tsaki ya yi ya amshe dubun ya saka a aljihu yace, "Ke dai ce abar ji ke sauran jaje ya rage wa." Ficewa ya yi ya barni gun na daskare hawaye na zubowa a idanu na, ji nake me yasa ma kasance a raye? Me yasa ban sake guduwa ba kamar yadda muka gudu daga Iyami? Me yasa na zauna gidan Deeni har na samu ciki ? Me yasa ban bi duniya ba? Tabbas nayi ma kaina babban rashin kyautawa tunda har na kai matsayin aje yaro ina zan je kuma yanzu?" Kukan gaske ya zo min har na falo na jiyo sautin kukana. Ko ban fa i ba nasan matan unguwarmu sun samu abin tattaunawa a cikin unguwa a haihuwar... "Jiddah me ye abin da ya yi zafi za ki zauna nan ki dinga rusa kuka ke da Allah Ya azurta da samun kyautar an mutum?" Yayar mahaifiyata ce ke min maganar, ta jima tana min nasiha, muna cikin hakan muka ji mutane na cewa "Oyoyo ga mutanen Kano." Ni da Inna bamu san wa ya riga fita ba wajen ba domin mun fahimci Hajjo ce ta zo. Yara ke ta shigowa da kayan abinci da kayan miya da abubuwa iri-iri kamar daga sama. Ban sake tsinkewa da lamarin ba sai da naga an shigo da buhun shinkafa buhun dawa buhun gero buhun fulawa da jarkar manja data farin mai , hatta magi kala-kala aka shigo da su. Sai da aka gama shigowa da komai sannan Hajjo ta shigo auke da akwatin kaya da atuwar leda . Mutane nata yi mata sannu, nikam tashi nayi da gudu na afka jikinta na fashe da kuka mai ta a zuciya. "Haba Jiddah miye na kukan kuma tunda ga Ni? Kin san ban san kina kuka ko? Share hawayenki ki amshi sa on Uncle Salim inki." Ai kukan kamar ara turomin shi ake baki aya kukana ya saka jikin kowa sanyi harda Hajjon itama ta fara share hawaye tana cewa, "Ki dai ara ha uri Jiddah Allah na nan bai manta da ke ba, tabbas gaba sai kin ba kowa mamaki." Sai da Hajjo ta ga na natsu sannan ta bu e akwatin kayan jarirai ne masu kyau da tsada har da pampas aton gaske, ledar kuma atamfofi ne da leshi tare da shadda dukkansu a inke suke. Hajjo ta dube ni tace "Wannan in ji Uncle Salim inki yace yana gaida ki sosai." Nan da nan akai ta aga kayan ana saka albarka, Hajjo ta fice waje ta dinga ware kayan da duk za ai amfani da shi nan take ta fasa buhun shinkafar ta iba tace a ora girki duk ga mutane zaune ana aikin ana cin abinci ai aikin yafi da i da sauri. Nan da nan kuwa gida ya cika da mutane ana ta aikace-aikace kamar ranar sunan ma. in cikina ya kau, komai ya zama tarihi na angaren kayan abinci da kayan da za mu yi fitar suna Ni da Yarona. Sai tunanin abin yanka ya dawo ya yi min zaune a cikin zuciyata don haka sai jikina ya yi sanyi don banga alamar Deeni zai yanka min ko bindi ba balle Rago ko Akuya. Hajjo ta jani inda ba mutane tace, "Jiddah Mahaifiyarki ta kirani a waya ta gayamin halin da kike ciki duka, tabbas na girgiza sosai me yasa dangin mahaifinki basu da tunani ne? Me ye amfanin yi maki aure da wanda bai da tsayayyen aiki ko sana'a? Me yasa basu dinga taimakonki tunda su sukai maki auren? Yanzu me ya rage ba ai ba na hidimar sunan?" Cikin ajiyar zuciya nace "Babu abin yanka (Rago) don ban ganshi ba haka bai min maganar akwai ko babu ba." Hajjo ta girgiza kai tace, "Wannan kuma shi ta shafa kada Allah Yasa ya yanka ai yaronsa zai mawa ba ke ba, don haka mu bai shafe mu ba, kece tamu don haka ba zamu bari ki wula anta ba duk rintsi don haka na soyo maki naman rago nayi maki dambun kaza ga kwalin kifi can da za a yi amfani da shi cikin alala gobe da kwai shi ne damuwarmu, kuma na siyo kayan abincin can ne da ku en da iyayenki (yaran Hajjo) suka bada a kawo maki, yanzu haka akwai Naira dubu ashirin a gurina wadda za ki kama sana'a bayan suna zamanki a haka ba zai yiyu ba, Jiddah ita rayuwar aure da kike gani ta gaji aci da bauri tare da zuma mai cike da za i, ina son ki ci-gaba da ha uri da rayuwa ki jure watarana sai labari, Jiddah ina ji a jikina za ki zama abar kwatance abar alfahari a cikin dangi da jama'a ko'ina sai anyi alfahari da ke Jiddah insha Allah." Tunda ta fara magana nake share hawayena ina jin inama maganarta ta tabbata? Amma ta ina hakan zai faru? Na kasa ma cika burina na samun zama cikin aminci da walwala ko da hakan na samu zan farin ciki, so nake naga rayuwar aurena tamkar yadda nake ganina a mafarki tare da wanda ban ta a ganin ko da fuskarsa ba, so nake naganmu muna tsokanar juna, muna kiran juna da sunayen soyayya irin su Prince da Princess ko King da Queen, amma yaushe zan samu hakan? Deeni sam bai iya rayuwar farin ciki ba, ko da yake ban sani ba ko nice bai son mu yi rayuwar farin cikin da shi tare ba, idan ba haka ba komai nakan yi shi kan a'idarsa yadda yake so, amma shi sam ko a jikinsa babu abin da yake birge Deeni irin yaga hawayena, yana son ganina ina kuka yana farin ciki ya ganni cikin damuwa ban san me yasa hakan ba sam... "Ke Jiddah ba naji ance kina da hawan jini ba? Amma kuma kike tunani irin wannan? Tun azun nake magana amma hankalinki sam bai gurina kin lula duniyar tunani? Don Allah ki kiyaye lafiyarki Jiddah ko don gaba ki ji da in yin sabuwar rayuwarki cikin aminci kin ji?" aga mata kai nayi, amma har ga Allah tunani nake yaushe ne ma zan daina tunani bayan kullum sai abin tunanin ya same ni? Don haka jin Hajjo kawai nake nasan ba in ciki ne ajalina kawai. RANAR SUNA *** Tunda asuba kowane magidanci wanda ya samu aruwa ke tashi ya yi wanka ya kimtsa ya saka sabbin kaya don zuwa gun ra in sunan ansa, amma ban da Deeni yana aki kwance yana she a barci cikin natsuwa da kwanciyar hankali, duk abin da za a auko a cikin akin sai dai na je na auko, tabbas ya takurama mutane da dama barcinsa amma wa ya isa yace ya tashi ya fice? Amsar ita ce, babu shi duk gidan nan. Ina jin wayarsa na ara ita ce ta tada shi daga barcin da yake, muna jin shi yana cewa ba zai samu zuwa ba amma a saka sunan yaron Aliyu. Ajiyar zuciya nayi tabbas haka sunan da Safiya ta gaya min yace mata zai sama yaron kenan, Allah Sarki! Wai Safiya ta fi ni muhimmanci a gun mijina Uban ana? Babu komai akwai Allah. Maza ne da dama suka dawo daga ra in suna dangin mahaifiyata sunata sama yaron albarka, nan da nan aka fitar masu da koko da osai tare da tuwon da aka bi dare aka yi daman don hakan. Sai da gida ya cika ya batse da mutane sannan Deeni ya tashi ya fito, ba kunya ba tsoron Allah ya auki buta ya shige kewaye (toilet) ya fito ya wanke jikinsa inda ya saba wankewa ya shige aki ya sauya kaya ya a min kira. Ina zuwa ya dubeni fuska murtuk yace, "Dame-dame akai ne na abincin sunan?" Cike da fara'a nace, "Akwai alala, shinkafa, tuwo, dambu." Ya ta e bakinsa yace, "Babu so o da dinja kenan?" Ina murmushin Yau abin da armashi nace, "Duk za a yi su, har da kunun aya ma za ai don an kai marka e ma yanzu haka." Ya jinjina kansa, "To saura kada ki samu manyan kuloli ki zuba min ni da abokaina ki aje zan aiko a amsa, kuma naga nama can a kuloli ki tabbatar kin zuba min mai yawa, kar ki manta ki zuba mai yawa a kaiwa awarki Safiya Yau na huta da bata ku in abinci." Jin Deeni ya halakar
Chapter 17 · 0% Book details