← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 133

Sashe 13

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
*____________________________________*
KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Page 11
Ina zaune ina sa
awa da kwancewa Deeni ya fito daga
aki, shi dama bai wanka sai dai idan ya gaji da kayan jikinsa ya dawo ya cire su ya saka wasu, duk da lokuta da dama zai ta tashin wari irin na mutum ya sha rana amma ko a jikinsa, ga sumar da yake bari cike da hammata na
ara taimakawa gun fitar wari a jikinsa, amma ruwansa shi, ko a jikinsa. Ni kuma ina bala'in son namiji mai tsabta wayayye, wanda ko da yaushe zamu kasance cikin farin ciki da walwala, muna wasa da tsokanar juna, amma ban da Deeni, kawai shi idan ba dole akwai maganar da zai mun ba, bai min magana sam. Idan ya shigo gidan duk da bai sallama nakan basar na amsa ma shi sallama nayi kamar naji ya yi sallamar. Duk da yadda yake gwasaleni hakan bai hana ni
arin dinga jan sa da wasa ba, amma sai ya buga tsaki ya fice bai nuna ya jini sai ta silar tsakinsa zan fahimci ya ji ni sarai lokacina ne bai da shi kawai.
Ina cikin tunanin zaman gidan aurena Deeni ya fito ya sauya kayan jikinsa, har ya wuce ya dawo ya sunkuya ya
auki abincin da aka aiko min da shi. Gudun kar ya cinye kuma ina bu
ata yasa nace a sanyaye "Don Allah ka rage min ban ci ba, kuma yunwa nake ji." Wani banzan kallo ya bini da shi ya ta
e bakinsa kamar zai aje robar abincin sai kuma ya
auka yace, "Mutum sai shegiyar rowar tsiya ta gadon gidansu. Ki ma gode wa Allah da har kike aje abu ina
auka, ba don ban da shi ba ne sai don na taimaka maki wani lokacin kuma naga yadda za ki yi kamar dai yanzu da zan
auke abincin, ba daga gidan rasuwa aka kawo min sadaka ba har gida? Ko gidan ke ka
ai ce mai iko da shi? Ina ga nan gaba cewa za ki dinga yi gidanma naki ne ko? Ban da munafukar rowa da son banzar tsiya ma irin taki ni da gidana ace ban cin abin da ke cikinsa? Ke kam anyi marowaciyar gaske Dilla." Ya
auke abincin ya koma gefe na ya zauna yana ci, sai kawai raina ya ban na je na saka hannu mu ci abincin tare muna
ar fira ba mamaki daga nan hakan ya
ore da nafi kowa murna da farin ciki gaskiya, ina matuwar son naga ina abubuwan birgewa da mijina amma ina shi ba ruwansa ko kallonsa nayi nai murmushi sai yace "Rainin ne ya motsa ko?" Idan kuwa yana zaune na je na zauna gab da shi sai ya ha
e rai ya tambaye ni "Lafiya ki zo kika tasani gaba kamar wani marar lafiya kin mun zuru da wa
annan idanun naki?" Ni kuma sai na kasa magana sai kawai na mi
e na bar gun amma har a zuciyata so nake mu yi rayuwa tamkar yadda musulunci yace, "Rabin jin da
in rayuwar duniya samun mace ta gari." To ni ya zan na zama ta garin ga Deeni? Ko da yaushe tambayar da nake ma kaina kenan. Yaushe Deeni zai dinga sakin fuska yana min dariya muna wasa da dariya? Yaushe ne zan ga Deeni na mun magana babu
unci a kan fuskarsa? Na rasa me yasa burina ya
i cika na zaman aurena, tun ina Lagos nake mafarkin gani gidan aurena da wani dogo mun rungume juna duk lokacin daya dawo daga waje, haka ina ganin muna abubuwa masu kyau na soyayya da saka farin ciki, sai dai ban ta
a ganin fuskarsa ba, ko da yaushe jikinsa kawai nake gani kansa na cikin jikina ko dai yana sunsunar wuyana ko kuma ya rumgume ni yadda ba zan ga fuskarsa ba. Babu ranar da ban mafarkin nan har aurena ina yi, kawai tsorata nayi don naji ance aljani na auren mace don haka nake
in barin mafarkin ya yi tasiri a zuciyata ko da safe idan na farka. Na yi tunanin idan nayi aure ba zan sake irin mafarkin ba amma sai naga ban daina ba, kullum sai nayi mafarkin ga shi wanda nake gani dogo ne amma ban ta
a ganin fuskarsa ko na gane fari ne ko ba
i ba, kawai ina mafarkin namiji ne ko muna rungume da juna ko yana min kiss ko kuma nayi lamo a jikinsa tamkar wata mage. Hakan yasa nake son tabbatar da mafarkina akan mijina amma ina shi ba haka ne a gabansa ba, gwarama da kafin na kama shi da
awata Safiya yana
an murmushi ya ta
e baki idan nayi mai shagwa
a ko ya shigo gida nace "oyoyo Lovely " To yanzu duk wannan ta kau tsakanina da shi muguwar harara da uban tsaki ne, sai kuwa idan yaga abu ya
auke duk da yasan ba shi ne ya kawo abin ba.
Kamar wasa Deeni ya zauna ya cinye abincin ya dube ni fuska ba walwala yace, "Tsabar iskanci ruwan shan ma Yau sai na ce aban?" Girgiza kaina nayi na mi
e da
yar, na fita don kawo mai ruwan, wanda nasan ya fini gaskiya ya kamata ace yana fara cin abincin na kawo mai ruwan kamar yadda na saba yi mai ko da yaushe. Ina jin shi yana cewa, "Yarinya ba zan
auki rainin hankali ba ni da ku
ina, dama kin natsu kafin na natsar da ke a banza. Ina ma amfanin auren yarinya
arama? Ni ban san makancewar data sa na kai kaina ba nace ina sonki ba ma, ko da yake wannan shegen farin ne ya ja ni ya kaini ya baro." Ni dai ban ce
ala ba ko a zuciyata domin dai nasan ban da gaskiya, taya miji na cin abinci ba ruwa a gabansa? Ba haka naga Mamata nayi ba, ko da yaushe tanadar komi take na mijinta, idan yana cin abincin ma tana gefensa suna labarin duniya, dana jama'ar gari. Lokacin dana kawo mai ruwan har ya cinye abincin tas yana latsa wayarsa, idona ya kaimun kan sunan Safiya dake cikin wayar alamar ita yake son kira. Gabana ya fa
i sosai har kaina ya amsa naji juwa na neman kadani na zubar da ruwan a jikinsa na shiga tara kuma ba uku ba, na samu na daidaita natsuwata na aje mai ruwan cikin muryar da ka
an ya rage na fashe da kuka nace "Ga ruwan na kawo." Har ya kanga wayar a kunne ya janye yace min, "Munafurci dodo ne, mai shi yakan ci." Ban ce komai ba na wuce na koma inda na tashi na zauna zuciyata na suya da tafasa, ji nake tamkar na ha
iye zuciya na mutu,tsabar yadda zuciyata ke luguden tara-tara. Kamar daga sama naji yana cewa, "Ya kina gidan ne ko kuwa? Ni fa da
ina dake kenan banzan tsoro wallahi miye naki a ciki aini zatai mawa idan ta isa ko? Sai kuma ya yi murmushi yace to ina zuwa yanzu mu yi bankwana ki
an jira ni ka
an." Kasa ri
e kaina nayi sai da na
ago na dube shi har ya mi
e tsaye nace, "Yanzu don Allah baka rabu da Safiya ba, har yanzu kuna tare? Baka gudun mijinta ya kamaku kamar yadda na kamaku?" Ya wani zaburo kamar zai kai min mari yace, "Dama jiranki nake, uban miye naki a ciki to? Kika kama mu satar me mu kai maki? Wallahi ki fita idona na rufe kafin na sauke maki kwandon mutunci. Ko gidanki ne nace? Nace gidan naki ne na kawo ta ciki da za ki min munafurcin banza? Idan gidan iyayenki na kaita ba sai ki sa a koro mu ba." Har ya fice waje yana masifa, ni dai kwanciya nai mina-mina ina kuka mai matu
ar ciwo, ji nake tamkar ba ni ba, ji nake ban da kowa a duniyar nafi kowa matsala haka nafi kowa damuwa.
Kamar wasa haka na wuni cikin gida ba wanda ya le
o ni har la'asar sannan Binta ma
wabciyata ta shigo tana min gaisuwar mijin Mamata. Na amsa mata har nayi mata godiya, ta dubeni sosai tace, "Jiddah bari na kawo maki kunun kanwa ki samu ki sha yanzu naji ina marmarinsa na dama shi, to nasanki da son shi, dama zuwa nayi naga ko kina nan na kawo maki." Allah Sarki! Da
i naji sosai amma don kar ta gano gazawata ko ta fahimci yunwa gareni sai nace cikin
an ya
e, "Lah ai da ma kin bar shi wallahi na gode Binta." Tana kallona kamar bata sanni ba ko ta jima bata ganni ba tace, "Amma Jiddah kin saka abin nan har yanzu a ranki ko? Kin ga yadda kika koma kuwa? Baki
aya kin fita hayyacinki da anganki ko baki fa
a ba ansan kina cikin damuwa. Don Allah ki manta da komai kinga ko asibiti ana yawan yi mana fa
a kan damuwa ance har hana haihuwa take yi." Murmushin ya
e nayi nace a sanyaye "Ban lafiya ne Binta don haka ko gidan gaisuwar ban je ba, ba abin da ke damuna ni." Cikin shakku tace, "Bari na mi
o maki kunun ki daure ki sha, amma ban daina gaya maki ki cire damuwar namiji a ranki don anyi babu ke wallahi indai
a namiji ne duk yadda kike kau da kai kike ha
uri da shi idan ba ki dace ba, sai ranki ya dinga
aci a banza." Ta fice na bita da kallo kawai raina na gasgata maganarta, amma kuma me yasa Deeni zai mun hakan? Bayan yasan ba sonsa nake ba lokacin da akai aurenmu ban san shi ba, nayi biyayya ne kawai na aure shi saboda ban da gatan da zan ja da aurensa. Haka kuma ban san kowa ba a zuciyata amma dai nasan wanda nake so nayi rayuwar aure da shi a cikin raina shi ne irin wanda nake gani a cikin idanuna da mafarkina idan nayi barci, shi ne wanda nake hango muna rayuwar aminci mai cike da walwala da mutunta juna. Amma ban san me yasa zuciya ke son irin rayuwar ba duk da bata dace da irin shi ba a zamantakewar aure. Ina nan Binta ta kawo kunun yana ta
amshi, taban ta fice tana
ara ban shawarar na yakice damuwa na samu zaman lafiya inba haka ba ni zan jawa kaina ciwo babu mai jinyata da
awainiya da Ni sai dolena, nace a raina tana nufin Mamana kenan.
Tabbas kunun ya yi mun da
i sosai na shanye duka duk da yana da yawa, na tashi haka nan ta kama sharar gidan duk da mugun ciwon kan dake addabar rayuwata, ina son na manta da komai ne don haka nake tsirar aikin da zai sa ma manta yadda nake cikin damuwa, sai dai sharar nake amma hawaye sai zuba suke a idanuna, a bayyane nake furta, "Yaushe ne zan ji da
in rayuwata? Yaushe ne zan cika burina? Tabbas ina son na koma karatu ko dan na samu sau
in ba
in cikin cikin gidana, amma Deeni zai barni na koma karatuna? Ina son naga Mamana a farin ciki yaushe ne zan saka ta cikinsa? Ina son rayuwar gidana ta daidaita yaushe ne zan daidaita ta?"
Ina cikin sharar naji sallamar wadda har in mutu ba zan manta sharri da alkhairinta gare Ni ba, wadda ta za
i zamana a cikin ba
in ciki madadin farin cikin da Ni na za
ar mata zama.
Shin kun san Wacece wannan?
Ku biyo Haupha dan jin wacece wannan matar tai ma Jiddah sallama a wannan lokacin da take tsaka da neman makullin zaman lafiyar rayuwarta.
Taku a kullum Haupha
[7/18, 7:23 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA
IN ALLAH*
Labari da rubutawa
Chapter 13 · 0% Book details