← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 133

Sashe 29

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da mata su kai masa a zuciya idan zai masu waccan yarinyar tabbas zai murna ba mamaki babban burinsa ya cika sanadin ta. Haka Mustapha yai ta sa awa da kwancewa kan Jiddah wadda ita sam bata ma san yana yi ba duk da cewar a zamanin zamanta gun Hajjo ta san shi amma ba irin sanin nan ba na sosai da sosai ba, amma tabbas idan ta ganshi zata shaida shi ganin farko ma kuwa. Uncle Salim ya dubi abokinsa da fuskar tausayi yace, "Bai kamata ba ace ko da yaushe kana aje abu cikin ranka ba, saboda bai da wani amfani ka sani Allah shi ka ai ne zai iya magance maka damuwarka, wallahi watarana sai kaga kamar ba a yi ba." Mustapha ya dubi abokinsa ya ja numfashi kawai bai ce komai ba, domin ya manta da wata damuwa da yake cikinta ma sam ganin waccan yarinyar da tunanin abin da ya fa o mai. Da haka suka tashi suka wuce kowa na tunani a ransa, shi Mustapha yana jin tamkar ya tambayi Salim me ya kawo Jiddah amma yana jin kunya sosai. Shi kuma Salim yana tunanin wace irin sana'a ce ta dace da Jiddah matsayinta Na mace kuma yarinya arama? Jiddah kuwa tana shiga gun Zainab suka baje suna ta fira har akai sallah bata koma gidan Hajjo ba, sai ga Hajjo da Afnah ta kawo tana kuka, aikuwa sai fa a take masu su duka sun banzatar da yara suna ta firar banza da wofi. Zainab ce tana dariya tace, "Kin ga Hajjo gidan su Maryam fa ta iske ni ko can ma mun jima kana muka dawo nan kin ga ai bata jima nan gidan ba sosai kenan?" Ita dai Hajjo tai banza da ita ta wuce tana cewa bari na kawo gudar ita tafi ha uri don barci take ma. Zainab ta amshi Afnah tana ta murna, "Oh ikon Allah! Yanzu Jiddah ke ce da yara har uku?" Ni da ita muka kwashe da dariya, Hajjo ta shigo ta kawo Afnan Haidar na bin ta a baya, amma sai ya i tsayawa ya bita suka koma tare. Sai da mijin Zainab ya dawo sannan na koma gidan Hajjo. Akan hanyar ne naga Mustapha na an tsaya in gaida shi naga kamar bai gane Ni ba, don haka na wuce abuna na fa a gida. Sai da na kwana uku sannan muka shiga kasuwa da Hajjo ta kaini gun an takalma da gun an atamfofi da shadda har da leshi , da ita su kai cinikin komai aka gama aka rubuta komai a takarda da farashinsa, mu ka dawo gida. A gida ne aka fitar mun da ku in kowane kaya yadda zan sai da shi, na shiga gidan Zainab don yi mata bankwana tun da gobe da wuri zan tafi gida. Yana zaune yana jin cewa duk duniya shi ne kawai ke da irin wannan addarar ko kuwa shi ne bai dace ba? Me yasa ya kasa dacewa ne shi? Me yasa duk yadda ya so ya rayu cikin farin ciki hakan ke faskaruwa? Ina ma ace bai yi aure ba? Kawai ya ganta ta shige makwabtanshi fuskarta auke da murmushi kamar ko da yaushe, tsab da ita ga alama bata da wata damuwa don duk lokacin da zai ganta a cikin farin ciki take. "Allah ka kai damo ga harawa." Ita ce kalmar da zuciyarsa ta ayyana mai bai san ya akai ba kawai ya ji ya saki murmushi mai tafe da sauti ba. Bata jima ta fito yana ganin matar gidan ta rako ta ga alama bankwana suke. Sai ya ji take tamkar ya yi mata magana su gaisa amma daya tuna da tana da aure sai ya fasa kawai ya juyar da kansa gefe kamar bai ganta ba. Har ta zo ta wuce ta gabansa yana kallonta ita kam ko inda yake bata kalla ba, ta shige gidansu Salim. Ajiyar zuciya ya saki kawai ya ji sabuwar damuwa ta dabaibaye shi baki aya. Washegari da sassafe Uncle Salim ya kaini tasha ya biya min ku in mota da ku in kayana ya ara min da wasu ku in, sai da ya ga tashin motarmu sannan ya bar gun. Kasancewar na fito da wuri sai na iso da wuri, nan da nan na bugama wa anda na gayama wa zan je sarin kaya, kafin kace me ? Gidana ya cika da mutane masu duba kaya, kowa ya za a ina rubuta sunan mutum da abin da ya siya da ku in sai arshen wata ya ban ku ina. Cikin ikon Allah kayan basu jima ba na saida su, duk da cewar na fahimci babu wasu kayan tunda a rubuce aka ban sai ban damu ba, na auka mutanen dake zuwa siya ne ake samun marassa tsoron Allah na auka, ashe ba haka bane ba, duk lokacin dana fita zuwa gidan biki ko suna ashe sai Deeni ya kawo mace gidan idan sun gama abin da za su yi sai ya bata takalmi ko atamfa ko leshi, abokansa kuwa yai masu tallar shadda suka ce ya kai, ya ibi guda hu u ya kai ban da labari. Ranar wata Alhamis ina zaune ina ta arin lallashin Afnah tana ta kuka wata yarinya auye mai tallar fura ta shigo gidan. Na kalle ta naga ban santa ba kuma ban kira ta ba don haka nace mata lafiya? Shi ne ta ce min, "Don Allah maigidan na nan?" Nace mata "Bai nan amma lafiya kike nemansa?" Sai ta sauke waryar furar ta fiddo leda ba a ta ban, tana cewa, "Daman wannan takalman zai sauya min sun yi min yawa in ji Innata." Na amshi takalma da fuskar mamaki ina kwance leda naga takalman saidawa ta an dubu biyu da ari biyar, na dube ta nace, "Ke ya akai wa annan suka zo hannunka?" Kanta tsaye tace min, "Rannan ne mu ka zo Ni da budurwarsa Hinde suka ce na jira su suka shige aki to bayan sun fito ne na ganta da takalmi da atamfa shi ne nace ina so ya ce na bada Naira dubu na za a na shi ne, to na ba shi dubun kuma naje gida na gwada ance bai min daidai ba na zo ya sauya min wasu ko da irin na Hinde ne." Yanzu na gano bakin zaren, kenan dai da hajata Deeni ke bin matansa da ku e na yake sallamar karuwansa? Na auki takalmi na kai aki na aje na fito nace mata, "Ki tafi cikin gari ki neme shi ya baki wasu takalman amma ki gaya mai matarsa ta wace wa annan ruwansa ne ya baki wasu ko ya biya ki ku inki. Sai taimako na gaba da za ki min, na mi a mata naira ari biyu nace, "Gobe idan kun fito talla da waccan yarinyar ki zo mun nan gidan da ita don Allah kin ji?" Idan kika kawo ta ki dawo washegari zan cika maki ari uku kin ga ari biyar ta tashi kenan. Da murnarta kuwa ta fice nayi mata kwatancen inda zata iske Deeni na samu waje na zauna sai kuma na tashi na auko list in kayan da na zo da su dana wanda na saida na fara lissafawa ina arin gano abubuwan da babu a ciki. Ba aramin mamaki nayi ba lokacin da na fahimci Deeni ya kwasar min kaya masu yawan gaske, nan da nan kaina ya fara juyawa na rasa me ke mun da i sai kawai na goya Afnah na sa a Afnan na nufi gidansu Maman Khairat daman Haidar na can. Allah ka ai ya kaini gidan lafiya na zube ban sake sanin inda kaina yake ba, sai bayan dogon lokaci na dawo hayyacina. Mamar Khairat ta tambayeni abin da akai min da zafi haka na kwashe na gaya mata. Jinjina kanta kawai tai ta kasa cewa komai. Sai dare sannan na koma gidan nasan ko kwana zan ba zai damu ba haka idan na koma ba zai ce ina naje ba, yanzu rayuwa muke gidan tamkar kowa zaman kansa yake sai mu yi sati bai tanka min ba sam. Ni ma yanzu na ware sosai da nuna halin ko'in kula da rashin maganar don haka ban damuwa sam. Har ya dawo gidan ya kwanta, kamar na je akin nashi mu yi ta cikin daren sai kuma nace bari sai gobe idan yarinyar ta zo sannan sai ayi ta baki aya idan ya so gidan ya one baki aya. Washegari kuwa har wajen arfe aya na rana ba yarinya ba labarinta balle naga awarta da aka ba kayana, har na fitar da rai sai naji ance " Za ku sai fura?" Har ina taune harshe gun cewa " E za a siya kawo." Sai kuwa ga yarinyar jiya da wata tare da ita, da fuska ta nuna min ita ce yarinyar, aikuwa na ce su sauke na dubi ofar akina naga kwa on na nan ma dubi yarinyar nace " Don Allah shiga daga can cikin akin ki auko min wurin da zan zuba furar." Ta kuwa shige na kuwa bi ta da sauri na ja akina na datse na auki cikon ku in yarinyar jiya na bata, nace maza ki je gidansu ki ce matar wanda ya bata kaya da suka gama iskanci rannan ta rufe ta a aki tace sai an biya ta ku in kayanta zata bu e ta." Har ta tafi nace ki fara biyawa gun abokin iskancin nata ki gaya mai na datse karuwarsa a aki nace sai an biyani ku in kayana." Na koma na samu waje na zauna sai kuma naga gwara na kai yarana ajiya kada ma su hanani rawar gaban hantsi idan Deeni ko iyayen yarinyar sun zo. Na kuwa mi awa Binta su nace ta ri e min su zan shiga wanka amma sai na fara gama wanke kayansu. Ban jima da dawowa ba sai ga Deeni, zuwa lokacin yarinyar sai uban ihun kuka take cikin aki nikam ala bance mata ba, domin ban tsara zance matan ba sai gaban iyayenta ko wanda ya bata kayan nawa. "Ke lafiya za ki rufe masu yarinya a aki?" Na dube shi naji kamar na kife shi da mari nace, "Lafiyar ce ta saka haka,
Chapter 29 · 0% Book details