← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 138

Sashe 99

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali matarsa ta tsakiya ta budi bakinta ta ce" Haba hajia, me yasa kika cika zafafa abu ne wai a rayuwa?, Yanzun wannan ai bai dace ace kece kika yi wannan abin ba kamar wata yarinya karama?, Me ya tauye mu a gidan nan? Ko mu mun ce zamu kawo bakin ne ya mana iyaka da dukan wajen da muka so ajiye su?, Ko ya taba hanna mana abinda zamu dafawa bakinmu ne? Haba hajia kece baba a gidan nan aman kuma kece mai yon wasu abubuwan da basu da dadi, kar ki manta ke ya dace ki koya mana kyawawan dabi'u fa"

Sai da ta bari ta kai karshe ta debeta da ido ta watsawa kasa ta ja uban tsaki tana fadin" Kin san ai ni ba munafuka bace da zan tsaya yin kumbiya kumbiya a kan abinda yake cikin zuciya na ringa munafuntar kaina da kaina sannan na munafurci mutanen dake tare da ni, sai ki rantse da wanda ya busa maki numfashi cewar abin nan baya ci maki tuwo a kwarya, bafa wani abin boye boye bane, abu ne na gaskiya wanda yake abin a duba, ba maganar bakin ciki sai magamar gaskiya, dan haka na kawo kukana idan zaman adalci ake yi a gidan nan a duba min"

CHIEF OF ARMY haka jikinsa ke rawa yana tsaye yana kallonta

Maman Muhay ta girgiza kanta dake kasa a sanyaye ta ce" Allah ya baki hakuri, sai da ya so ya kaisu wani wajen mune muka hanna, bamu san hakan zai hadasa wata matsala ba, aman in sha Allah idan har yayan ya amince sai su koma wani wajen, hakan ba zata kuma faruwa ba"

MUHYIDEEN ya yi dan murmushi mi ciwo yana sada kansa da hayaniyar da ake yi a hankali ya furta" Allah ya sanyaya "
Sannan ya mike ya fice a falon, domin wannan dai ba huruminsa bane, koma menene zasu daidaita kansu ne tsakaninsu

Yana fita CHIEF OF ARMY ya juya ya nufi dakin barcinsa yana fadin" Idan kun fita ku rufe min kofar "

Da wani bakin cikin ta raka shi da kallo hakama sauran
Sosai damuwar yannayinsa ya kama Mama, aman kuma na zata taba yin gigin zuwa a yanzu ba domin wata fitinar take ita hadasawa kanta, dan haka ta mike ta nufi bangarenta tana tunanin sanadiyarta ne ake son saka masa hawan jini ko me? In sha Allah ba zata basu damar su wulakantashi ba, in dai a kan bakin yaronta ne zata je da kanta ta gyara masu wani wajen ta kawata masu yadda zasu ji dadin zaman

MUHYIDEEN na dawowa wucewa ya yi ciki ya rufo kofarsa ya zauna bakin bed hadi da dafe gaban goshinsa

Sai kuma ya tashi yana watsar da tunanin ya dauro alwallah ya dawo ya shiga gabatar da shafa'i da wuturi dan gaba dayama ya manta da Shuwwa da barci ya kwasheta a saman doguwar kujera lulube da bargonsa, yana gamawa ya yi kwonciyarsa ya shiga neman barci

_____________________________________

Da sasafe tun kusan karfe shida Dad ya bar gidan, cikin shirinsu na kaki yau ba tare da ya nemi kowa ba sai sojojinsa masu bashi tsaro

Cen kusan karfe tara kira ya samu MUHYIDEEN daga baban ofishinsu daga shugaban kasa cewar yanzu yanzu ana nemansa, hakan ya sa da gagawa ya diro ya shiga shiryawa a gagauce ya saka kaki dinsa ya fice da mugun sauri yana dan daga mata hannu a lokacin da take fadin" Yalabai ina kwana" ya wuce ya tafi Wajen da ake kiransa

Kusan karfe goma sha daya zuwa sha biyu jiniya ta ringa yi a cikin gidan wanda ko barci kake yi dole ka farka ka fito ka ga abinda yake faruwa a gidan
Kusan kowa yau sai da ya fito a tankamemen balbalin gifan na CHIEF OF ARMY, harda y'ayansa da matayensa da ma'aikatansa baki daya kowa ya fito harda su Malan, wa'inda basu fito ba kawai mahaifin SHUWWA ne da mamanta, summa aban nata ne ya hanna su fitar dan ita ta so ta fito din ya nuna aa gidan sojoji fa suke ko ba komai ai ba za'a rasa jiniya ba

Wuleliyar motar dake parrke ba'a bude ba zagaye da sojoji kowa ya fi kallo, har CHIEF OF ARMY ya fito a motar da yake yana murmushi ya shiga fadawa kowa wanda yake ahalinsa, iyalinsa da bakinsa cewar su karasa baban falonsa da aka bude aka basu damar shiga

Kowa na kallon dan uwansa ne, aman kuma ba damar yin musu ko tambayhar ba'asi, sshigar dai kowa ya yi dan sun fuskanci koma meye abu ne da ya shafe su

Bangaren da iyayenta suke ya je da kansa ya yi salama ya nemi alfarmar su karasa falonsa
Suma din sun karasa din ba tare da musu ba sun kuma zauna a saman kujerun da aka nuna masu kowa ya yi tsuru yana saurare

A hankali Shuwwa ta dunguri Nahidt kasa kasa ta ce" Ke wai me aka yi ne?"

Nahidt ta daga kafadunta itama kasa kasa ta ce" Ko dai am daura min auren ne da Malan za'a mana nasiha? Ko kuma auren ne za'a daura? Baki ga yau Aban naki sai kyalin amarci yake yi ba?"

SHUWWA ta girgiza kai tana janye hijab dinta baki wanda ya kai mata har kasa mai hannaye da zif ta ce" Allah dai ya sa ba wani abu ya samu katona ba gaskiya, dan na fara tsorata ban ganshi ba a hargagin nan, matsalar auren soja kennan , su ko makotaka kake da su zakana gannin fitintinu ne kala daban daban, ni gaba dayama na rikice"

Fausy kasa kasa ta ce" Kin fola ne?"
Shuwa ta girgiza kai ta ce" Ba maganar folawa, munma saka ranar rabuwa, kawai dai katon akoy shiga rai ne, inaga sai abana ya tofe ni da adu'ar dangana"

Dan murmushi ta yi zata bata amsa katuwar muryar wani sojan yake sanar masu *CHIEF OF ARMY* zai shigo

Basu wani damu ba dan sun san ai Dad ne zai shigo kuma an saba yi masu wannan shelar, kowane dai na dan sha'aninsa, aman kuma hankalinsu na kan kofar shigowar

A hankali ya bude kofar ya shigo da salamarsa da kuma muryar nan tasa mai rikita kwonya
Gaba daya idannuwa ne suka sauka a saman kansa
Lokaci daya dukan wani wanda ya gane kalar kakin dake jikinsa da galolin dake kafadarsa da gaban kirjinsa ya mike tsaye yana mai zuba masa ido, har Dad ya bayana a bayansa cike da murmushin farin ciki kafin ya bayana a gabansa da wata chemise blu mai dauke da takardu a hannunsa
Mutanen falon ya sake waigowa yana kallo a lokacin da Shuwwama ta mike tana fadin" Bari dai mu tashi muma kar aje wani abun ne za'a yi" domin ita dai bata san meye ake nufi da hakan ba, aman kuma yannayin MUHYIDEEN ya saka ta kure shi da ido har ya sauke dubansa a kan mahaifiyarsa wace jikinta ke rawa tana kallonsa cike da tsoro da kuma wani irun abu dake ratsa ilahirin jikinta tana son gane me hakan yake nufi, sai dai kallon da ya mata yana mai risinar da idannuwansa ya saka langwabar da kanta da wata murya a sanyaye ta furta" Masha Allah......."

Chief of army ya yi murmushi shima a sanyaye ya furta" Yau dai Allah ya taimake ni na samu ya amshi kujerarsa, Allah ya taimakeni na hada shi da manya sun rarasar min shi ya amshi kujerarsa, domin ni na gaji, shekaruna sun ja, kaina ya dade da dena gane hayaniyar gidan soja, hutu nake da bukata da kulawar iyalina, yau gashi Allah ya nuna min, sai dayar rigimar da nake kwana nake tashi da ita, wace zan roki alfarmarka sannan na kama kafa da iyayenka, da Abanka gayanan zaune, su sake saka baki na miko maka takardun arzikinka baki daya ka rike, ka koyi juyawa domin bana so na mutu da su a hannuna su zamto jayaya ko wani gardama, duda akoy sunnanka a sama aman dan adam a kan arziki babu abinda ba zai iya aikatawa ba, My Son ka yarda ka amshi tarin dukiyar nan ko zan ji nauyin nan ya sauka a kaina"

Idannuwansa ya rintse da karfi yana jin yadda aka kwashi murna masu yin ihun murna na yi masu barka a bayane na yi, haka kuma wa'inda bakinsu ya mutu murus na kallo tamkar wa'inda suka summa a tsaye

Mama ce ta sake kallon mijinta a raunane ta langwabar da kanta ta ce" Aya Abansu, fushi ka yi da mu ne?"

Matarsa ta tsakiyama ta fuskance shi tana fadin" Abansu aikin ka ajiye ne?"
Chapter 99 · 0% Book details