← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 138

Sashe 43

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana wannan fadan a zuciyarsa ya zagayeta ya sauka ya fice da dan sauri dan an fara tada sallah , abinda baya wasa da shi da shi kennan a cikin rayuwarsa, idan me yake yi aka yi kiran sallah zai je ya salaci Salah ne tare da jama'a a masalaci, idanna jeji suke zai bi tawagar al'uma su yi Salah ne, ya kasance daya daga cikin masu yowa sojoji tuni a kan mahinmancin sallah, Manzon Allah sallalahu alaihi wa salam yana cewa" Walahi, a duk lokacin da akai kiran sallah, nakan ji tamkar na rura wuta mai girman gaske na zauna dan na gane wanda bai shigo masalaci yin sallah ba tare da wani kakarfan rashin lafiyar da ta hanna masa tashi ba, na saka a kamo shi na saka shi a cikin wutar nan har sai ta kone da shi kurmusssss!, Yakan ce da mutun ya sani, da zama ya yi sallah a cikin gidansa bayan an yi kiran sallah gwara ya yiwa kansa fatan gidansa ya kama da wuta da shi a cikin gidan su kone kurmusss da azabar da yake dorawa kansa.....Wa'iyazubilah!, Wannan dalilin ya sa a duniya bai ga wata shagalta da zata shagaltar da shi kin halartar sallah a cikin masalaci ko a jam'i ba, shedan ne? To ya ce A'UZUBILAHI MINNA SHAIDANNIN RAJIM!,

A lokacin da ya bar falon a bayane ta dan girgiza kai a fili ta ce" Mema Nahidt ke son tirani aikatawa? Ashe Nahidt bata sona? Ko dai bata ganshi a fili bane da kyau? Allah yai min tsari da kai, gabjejen kato kawai?, HM bara na yi sallahta na gama na fara karantar ta inda zaka bani takardata! Ina ni ina zama da kai? Ni da bake son na yi aure na hayayafa? Kai kuma ai ba abokin yina bane wollah!"

🤔🤔🤔🤔🤔🤔 Kuma ke?💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 2️⃣2️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A wannan rana da SHUWWAR take amarya a cikin gidan MUHYIDEEN ya kasance mata rana ce kamar sauran ranakunta da take shigewa dakinta ta yi barcinta a cikin gidansu da ita da yayunta, domin tunda ta koma cikin dakin da aka sauketa cewar nata ne bata kuma fitowa ba, haka kuma babu bakon da ya zo gareta da sunnan ya leko amarya, uwa uba angon da ta gama gane lamarinsa nada bukatar gyara,
Aa bangarensama yana dawowa saman table ya je ya dauki tea dinsa da mai aikinsa ke ajiye masa kowani dare da dan pizza ya haye sama da su ya bude dakinsa ya shige ya rufe ya ci gaba da abubuwan da suka zamto masa jiki kafin ya maida hankali ya ci pizzar nan ya sha lipton dinsa sannan ya haye saman bed dinsa da litafinsa na turanci ya bude ya shiga karatu a nutse ba tare da ya tuna cewar an kawo masa wata halita mai zamansa wace take amsa sunnan amarya wace take da bukatar kulawarsa irin na kowace amarya
Daga nan barci ne ya yi awon gaba da shi cen dare sosai har sai da kiraye kirayen sallar asubahi suka tashe shi

A gagauce ya shirya ya yi masalaci, ya samu sallarsa ya dawo ya haye sama a lokacin dukan ma'aikatansa sun fito sun kuma bazu sunna ta aiki ka'in da na'in kowa da irin aikin da yake yi kama daga guare gyare da goge goge, da girkin abin kari, da dai sauransu, sannan a cikinsu babu mace ko daya baki dayansu maza ne kuma suma masu kaki ne kananunsu sosai sune suka samu wannan mukami na kula da bangaren LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY

Kamar yadda ya saba shiryawa dan ya fita da wuri bakin aikinsa hakan ce ta faru da shi a yauma

A nutse ya shirya cikin kakinsa masu ruwan haske domin yau bai saka masu duhun nan sosai ba yana yi yana tunanin yadda zai kare da mutanen da sukai masa a gamo a gamo sukai masa auren dole, sai kadai sai ya saki dan murmushi yana juya kansa a hankali sannan ya dantse lebensa wanda ke nuna alamun abinda ke cikin zuciyarsa sam bai tanadar masu abun alkhairi ba, Allah ne kawai zai raba su da junna

Wayarsa ya dauko yana daura agogo a hannunsa na hagu da hularsa yana kallon saman screen din gannin mahaifiyarsa ke kiransa da sasafe haka bayan shi yake fara kiranta da safe wajen karfe tara haka ya gaisheta sai kuma da dare yakan kireta su dan taba hirar kurumci kafin su yi salama kowa ya kwonta

Turaran da yake yiwa jikinsa wanka ya dane kansa bayan ya bale mabalin ya shiga bin sasan jikinsa da shi yana kallon wayar domin ba zai daga ba so yake ta katse sai ya bi kiran

Abin mamaki tana katsewa wani kiran ya sake shigowa hakan ya saka shi dauko macajin da yake gyaran sajen fuskarsa ya juya wajen madubin dakin yana cazar gashin sajen da ya masa lufluf a fuskarsa ya gama ya ajiye sannan ya dauka ya katse kiran da kansa ya maida mata wani

Tana dagawa a dan gagauce ta ce" Barka da safiya MUHAY, yaya ka tashi? Ina amarya? Yaya aka yi baka kireni jiya ka bani ita mun gaisa ba? Sannan me yasa baka yiwa matarka ta nan bayanin ka karra aure ba sannan ka yi mata rarashi irrin wanda ake yiwa kowace mace mai daraja Idan an mata kishiya? Hakama dazun mamanka ke ce min ita rabonta da kai a kadan an yi shekara biyu ko a waya ta kireka bakaa dagawa, wai MUHAY ba zaka iya fitowa a mutun ka fadn me yar uwata da ta fi kusanci da ni fiye da kowata halita a duniya, abokiyar tagwaitaka ta yi maka da raini mai tsanani ya shiga tsakaninku haka? Itama ta yi mamakin aurenka ta kuma ce a ce maka ka kawo mata matar itama ta gaisheta tunda uwa take a wajenka, kana jina kuwa???????" Ta fada tama dan sauke numfashi domin tunda ta farra maganar ko sau daya bata ajiye maganar ba sai da ta kai karshen nan kuma take tambayarsa idan har yana jinta kuwa?

Ajiyar zuciya ya sauke kadan ya ce" Um "

Wayar ta kalla ta sake maidawa a kunnenta tana kallon matarsa dake zaune kanta a kasa ta ci kuka har ta gode Allah fuskarta ta yi mata jajajir idannuwanta du sun jeme kuka ne take na jin wai MUHAY ne ya karra aure bayan ko ita da take matarsa uwar gida bata saj menene auren da shi ba yanzun har a ce ya sake wani auren?

Idannuwanta ta kankance zata yi magana YARINYAR wajen CHIEF OF ARMY ta shiga da gudunta ta zube a gabanta jikinta na rawa hakama idannuwanta na cicikowa da kwallah ta ce" Mama, wai da gaske yayanmu ya yi wani auren a garin da ya tafi aiki? Mama sai ya cike matansa ba tare da ya aureni ba? Mama sonsa nake yi tsakanina da Allah me yasa gani a cikin gida sai dai ya ringa auren wasuna? Da me suka fini ne? Mama ya auri wata mace a garin da kowa ya san sun yi fitt a bin malamai? Ka bari danka ko mijinka ya dauki mace a garin sai dai ka yi hakuri da shi ka barawa duniya shi shine Papa ya yiwa yayanmu aure a cen? Mama ai mu da mu kuma ganninsa sai dai idan Allah ya yi, aman walahi mun shiga uku wayo Allahna"

Matarsa dake kallonta da mamaki ta ce" Ke dama ki ce mijina kike so a nan ? Mijina?"

Idannuwansa ya karra rintsewa a hankali ya ce" Mamanah?, Zan yi kiranki idan na isa office please hayaniyar ta min karfi da yawa"

Mama kanta da ta yi mutuwar zaune tana kallon yan matan da suka mike kowace ke fadawa yar uwarta ba siga tamkar zasu tashi sama sai ta samu kanta da gyada kai ba tare da ta iya amsa shi ba ta katse da sauri tana mikewa tsaye

A hankali ya soke wayar a cikin baban aljihun wandonsa na kusan gwuiwarsa ya rufe ya karasa ya ja abin kusan bed dinsa ya dauko bindigarsa yar karama yana ta hade naman gaban goshinsa domin har ga Allah ihun da sukai masa ya saka masa ciwon goshi,
Matsanancin mamakin yaran yake ji a ransa, ya kuma yiwa kansa tanadin shiga garin ko dan ya hada kawunansu ya gwara ta yadda zai hadasa masu kumburin gabam goshi mai tarra ruwan nan da baya warkewa kwana kusa, ta haka zasu dan bambamce shi ba sa'an yinsu bane, itama da ya auran ne take tunanin ta isa wajen da zata saka a kireshi a masa fada kau? Shi kam da ta ga makoncinsa da yaya zai yi da yarinyar nan da raininta? Wai dan ya yi aure ya kireta ya bata hakuri! Hmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmm

Sai da ya gama dubawa ya dura bulet ya dage wajen dannawar ta yadda ba zata harba da kanta ba sannan ya soketa a bayan wandonsa ya ja rigarsa ya rufe
Chapter 43 · 0% Book details