← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 138

Sashe 68

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nahidt ta yi dan murmushi ta ce" Ai yalabai wannan dalilin ya sa zaka ga wani lokacin sai a hankali, ai marayu ne mu bamu da uwa bale uba , lamarin sai gyaran Allah, daidaiku suka san hakin maraya, daidaiku suka san Allah baya so a taba maraya, daidaiku suka san shafa kanmuma alkhairi ne, yanzu haka dai kwanaki aka ce ko da danginmu a nan wajen? Shi kuma wanda ya zo din nan yayanmu ne shi dinma shine nake fadawa Shuwwa kulun cewar du inda zamu je in sha Allah ba za'a kashemu ba a duniya Allah zai saka tausayinmu a zukatan jama'a wannan ai lamari ne na ubangiji ko Yalabai?"

Kai SHUWWA ta girgiza tana dane dariyar Nahidt a ranta tana ayana' Da ace sunna da tausayi sojoji ai da ba zasunna kashe mutane ba, in zaki tashi ki tashi Allah ya sa mutuwa hutu ce a garemu kawai!'

A hankali ya maida dubansa saman kanta , sannan ya sauke idannuwansa a saman akwatunnan da take janye da su maka maka biyu masu kala daban daban, irin gata mai kala kala din nan

Bakinsa ya tabe yana gannin yadda wandon dake ciki shima fari kal ke bayanar da kansa hakan ya sa ake gannin girman cinyoyinta ta cikin abayar dake jikinta sannan ya dan juya cikin dabara yana satar kallon camerar dake boye wajen jerin fitilun dake lake ya sake juyowa yana kallonta da karra bin yafawar mayafin abayar da ta yi da kallo ya kuma samu kansa da ayana magana kamar haka ' Shi kuma turaran ko na meye? '

Bakinsa ya tabe ya mike tsaye yana duban agogon hannunsa hakan ya sa su dukansu suka kalli hannun nasa suma

Nahidt ta yi wani murmushin tana fadin" Ga dukan alama dare ya yi Yalabai tafiyar ko sai Ido na gani?"

Dan sake kallonta ya yi ya girgiza kansa ya yi wajen kicin da karkashe dukan abinda ya dace a ransa yana ayana' Ita bata gajiya da surutu ne? '

Da ido suka raka shi, kasa kasa Nahidt ta ce" Shuwwar koda kashe mun ya yi da daren nan babu mai sani, Allah mun gode maka haka rayuwa zata yi da mu ashe"

SHUWWAR ta zauna itama tana rafka tagumi tana kallonta
Wayarta ta bude ta shiga dora numbobin Aban Shuwwa ta zauna a gefenta tana sauraro

Wayar na fara ringin ya daga kiran da doguwar salamarsa

Da hausa ta ce" Kaima ya tabata a gareka amincin Allah, Aban Shuwwa kana ji?"

Malan ya gyada kansa yana sauraronta
A sanyaye ta koma yaren larabci sak ta ce" Ina sonka, (ana ahbuk ya habiby), inta amri ya hayati, inta amry ya nurry.........."

Fitowar MUHAY ya yi dan turus yana kallonsu da larabcin da take shekawa,
Da dan gagawa ta ce" Kai dai ka ringa gwada kirana lokaci zuwa lokaci idan Allah ya sa na kai gobe na yarda a daura auren nan, Aban SHUWWAR ina sonka sosai ka ji?".....................kit ta kashe tana kallon SHUWWAR da kikifta ido

SHUWWA ta yi yar dariya tana mikewa ta kara rungumar akwatunnanta da niyar bin bayansa

Juyowa ya yi yana kallonta a hankali ya ce" Barsu ".......................

Yana gama fada ya fice a dakin gaba daya
Sake juyowaa ta yi a haukace ta ce" In barsu?"

Nahidt ta daki kafadarta tana fadin" Ke banza yana nufin mu barsu yarensa su dauko mana, ko ba komai Shuwwar mun fa ga dadin rayuwa ko yau muka koma ba laifi Allah dai ya amshi tubanmu"

Ita kam SHUWWA gaba daya jikinta karra mutuwa yake yi, hakan ya sa itama ta barsu a nan aman ta dauki jakarta yar hannu ta fice
Itama Nahidt din binta take a baya har suka shige motar da aka nuna masu

Daga nan basu zame ko'ina ba sai filin jirgin sojoji inda jirgin CHIEF of army yake

Sunnaa zuwa an gama shiri dama su kadai ake jira hakan ya sa suka bi bayansa yana hawa sunna biye da shi har suka shige sannan aka rufe Jirgin ya dan tafiya kadan ya daga domin ba mai yin doguwar tafiya kafin ya daga bane

Ajiyar zuciya take saukewa tana kallon waje daya, zuciyarta cike take da tunanin abinda ta gani a lokacin da zasu fito daga balbalin gidansa
Saurayin nan yana cikin masu yi masu aiki a da, a yanzu me ya kawo shi?
Sharewa ta yi domin dai a gidan sojoji ne, yana da damar zuwa irin na kowa a duk lokacin da ya yi ra'ayin hakan, bale tafia ogansu zai yi ai dan ya zo cikin masu masa Allah ya tsare ba damuwa bane

Kanta ta dan girgiza ta dube shi, tunda ya lumshe idannuwansa bai bude ba, a hankali take bin bak'ar rigar dake jikinsa da kallo wace bata kama shi sosai ba har zuwa hannayensa
Jijiyoyin hannayen suka fi dauke mata hankali,
Dan ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta lumshe idannuwanta itama tana dora kanta a gefen kafadar Nahidt

Nahidt ta yi dan murmushi tana cire kanta a kansu, domin dukan motsinsu kallo take tana kuma binsu da fasara a kasan zuciyarta

Sun sauka lafiya, a nan ya rabu da sojojin da suke tare, ya amshi mota daya ya tuka su, kasancewar dare ya fara tsalawa ya sa du suke lulumin barci har suka karaso gidan CHIEF OF ARMY

Nan idannuwansu suka bude tarrrr sunna bin tsaro da tsarin ginnin da kallo
Bai zame ko'ina ba sai cen ciki bangaren matan ya parka motar ya bude ya fito yana lumshe idannuwansa domin yinwa yake ji, ga gajiya, ga bacin rai

"Um, kamar ba za'a mutu ba jama'a" ta fada tana waigawa tana sake kallon yannayin gidan

Shima da yake kallonta gannin botiran rigar daga kasa har sun babale hakan ya sa sosai yanzu aka fi gannin tsarin halitarta ya tabe baki a kasan zuciyarsa ya ayana 'ko dai kina abu kamar ba zaki mutu ba'

Gaba ya yi, hakan ya sa suka bishi da dan sauri gaba dayansu

Babar kofar ya kama ya dan kwankwasa kafin ya bude ya tura da salama a Bakinsa

Da sauri ta mike daga zaunen da take tunda ya ce da ita gasunnan zuwa take zaune da carbi a hannunta hankalinta a tashe

Da sauri ta karaso tana riko hannayensa tana duduba fuskarsa da hannayensa ta shiga fadin" MUHAY me yake damunka? Me ya sa ka fito da daren nan, wani abu ya faru ne? tell me Son me yake faruwa da kai, dan Allah yau ka fada min abinda yake damunka ka ji? Ka sanar min ko hankalina zai kwonta ka ji?"

A hankali ya rike hannayen nata dan ya tsayar da ita waje daya ya dago da hannayen nata kusa da bakinsa kasa kasa ya ce" mahmanah, mamah me yasa baki yi barci ba har irin wannan lokacin?"

A hankali ta ce" Kana tunanin zan iya rintsawa ne?, Ka ce zaka taso fa, ta yaya zan iya samun nutsuwa dan Allah?"

Ajiyar Zuciya ya sauke a hankali ya ce" I'm hungry mamahnah"

Cikin nasa ta kalla tana dan kwalalo ido ta dafe gaban goshinta tana fadin" mu je ka zauna na shiga kicin mu je"

Sai da ya kauce a gabansu idannuwanta suka sauka a kansu
Su biyun sunna tsaye a bayansa ne sun zuba masu ido da yannayi na birgewa
Fuskokinsu sun shinfidar da yannayi na birgewa a tatare da su da shaukin kallon soyaya irin ta uwa da d'a, du girman jiki irin nasa da tsarewar gida sai gashi yana magana kamar dai a dan shagwabe duda muryar dai gatanan dai bata da risinawa, aman kuma ta bada amo daban kamar na kana shagwabar nan

Kallonsu take daya bayan daya, idan ta kalli wannan sai ta kalli wancen, hakan ya sa sukaa tsargu harma suka sha jinnin jikinsu

Wani lalausan murmushi ne ya bayana a saman fuskarta ta juyo wajen MUHAY da ya karasa saman kujera ya zauna yana lumshe idannuwansa a sanyaye ta ce" SHUWWAR ? "

Nahidt ta saka hannunta ta dan turo Shuwwar gaba tana Murmushi

A sanyaye Shuwwar ta dan hade hannayenta tana sada dubanta daga kallon Mama kai tsaye
Ta samu kanta da jin nauyi da kunyar maman tamkar a waya da zasu yi magana

Mamah ta saki murmushi tana sake juyawa ta juyo ta kamo hannun Shuwwar a sanyaye ta ce" masha Allah, masha Allah, tamkar balarabiya my daughter masha Allah Marhababikum" ta idasa tana kamo hannun NAHIDTma tana janyo su ciki gaba dayansu

Nan fa mama du ta rikice ta zaunar da su , sunna hada baki wajen gaisheta aman ita fadi take" Bara na je kicin ku zauna bara na shiga kici oh ya Rab MUHAY baka ce da ni da su zaka zo ba, ka taso su da daren nan haka?"

Shi kam kallon maman nasa yake da mamakin farin cikin dake saman fuskarta dan ta gansu

A sanyaye Shuwwar ta ciro ledar dake cikin jakarta tana budewa ta ce" Mamah, kar ki je kicin da daren nan, ga abincinsa da bai ci ba, idan kuma sabo yake so sai na je ki zauna ki huta plz"

A hankali Mama ta juyo tana kallon fuskar SHUWWAR din, haka shima sai ya samu kansa da zubawa fuskarta Ido

Mama na kallon abincin a sanyaye da yannayi na farin ciki ta ce💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 3️⃣8️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Chapter 68 · 0% Book details