← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 138

Sashe 133

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Nahidt ta lumshe masa idannuwanta sannan ta bude , ta dan dantse lebenta na kasa tana wanna idannuwan nata a hankali sai kuma ta ciro harshenta kadan ta dan lashe saman lebenta da yannayi irin na baban lamari, sannan ta hade lebunnnan nata ta tura masa kisss lokaci daya ta yi kamar zata dan duka da idannuwan nata ta masa nuninda wajen da Sahiba take kilace sai kuma ta dora hannunta na dama a kan mamanta dake cikin rigarta ta atampa ta dan matsa wajen tana yatsine fuskarta sannan ta shagwabe bakinta bata ce komai ba

Sai da ya ja numfashi ya yi saurin matse kafarsa a birkice ya sake kallonta sai kuma ya kai dubansa kan Furera da ta kusa suma da gannin barikin da take fada tsagwaronta

Baakinsa na rawa ya ce" Ba'a kyauta ba, Allah ya baki hakuri ba za'a kuma ba Kin ji Furera? Ku tashi ku je yau barci nake ji da wuri Allah ya baku hakuri gaba dayanku ku je ma karasa maganar da safe in sha Allah"

A nan ne ta gabatar masa da abinda take so a dora, bayan furera ta wuce fuuuuu

Ido ya tsatsareta da shi na dan lokaci , ta cikin idannuwan nasa kuwa yake aika mata da sakwanin dake cikin zuciyarsa
A hankali kuma ya janye ya maida kan hajia a nutse ya furta" Wai haka Nananah?"

Hajia ta gyada kanta tana tabatar masa hakan NAHIDT din ta yanke

Ajiyar zuciya ya sake saukewa a nutse ya furta" Allah ya kara mana fahimtar junna da zama lafiya a tsakaninmu ya kauce dukkan fitina, Allah ya sa hakan ya fi zama alkhairi

Haka yana ji yana ganni NAHIDt ta mike ta masu salama ta fice a falon

Yana zaunen idannuwansa na Kan Hajia dake ta kokarin zuba masa abinci

A hankali ya saka hannunsa ya kamota ya dorata saman cinyarsa a sanyaye ya ce" Maryam ni yinwa nake ji"

Abincin ta kalla ta kuma kalle shi da mamaki ta ce" Yah Ustaz to bara na zuba maka....."

Kansa ya girgiza a hankali yana sake kashe ido ya ce" Ai mai gari ya cikan cikina sosai harda guzurin fura, shi yasa Sahiba ke ta neman abincinta............."
Kanta ta sada tana Murmushin jin kunya da kuma mamakin yadda Malan ya dubeta bayan ya samu daleliyar diya irin NAHIDt? Sai dai tuna cewa mijinta kai adalci ne, samun wace ta fita kyau ba yana nufin zai wulakantata ba, dan haka ta aniya bashi hadin kai da iyakar iyawarta domin Malan baya rabo da bada darasi kala daban daban.....yakan ce baya so a tashi daga zikiri da cutarwa ta kowani gefe........ 😍

______________________________________

Kwana uku tsakani ya kasance Nahidt ta rufe sati a gidan Malan, hakan ya sa yau yana anguwa sunna mesage take fada masa tana son zuwa gida ta kai ziyara , sun yi zasu hadu da Shuwa su wunni a cen gobe idan har ba damuwa
Hakan ya sa ya yi mata tambayar ita daje fama da barcin nan na gajiya ba lokaci ba zata yi hakuri ta karra hutawa ba kuwa?

A nan take sheda masa ita fa ta fara tsorata da barcin nan, domin Allah bata tare da gajiyar komai, shi yasa take son zuwa ta fadawa Mamansu ita kanta abinnan na damunta, yanzu ana hira da ita kana iya juyowa ka ga barci ya yi awon gaba da ita, abu kamar sammu? Kar aje a matsayinta na babar yar sarki an samu wani zai mata aiki da cikawa.....kai da ta shiga uku cutar barci ai cuta ce mai girman gaske sosai da sosai😌 (😂 toh fa)

Ya dai bar maganar kan har ya dawo

Da dare da ya shigo ya samu Furera an gayu a bangarensa, tuni ta gama shiryawa zuwansa domin yanzun fa su Madame Furera abin ya karra daukaka, daraja take kankarowa kanta ba ji ba gani, shi yasa ake shafa jan baki a kamanta barikin nan, tunda dai ai rami ne kowa nada shi a jikinsa itama zata iya sarafa nata tunda ta kula maza yan cin amana ne (🥺 kashhhhhhh)

Kamar yadda aka saba zuwa a gaishe shi hakan ne, sai dia Hajia kadai ce ta zo yau

Har dare na neman tsalwa shiru ba NAHIDt, hakan ua fara daga masa hankali, dan haka ya fadawa Furera zai lekata, du kuwa da ta nuna a kan me ai lafiyarta kalau ya nuna mata hakinta ne ya san ta wuni lafiya sannan ya san ya barta lafiya wajen barci, tama shirya gobe kowace ta je ta ziyarci gida

Da wannan ya samu ya fito ya nufi bangarenta

Tunda ya kama kofar ya bude ya ji ta budu ya ji hankalinsa na Neman tashi

Da sauri ya shige yana waige waige da salama a bakinsa sannan yana kiran sunnanta

Gabansa ne ya yanke ya fadi ganninta kwonce saman kafet, ga dukkan alamu barcin nan tun na sallah da ta yi ne ta kudundune sai yinsa take tamkar wace ta mutu

Da sauri ya dagota yana juyota dan gannin jikinta lokaci daya kuma ya ce" Nahidt, NAHIDt ?"

Luuuu ta yi d idannuwanta tana kallonsa sia Kuma ta maida ruf bayan ta masa murmushi hadi da fara ambaton sunnansa barcin ya kuma yin awon gaba da ita

Hankalinsa ya sake tashi ya cire mata hijab din ya dauketa ya yi ciki da ita

Saman gadonta ya dorata ya aniya damunta da tambayoyi yana ta damukarta dan ta farka

A fuzge ta saka dan kukan shagwaba tana ture shi ta ce" Muhamad barcinma ba za'a barni na yi ba sai an saka min ido, haba ina yanci na dan kasa ne wai a gidan nan?"

Ta idashe tana juyawa hadi da jan bargo ta sake rufawa a jikinta

To fah malan ya rikice, lokaci daya ya shiga karatu irin na rukiya, ayoyin karya sihiri kai babu adu'ar da bai kamo ba yana mata tofi aman ko gezau , barcinta take tamkar wace ta sheka, kuma ga dukkan alamu barcin ya yi nisa kuma tana jin dadinsa

A kan dole ya mike ya sake rurufeta ya kuma yi mata adu'a ya fice bayan ya sake shafa fiskarta ya rufe ya tafi da ky din

Da asuba shi ya budeta ko barcin kirki bai samu ba ya tasheta dan ta yi sallah
Tana layi sai da ta shige bayin sannan ya iya sauke ajiyar zuciya yana tsaye gudun kar ta yi barcin a bayin har sai da ta fito sannan ya wuce masalaci

Koda ya dawo sai da ya kuma lekata, yanzun kam ya gama yarda zai kaita gidan da kansa idan aka ce a je asibiti sai a je, idan kuma wani aikin sihiri ne sai a dauki mataki mai karfi, shi kam ya fara tsorata da wannan barci tamkar an sauko mata da shi? Kafin ya fita sai da ya fada mata ta shirya fa zai kaita gidan da kansa, sanann ya fice

Sai da ta shirya din sannan ta koma ta kwonta ta sake yin barcinta a falo domin ko kari bata yo ba, ta fi damuwa da barci sama da karin, so dai take a jima kadan ta farka ta ci domin sai tana barcin kuma yonwar zata tasheta sai ta ci kamar me sai kuma ta koma

Da karfe goma sun gama fitowa domin yana mota zaune ne da kansa zai tuka su yana kiran kowace a waya ya fada mata ta fito yana mota sai da ya yiwa NAHIDt kira uku ta daga kamar ta yi maye , a sanyaye ya fada mata ita suke jira sannan ta hantsilo tana murje ido ta dauko hijab dinta da nikaf dinta da wayarta ta fito tana rufe bangaren nata ta karasa wajen motar ta bude baya ta shiga dan ta ga tuni hajia baba ta hakimce a gaba warau Furera

Da kula da tausayi ya ce" Barcin ne dai?"

NAHIDt ta gyada kai, sai kuma ta shiga matsar kwallah ta ce" Na shiga uku, barcin nan na damuna"

Hajia ta ce" Subahannalah wani irin barci kuma?"

NAHIDt ta ce" Inaga an shiga gabana ne , na shiga ukunna hajai barci ba dare ba rana ba lokaci? Yanzunma jinsa nake kamar fatar idona zata like"

Hajia ta ce" Subahannalah malan bata da lafiya ne?"

Malan ya sauke ajiyar Zuciya ya tashi motar bayan ya yi adu'a ya ce" Shine zamu je gidan a ji, ga dukkan alamu bata da Lafiya ne "

Cike da kulawa Hajia ta ce" Aya, Allah ubangiji ya sa ba komai na damuwa bane, aman bara to nima ja biku, dama gidan gaisuwar ne zaku ajiyeni idan aka tabatar ba komai bane sai na tafi wajen su inna gidan gaisuwar"

Malan ya ce" Aa, ki je wajen rasuwar nan, kin ga jiya aka yi baki samu sutura ba, yau ki wuni a cen idan da wata matsakar duka zan kireki"

Kai ta gyada tana fatan alkhairi , Furera kuwa ta tabe baki tana fadin" Ni a gidan Nabilah zaku ajiyeni yaronta ne ya kone"

Itama amsar ya bata ya ci gaba da tukin, domin ba zai iya jan kowace magana ba, ita ke ciwon shi ke wahala, bai rintsa ba haka zuciyarsa ke bala masa balin balin kamar ya cire ya ajiye ya huta

Sai da ya ajiye su sannan ta koma gaban , sunna tafe yana mata sannu har suka karasa

Tun daga waje ya ringa godewa Allah da ta saka Nikaf, domin dogaran ne, matan ne kowa marhabin yake masu ana gaishe su a tsugune ana girmama su

Jakadiya ce ta masu jagora tana fada masu ai Hajia IBTISAM sun jima da zuwa ita da Soja sunna ciki

Ita dai NAHIDt jinta take yi domin ji take kamar zata kifa ta yi ta barcin, ko kula da tsarin gidan nasu bata yi ba burinta ta ganta a saman wani dan abin kwonciya ta dan raba ta dan huta.......
Chapter 133 · 0% Book details