Sashe 28
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fauziya da jikinta ya fara sabawa da faduwar gaba a kan lamarin Hamza ce ta yi watsi da komai ta fuskanci mutanen nan biyu, NAHIDT da Shuwwar zata iya cewa sunne ahalinta, a tare aka kwaso su a tare jirgi ya sauke su a garin nan, ba dangin iya ba na ABA tafiyar jirgi ce ta hadda su, aman suka hadu da niyar su taimaki junna ko dan samun abin kaiwa baka, Nahidt dai ta fisu a lokacin kuma ta fisu rashin tsoro a lokacin........a haka suka rungumi junna in wani tudu in wani gangare har suka kawo yau a tare, da dukan karfinta ta kori shedan tana mai ayanawa zuciyarta cewa' zuciya ki bar rudani duniya ki bar rikita ni!' domin ta rigaya ta yiwa kanta alkawarin ko mutuwa zata yi sai dai ta mutu da abin kunyar nan
A sanyaye ta yi murmushi tana fadin" Shushu, me kika rasa na y'a mace? Ki duba ki ga tsarin halitar da Allah ya yi miki, kina da harda a kanki, sannan ba kaifi daidai gwargwado na bokon muna da mu dukanmu, Shushu dan kadararmu ta zo a haka shikenan sai mu yi tunanin bamu da daraja ?, Muna da ita mune muka karra watsar da ita, shushu mace tana da daraja, tana da mutunci, du kuma namijin da zai riki mace dan ya wulakantar da ita tabata bai san darajar mahaifiyarsa ba, da ace ya sani da ya yi duba da irin nauyi da mamansa ke dauka a cikin gidansu ya rike matar aurensa da daraja haka kuma ya dubi na waje da daraja, meye mace ta yi maka? Allah ya halita maka ita ne dan ta kasance abokiyar rayuwarka, wace zaku rayu da farin ciki ko bakin cikinka tare, wace zata haihun maka ta dauki dukan nauyi naka, itace zata zamto abar da za'ana harin rayuwarta har a ringa furucin kar ka sakkar mata fuska zata rainaka ne? Wani raini ne ya yi saura kai da kake kasancewa zigidir a gabanta bayan ka fita shekaru ko yayane? Wani raini kake magana a kansa matar da ta ga ka rikice ka nemi nutsuwa ka kuma samu a tare da ita? Idan a duka bayan wannan bata rainaka ba ai bai dace ka yi tunanin zata rainaka ba a rayuwa, maganar raini ai ta kare da ace kana da hankali, kin ga Hamza yana da mutunci, abinda kike ta jaje kansa kan shaye shayensa kin ce ya halata ka zauna da mashayi bayan ka san mashayi ne? Wannanma gaskiya ne aman yaya kike so mu yi? Mu shine mutun a wajenmu, shansa kuma bai hanna shi ibadarsa ba, ido rufe ya hanna ki sha sannan a bayane ya nuna burinsa ya dauna sha, shaye shaye na saka bawa aikata munanan laifukan da ba zai iya gogewa ba a duniya, a haka zamu amsa mu kuma taimaka masa muma har ya daina, in sha Allah zai daina sha Shushu kuma zaki ji dadin zaman aure da shi"
Nahidt na murmushi ta ce" ki kunce min kunshin nan na wanke na yi wanka na je kasuwa, na ga kurkum dinmu da madarar sun yi kasa sosai bara na je na siyo kayan gyara da kuma kayan hada turaran wuta da na ruwa da su humura mu zo mu jika na jikawa mu soya na soyawa mu shiga shiri, Shushuna kin san sai na maki garra a wannan auren..........sai na fitar da bokici bokici na kayan aurenki, yanzu ne zan aurar da y'ata ! Ta karashe da yannayin tsokana dan ta san yanzu shushun zata ce ke ni yayata ce ke mamana ta rasu
Sai ta ga Shushu bata ce komai ba tana daria kawai kasa kasa itama ta kama kunshin ta shiga cire mata a nutse
Tabas yanzu ne suka dauki auren nan da mahinmanci
Sau uku kawai Malan ya lamuncewa Hamza zuwa wajensu dan shirye shiryen da suke yi, a wannan zuwan nasa uku da ya yi a falonsu ake yin zaman gaba dayansu a ringa hira anna barkwonci
Watau Hamza kamar wani jigo mai saka su farin ciki ya zame masu, a ranar kuwa da ya zube kudin gyaran amaryarsa sai da suka kusan haukacewa gaba dayansu domin a bayane suka rikice da tarin kudin nan
A lokacin Nahidt ta riki kudin ta ce" kai dai kawai Allah nuna mana Hamzanmu"
Shuwwar kuwa kai ta sada tana daria kasa kasa dan ta san fitarsa ake jira su kwaso shoki a gidan nan, domin jiya jiyan nan take maganar kudi ya fara kasa sun shiga uku
Kafin ya tafi yake fada masu maganar kawo lefe ya ce in sha Allah ranar daurin aure karfe bakwai mata zasu kawo lefe, domin a ranar ne danginsa na cen gidansu Tanus zasu zo sun ce sai sun zo zasu kawo lefen da mamana, kin san babana da son ya kankaro min daraja, to dai inaga fen zasu hade su kawo su, mu dai da angwaye zamu zo mu rakashe a kada manaa ganga oh...su Hamza za'a angwance................
Ire iren barkwoncin da ya saka Shuwwar din kanta yi masa waje mai mahinmanci ta ajiye shi a cikin zuciyarta
Zata iya cewa sonsa take yi, ta kamu da sonsa ne, yo ai ya isa a so shin, meye aibunsa? Bashi da wani aibu da zai zamo aibu a wajensu gaskiya, ko daya bashi da shi
Daga wannan lokacin bayan gyaran jikin amarya da suke yi sai suka koma gyaran baban falon
Watau dafe dafen kaza irin nasu na saudiya da suka koya a wajen mahaifiyarsu babu kalar wanda basu dafa mata ba kuma suka tisa keyarta ta cinye
Idan aka zo fannin maganin sanyi, maganin basir , tsumi kuwa cikinta har ya saba du irin yadda take nuna ta gaji cikinta ya cika a haka yayarta zata ajiye mata ta ce da ita ke dai dan karra sha ke dai kin jiya yar kanwata?
Da wannan suka ringa tunkarro lokacin har ya yi saura sati daya daurin auren, a nan ne Shuwwar ta fitar da akwatunnantaa dake jejere a dakin da suma rufe suka baje komai
A nutse suka fitar da kayan dinki masu mugun yawa wa'inda Shuwwar ta murje ido cewar in dai sunna so ta dauka sai sun dauka summa
Ai kam suka daukan kayan fitar biki masu yawa suka bari magariba na yi suka shige motarsu suka nufi wajen telensu wanda dama su yake jira
Kaya suka zube masa suka zube masa kudi da kwanakin da suke son kayansu
Ya kuma amsa ya amshi kalolin dinkunnan da suke so ya rabawa yarensa suka shiga aiki
Ana sauran kwana biyu daurin auren Shuwwar , hakan ya sa yayunta suka shige cikin hali na busy
Ba tarro suke yi nasu na kansu ba, abinda ya shigar da su a busy hade haden garra ne, idasa rurufe tarin uban turarukan da suka hadda mata na wutan ne da na ruwan, ga kuma na saudiya da suka siya a garin mai tarin yawan gaske irin na cikin yan kannanun kwalaben nan mai masifar dadi, Shima sun masa wajensa daban sun daure..............kai gata dai shuwwa ta same shi sai fatan alkhairi da zaman lafia da mijinta
Daga wanka ta fito tana tafia a hankali ta zauna saman kujera gaban sif dinta tana lumshe idannuwanta sanadiyar kanshin da jikinta ke fitarwa mai mugun dadi da irin laushin da jikinta ke karra dauka balema idan ta taba ruwa
Manta da ta hada mai karra fitar da darajar fatarta ta janyo a nutse ta shiga shafawa tana sake lumshe idannuwanta dan santsin da yake karrawa jikinta gaba data ga kuma irin nasa kanshin mai sakawa bawa nutsuwa a zuciya
Wayarta mai kirar apple watau iphone wace angwonta ya gwongwajeta da ita ta shiga dan haskawa alamun kira na shigowa
A nutse ta janyo wayar ta daga kiran tana karawa a kunnenta ta yi salama da sansanyar muryarta
A sanyayen shima ya ce" I'm sorry wifey yau du ban yi kira ba, kin san menene? Yadda kika san tashin duniya haka babana ya dauki daurin auren nan, har tunani nake anya anguwar nan ta dauki bakinsa kuwa? Yanzuma daga masaukin da zai sauke uban gidansa nake kin san bayan ya yi ritayama akoy kyakyawar alaka tsakaninsa da Chief of army, so ya tabatar masa shi zai mika sadakina wa Malan shine fa du babana ya rikitamu kan zuwan bawan Allahn nan, ina fata ba'ai min fushi ba?"
Dan murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta ta ce" Ban yi ba"
Watau jan aji, ko yace girma irin na Shuwwar na bashi mamaki, tamkar wadda ta shafi jinnin sarauta wani sa'in, shi tunda ya santa idan ka ga ta budi baki ta maka doguwar magana ta danganci abubuwan da ta gani na rayuwa ne irin sake saken da maza sukai mata na aure, bayanshi ko da su Nahidt sai dai ya ga kasa kasa ta yi tsokana ta kuma koma ta hade abinta kamar ba ita ta yi ba, sai Nahidt din ce zata ringa bambami ana riketa, wani lokacin har tunani yake shi mai maganar nan sai ya hadasa mata ciwon kai ai, domin shi dai tsakani da Allah, Allah ya yanka masa abin magana yi zai yi ta yi abinsa
Yar dariya ya yi a hankali ya ce" Kina irga awani kuwa?"