← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 138

Sashe 80

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SHUWWA ta lumshe idannuwanta a sanyaye itama ta ce" Kin ga, abinda ya yi niya zuwanmu ko dakatawarmu ba su zasu hanna shi yi ba, kin san ai yana da gardama sosai, bana tunanin mun isa mu saka shi ko mu hanna shi wani abin, Allah ya zaba mana abinda ya fi zama alkhairi zo mu je kin ga sun bude bayan motar chan"

Kafin suke karasawa suka ga Mama ta juyo a firgi ce tana kallonsu, kafin ta daga masu hannu tana fadin" Kar ku karaso ku tsaya daga cen......"

Gaba dayansu suka ja suka tsaya gabansu na ta faduwa

Mama da jikinta ya dauki rawa ta kalle shi tana fadin" Ka karra ganar da ni abinda nake ganni a kamanin matar nan da yayar matarka MUHAY"

Gwauron numfashi ya sauke ya ce" Kadeta na yi, ................" A sanyaye du ya fada mata abubuwan da suka faru har zuwa yanzu, hakan ya sa a wani firgicen ta sake kallon Matar dake hangensu aman bata jin tataunawar da suke yi, gaba daya kuma ta sake tsurewa da tunanin har an shigo da su wajen da za'a sake salwantar da rayuwarsu kennan

Ta so ta nuna masa idan y'ayan suka ga mutumen nan kuma ya kasance mahaifinsu ne a haka a lalacen nan hankalinsu ne zai tashi sosai

Sai dai kuma ta tabata uwar ba zata yarda a rabata da mijinta ba da wani kwakwaran dalili ba, sannan a yanzu ba zata so ci gaba da ganninsu sunai mata kallo irin na marayun nan da zarar ta kyautata masu ba, haka kawai take jin kaunarsu a cen kasan zuciyarta da son kyautata masu, dan haka ta sake fuskantarsa ta ce" Da ka fadawa Abanku mai yace?"

Hannayensa ya dan watsa ya ce" Yana cikin taro ne, na dan so kwatanta masa na ga zan yi ta magana ne ba zai fuskanci inda bayanina ya dosa ba"

Kai take gyadawa ta nufi motar ta sake bude bayan

Matar ta dan takure jikinta tana kallonta hakan ya sa Mama fashewa da kukan tausayi tana kallonta

A sanyaye da yaren buzanci ta ce" Su waye suka wulakantaku haka har suka saka muku tsoron mutun dan uwanku mai numfashi? Kin ga yaya sunnanki dan Allah? Kama hannayena ki zo ki ga wani abu, taho ki gani kin ji?"

Duda yaren haihuwarta Mama ke yi, sannan kalaman na mama kalamai ne masu saka Nutsuwa da yarda a zuciyar mutun, aman gaba daya sai Manma ta kasance kamar kurma a gabanta sannan ta kasa barin jikin mijinta du sai takura masa take yi bata sani ba

Sosai tausayinta ya karra kama Mama, ta juya wajen MUHAY zata fada masa cewar ta ki yarda ta fito sai ta ga ya juya wajen da suke da hannayensa ya yafito su

Sai da suka kalli junna kafin suka nufo shi kowace jikinta a mace sosai da kuma tsoron abinda yake faruwa

Sunna zuwa wajensa ya saka hannunsa ya kamo na Shuwwa hakan ya sa ta dago tana kallon fuskarsaa hadi da jin faduwar gabanta na tsananta

A hankali ya ce" Yaya sunnan mahaifiyarki?"

Shuwwa ta karewa lebunnansa kallo da ya dire maganar , hakan ya sa idannuwanta suka farra rawa

Nahidt dake kallonsu ce ta kai hannayenta wajen kirjinta tana rungumewa a hankali ta ce" Tsoro nake ji, jikina bari yake yi, Shuwwa tsoro nake ji, wayo Allahna me yake shirin faruwa? Yalabai me kake so da sunnan mahaifiyarmu? Sunnanta TINANA, haka sunnanta yake Shuwwa me yake faruwa ne ?"

Tunda ta fara magana matar ta juyo da karfi tana kallonsu ta madubin motar, kasancewar mai duhun gilas ne sai dai ka ga wanda yake waje ba dai shi ya ganka ba

Kalaman dake fitowa daga bakinta suka saka matar sake kura mata ido har sai da idannuwanta suka fara zafi

A yanzun da kanta ta miko kafafuwanta ta nufo fitowa jikinta na rawa har ta bayana gaba dayanta a waje kafin ta zubawa yan matan ido gaba dayansu

Wajen da ya zubawa ido suka juyo dan gannin me yake kallo ne kuma?

Kallon yan matan take yi itama da wani kallo mai nuni da kamar tama a tsorace da ganninsu a haka ne ko kumaa bata yarda cewa wadinnan din y'ayanta ne da ta haifa a duniya ba duba da ta baro su a cen karshen duniya yaya aka yi suka samu zuwa nan? Kai kwata kwatama ta yaya suka samu kasancewa a nan kai tsaye haka? Haka summa suke masu binta da kallon da ya dakatar da bugawar zuciyoyinsu, ballema Nahidt da wayonta a lokacin ya fi karfin wasa ko yaya mahaifiyarta ta zama ba zata bace mata ba, zuwa Shuwwa din da karfin jinnin haihuwa da kamanin suke ta dawo mata suka sakata daskarewa tana kallon matar da a jikin mahaifiyarsu kamar an raba hudu ne an bata daya, haka farin fatarta ya yi duhu , sannan fatar tata du taa bushe ba kamar matar da sukaa sanni yar gatan mahaifinsu mai kyau da tsari, mace mai lafiya da fara'a ba

A hankali SHUWWA ta ringa lalube a cikin duhu, domin so take sai ta riko hannu a cikin hannunta, aman ta kasa riko hakan har dai Maman MuHay ta fahimci haka ta karasa da sauri kusa da ita ta riko mata hannun tana kallonta hakan ya sa ta juyo, sai dai gannin ba Nahidt din bace sai ta saki hannun da sauri ta kuma damko na Nahidt din tana kallonta a dan tsorace ta ce" Kin ga , kina kuwa ganninta? Nahi itace?"

Nahidt ta juyo a hankali tana kallon fuskar SHUWWAR
Da karfi ta janyo Shuwwar suka rukunkume junna ta fashe da kuka mai karfi tana ihun fadin" wayo Allahna wacece wannan mai kama da mamanmu? Wayo Allah mun shiga uku , Mamanmu ba haka kamaninta suke ba, wannan ramamiya ce kuma ....kai wayo Allahna Shuwwa ba ita bace, ba ita bace SHUWWA ba ita bace....."

SHUWWAR dinma da jikinta ke rawa ta sake neman bambarewa daga jikin NAHIDT, sai dai tai mata wani irin riko tana kuma fadin" Ba ita bace, su a saudiya aka ce sun rasu, a saudiya muka baro su, a saudiya aka kamo mu aka baro su, au din ba zasu taba yin nesa da mu su barmu daga mu sai mu a cikin duniyar nan ba, Babanmu ke cewa zai iya yaki da duniya kaf saboda mu, su ba zasu barmu a wulakance ba...... Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ki yarda sun rasu, ke ko yarda sun rasu mun fara gannin fatalwarsu ne ko? Du laifinki ne, kece kike taos su daga kabarinsu!"

Matar nan dake kallonsu kamar an dasata idannuwanta ne suka farra gannin dishi dishi

A hankali ta dan sake kallonsu tana ta hanna kwakwaluwarta yi mata cakule dan bata so ta hargitsa mata tunaninta

A hankali ta dan daga kafarta muryarta a cen kurya da yaren larabci ta ce" NAHIDT, IBTISEEMMMM...... "💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 4️⃣5️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A hankali ta ce" NAHIDT.......IBTISEEMMMMMMM......." Sansanyar, zazakar murya mai irin nata salon da har yanzu babu bawan da ya lakanci sunnayensu kamar wa'inda suka zabar masu su ne suka sake dokar dodon kunnayensu, hakan ya sa a haulace suka saki junna sunna masu zuba mata ido a lokacin da take karasowa tamkar jikinta zai rabe biyu domin har kadawa take yo tsabar rawar da jikin nata ke yi har ta karaso wajensu ta kai kasa kamar yadda suke kasa ta zubawa fuskokinsu ido tana kallo

A hankali ta daga hannunta ta kai daidai fuskar Shuwwa dake kuka tamkar zata side ta shafa gefen fuskar tata a hankali , sai kuma ta saki wani irin lalausan murmushin da ya bayanar da farin ciko, nutsuwar da ta jima bata yishi ba a saman lebunnanta duda a busshe yake kamar yadda hannunta yake bushe kafin hannun nataa ya sakai ya tafi ya fadi kasa , alamu suka nuna kansu na ta suma ne

Ihu suka saka kusan a tare, wanda ya saka Mama zabura daga hawayen da take ta nufo su da sauri tana ambaton sunnan Allah gannin yadda NAHIDHT ke girgizata tana sake girgizata tana ihun fadin" ANNNA,, kar ki mana haka, baki mutu ba tun baya kar ki mutu yanzu, Anna ki tashi ki ji irin rashin jin da muka tafka ki zane mu, Anna kin san da ni yawon banza na ringa yi Ibteen Papy kuma ta ringa aure auren maza? Anna Annannnnnnnnnmmmmmmmmmmm"

Idannuwansa ya rintse a kansu a lokacin da IBTISAM ta mike tana nufo shi da wani irin wawan karfi ta juyo wajen da ya juya ta rukunkume shi a jikinta gaba daya ta fashe da wani karayan kukaa tama sake shigewa jikinsa, hakan ya sa sukai tangal tangal sannan ya sake tsayawa da kafafuwansa yana sake rintse idannuwansa
Chapter 80 · 0% Book details