Sashe 3
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Chirp OF Army ya fada a kausashe yana kallon fuskar mahaifiyar Lieutenant Ganaral din dake zaune a fallonsa
Sannin cewa ba zai ce komai ba ya sake fadin" Da kai nake fa?"
Dan gyaran murya ya yi yana fadin" Siga ta cika min a tea"
"Kennan dai da gaske ne dan ta kara maka siga daya a cikin tea dinka dan ta karra maka dandanon tea din ka salameta? Aure? Auren ne ka saki a haka?" Ya fada da dan karfi karfin da ya saka Kakarfan namijin nan rintse idonsa a hankali ya bude yana fadin" U see zan fara aiki ne, na karaso wajen Soldats"
Dan Jim wanda yake cikin wayar ya yi kafin ya masa salama dan ya san koda ya ci gaba da maganar a yanzu ba wani gane komai zai yi ba
Yana kashe wayar ya dubi mahaifiyar Lieutenant Ganaral din yana sauke ajiyar zuciya ya ce" Come on, calm down Madame, fushin ya isa hakanan mana, kema ai ta yi laifi yarinyar mana"
Da mamaki ta ce" Ta yi laifi? Ta yi laifi fa ka ce ELHAJ ? Wani laifi ne da ya cencenci saki dan an zarta siga a cikin tea? Anya kana son yaronka ya ci gaba da zama da mace a duniya kuwa? Ni yanzun ya fara bani tsoro, gaba daya Muhyideen ya fara bani tsoro, kuma zan fada maka walahi walahi zan je dakinsa yanzu yanzu da kaina wancen dakin da yake sauka lokaci zuwa lokaci na yi bincike na gani, Anya yaron nan ba yana da matsala ta mu'amalarsa tsakaninsa da mace ko namiji ba?"
Da sauri ya kafe fuskarta da kallo ransa na sake bacewa hakama dubansa na sake kausasa a kanta
A dagule ya ce" Kina da hankali kuwa? Subahannalah, dan ranki ya bace sai ki fara kawo wani tunani irin na mararsa ilimi kina zubawa a nan bayan a sanina kina da ilimi?, Dan kawai ya saki mace sai ki yi tunanin nan a kansa?"
Wannan karron muryarta sai ta yi kasa a kan ta mijin nata tana komawa saman kujera tana kuma sada kanta hakan kuma lokaci daya ta fashe da kuka tana yarfe hannunta ta ce" Watan auren nan uku da sati uku, kafinta ya saki wace ta yi sati hudu, kafinta nawa ya saka a jejere a jejere, shi ba mahaukaci ba, yana sakin matan ba da wani kwakwaran dalili ba, dan Allah dan annabi ba dole na fara tsorata ba? To ko bashi da lafia ne?"
Ta karasa fada tana dagowa tana sake kallon mijin nata
Shima sasauci ya fara yiwa hadewar da ya yiwa fuskarsa , muryarsa a sanyayen shima ya ce" Duka wannan bai kai wajen ambatar masa haka ba, Allah ya jikan aminina Marigayi da yana raye ya ji irin haka da ya nisa sosai a ransa, kin ga siga da ya fada ta karra masa a tea na tabata ba asalin shine damuwar da ta saka ya saketa ba, na san yanna da saurin hawa a kan kankannin laifi, na kuma san ya iya zartar da hukunci cikin sauri, aman bana tunanin zai aiwatar da aikin ganganci da sunnar ma'aiki irin haka ba, matsalarsa ba zaka iya gane inda ya dosa ba, ba fada yake yi ba, ba zai fito kansa tsaye ya yi bayani ba, idan kika ga ya yi dogon sharhi sai dai a kan mai laifi ne, aman ki yi hakuri ni zan fuskance shi in sha Allah, zan bi sahunsa in sha Allah, zan gane menene damuwarsa ne? Idan dai tunaninki na sako maki kila wa kala a kan lafiyarsa da mu'amalarsa ki sha kuruminki, lafiyarsa kalau haka kuma mata sunne ababen hutunsa ba namiji ba, kawai na fi karkata akalar matsalar a kan ko dai mace na fice masa a rai da zarar ya yi dan zama da ita, ko kuma sunna nuna masa halayan da ba zai iya jurewa ba kama daga Sata, karya, cin amana"
Ita dai bata sake furta wata kalmar ba har dayar matarsa ta shigo ita kuma ta mike ta fice a dakin gaba daya
Tana fitowa balbalin tankamemen gidan daya daga cikin y'ayan Elhajin mai sunna Zakiya ta duka har kasa tana gaisheta kanta a kasss sosai
Ta yi mamaki ainun da wannan Sabon salo na Zakiya daga bakin lokacin da Muhyideen ya zo gidan a matsayin d'anta, kai bama ita ba , ta ga cenji a wajen mutane da yawa na gidan harta da maman mai gidan nata
Shigewa falonta da macen police din dake biye da ita ta bude mata ta yi ta karasa saman kujera tana zama hadi da kure waje daya da ido
a bayane ta furta" Sata, Karya, Kula wani namijin? A karkashin auren MUHYIDEEN ? sai nake jin sam maganar bata samu wajen zama a zuciyata ba Elhaji"
Karasowar masu aikinta ya sakata sauke wata ajiyar zuciyar tana fuskantarsu suka shiga bayanin abubuwan da za'a girka a gidan
A dakin CHIRP OF ARMY
Tun da matarsa ta fara magana yake sauraronta har ta dire aya sannan ya dago daga danna wayarsa da yake yana turawa Muhyideen sako ya sauke dubansa a kanta
Wannan dai itace matarsa ta farko wace sukai auren saurayi da budurwa da ita, aman cikin ikon Allah halaya na mata na shirme wani lokacin komai tsufansu kan sakota a gaba, ita dai yanzun shekarunta na haihuwa Sittin da shida a duniya, aman takan aikata aiki irin na mai shan giya, watau wanu abin idan ta yi kamar tana cikin halin maye ne
Dan murmushi ya yi yana fadin" Kina nufin yar uwata kar ta zo da damuwarta wajena dan baki fita a aiki ba karfe hudu na yama bai yi ba bale ta ce aikinta ya shiga?"
Ajiyar Zuciya ta sauke tana fadin" Elhaji, idan an yi magana motsi kadan sai ka ringa gagawar nuna yar uwarka, ai a nan magana ce ake ta kishiya ba yar uwarka ba, idan damuwar ce da ita ta bari idan ta shigo sai ta fada maka ko? Damuwarta kulun ta wuce a kan d'anta? Na tabata a kan d'anta ne da ba naka ba ko? Elhaji yanzun yaronta ke hawa Jet din dake dauke da sunnanka, Jet din da malakarka ne a matsayinka na CHIRP Of army, shi Lieutenant Ganaral yake anfani da shi, ina tsoron gaba gaba ka yi irin na mai jan kunne ka rubuta shi a cikin wanda zai ci gadonka!"
Wayar ya sake kallo ya juyo ya sake kallonta da matsanancin mamakin furucinta, yana kausasar da fuskarsa ya ce" Ashe baki da wayo? Ashe ke din baki da tunani? Ya yi me da gadona?, Hum koda yake rashin sani ai ya fi dare duhu inji malan bahaushe, na maki uzuri har ki san wanene shi kafin ki yi maganar arzikin da na malaka a kansa, abu daya dai zan fada maki shine ki yi hakuri kin ji? Babu yadda zaki iya hanna shigowar damuwar da ta dangaci Son a gidan nan, domin kin ga mahaifinsa aminina ne tun muna yara har ya koma ga ubangijinsa, mamansa kuwa bayan hakkinta na matar aurena haka kuma yar uwata ce , sai dai na ce Allah ya baki hakuri"
Daga haka ya mike ya shige ciki yana rufowa dan bai ga anfanin zaman ba , domin a kan maganar nan ta ga damar da furfurarsa da yabarsa a fuska ta saka masa ciwon kai mai tsanani
___________________________________
Tsit kake ji wajen ya dauka du irin yawansu da girmansu
An yi masu layi ne, ko nace sun yi layi ne hawa hawa hawa hawa tun daga kan kwanar babar hanyar garin har karshen kwanar, kama daga kan soja, gendarma, costan, Police, garde da sauransu......babu kalar hular da babu haka kuma kowane kalar hula tafe suke da ogansu wanda shi kuma yake karkashin LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN
Cire abin kunnensa ya yi gaba daya yana sokewa a cikin aljihunsa
A yau kakin dake jikinsa da soja ne, bakake sidik da hularsa a kafe a kansa
Daga inda yake tsaye yana sako kafarsa gaba daya mutanen nan suka sara masa sannan suka ja suka tsaya basu sauke hannayensu ba
Bai basu damar sauke hannayen nasu ba har sai da ya shigo tsakiyar filin nan da tafiyarsa ta gagawa irin ta kakarfan namiji sannan ya ja da budadiyar muryarsa ba amsa amon murya ba komai ya bude 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.