← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 138

Sashe 136

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malan ya dago kansa yana fadin" MUHYIDEEN Furera ce fa, Furera iyalina? Yau Furera ce ta min min wannan abin? Ashe rashin hankalin nata ya kai haka? Ni walahi ji nake kamar na saketa na huta da shirme irin nata, ina dalili mace ba hankali ko daya? Ka ga har kiranta ta yi da mugun sunnan nan bayan na yi alkawarin du wanda ya kuma kiranta da shi sai na zane shi in dai na fi karfinsa?"

MUHAY ya sake tabe baki yana cewa" Gaskiya gwara kawai ka saketa, kai ni walahi na yi mamaki ko dai auren dole aka yi maka da ita ne? Ina dalili wannan fa ba zaka iya dukanta ba gaskiya tana iya nanaka da kasa baka ganninta ne wai? Yayama kake iya juya abar nan ne? Kai sbahanalahi gwara na auri kamar gajiyarka sau dari da wannan matar, kana gani fa gaba daya ba laushi ba lausasawa, ai da gangan na daga muryata dan na bambance da ihuna da nata wanne ya fi karfi? Wannan ta kwarara maku shi tsakiyar dare ai sai ku zata farmaki aka kawo ko yan fashi ne, inaga ka saketa ka auro wata ya fi alkhairi kawai"

NAHIDt ta yi saurin fadin" Haba yaya MUHAY, Haba abana kai kuwa ya saketa ya kawo wata fa kake cewa, ai ya yi hakuri ya sanyayar da zuciyarsa ya yi adu'ar Allah ya dora shi a kan daidai in sakin nata ne daidai to Allah da kansa zai karrar da zaman ba tare da ya kawo wata ba , idan kuwa ba shi bane Allah ya shiryeta, aman ba ruwansa da fadanmu gaskiya, kai ni nama yafe mata kawai a bar maganar ai dama ba kowa zata birge ba, aman ba sai an kai da su duka bama, duda na yarda da sadaukina ba ita ba ko gaba da ita yana iya horarwa ta kuwa yi la'asar ta yi sanyi walahi, aman bana so ni ma yafe na kuma yafe a bar maganar dan Allah"

Ido da hanci suka zuba mata daga Shuwwa dake jira ace a je a zaneta har mijinta

MUHAY ya juya wajen da nikaf din Shuwwa yake ya dauko yana miko mata da safar hannayenta yana fadin" Dan maimaida kayan nan mu tafi gida kin ji? Inaga Nahidt ta zama munafuka, wai mu zata nunawa zagaye? Ke din? Idan kin tashi yin kokowar dai da ita ki kula fa cikin nan dan idan ta nausa maki hannunta ya bare zan rufe ku ne a matsayin kun yi kisa, yan wulakanci kawai"

Shuwwa din kanta sakawa ta yi cike da mamakin kisar antyn tata, haka dai suka yi tafiyarsu da fada suka barta ta sake rike abinta tana rarashi da nuna masa dole zai ga irin haka, kawai ya kyale maganar cikin a yi fatan Allah raya itama Allah ya bata nata

Shi kam a gaskiya ya zama wajibi ya kaurace mata, ba dan komai ba sai dan kankin kanta, idan ta mike a haka zata fara halaka kanta ne a banza da wofi, gwara ta gane ta yi hankali

..............................................................

*A gurguje*ALKALAMIN KADDARATA

PAGE 7️⃣9️⃣

NA

SAJEEDA

END🤧

Cikin gata da kulawa suke
rainon cikinsu abun gwanin sha'awa, duka mazan lallab'a mtan suke dan wani abun idan suka nemi kirtashi dole suke nuna musu sunyi saranda ba dan komai ba sai dan cikunan jikinsu, kowace da na ta kalar laulayin, Shuwwa dai ba mai tsamari bane sai dai kawai canzawae yanayi na kana tare da d'an mutum a jikinka, inda Nahidt kuma har yau baccinta take sha hankali kwance, wanda hakan ba k'aramin shiga hakk'in malam yake ba indai kwananta ne, sai dai ya ya iya? Da ta fara fad'a masa baccin ma ba za'a barta tayi ba dole yake komawa daddab'ata har ta koma baccin, ya d'auki son duniya ya d'orawa cikin nan, fatanshi a yanzu d'aya ne ya ga me za ta haifa, mace ko namiji? Ya ji kukan jariri shima a kunnensa a hannunsa sannan ya ga yan halbe halben hannaye a hannunsa, yana matukar so ya ga budewar ido da Kuma kallon da za'ai masa a hannunsa, yakan ji tsigar jikinsa na tashi idan ya ga tana tube rigarta a gabansa, ba dan komai ba sai dan gannin da gaske jikinta ya fara tasawa ta yadda dole a gane shafafen cikin nan na dauke da dan mutun, domin tun yanzu cikin nata turawa yake yi sosai wanda hakan ya sa yake kan yi mata adu'a ba dare ba rana da fatan Allah ya bata ikon jure dawainiyar cikin da ita da kanwarta wace suke haduwar sati sati ko a gidan Malan din ko kuma a gidan Shuwwa din, ko a je gidan Mama wace ta ja masu kashedon su rage zuwar mata gida kar su jaza mata maganar mutane ace ta aurar da yaren aman kulun sunna gindinta ita kam su yi zamansu a inda suke
Shuwwa kam takan zuba tabararta idan ta rayo mata, tun dan zazabin farko farko da ta yin nan shikenan ya bi lafiyar jikinta sai dan karan kwadayi na cin salak wanda ya saka MUHAY koyar wanke salak, domin kadan daga aikinta a talatainin dare ta dan lalubeshi tace cikin nan du ya sakani aiki irin na yan giya, ka ga wai salak........., Sai ya koyi ajiye kayan wankesu a kusa idan ta bukata sai ya fitar da shi a frij domin idan aka saka salak a frij wajen da baya kankara sai ya shafe sati biyu bai yi komai ba, yana wankewa tana darwayewa tana yankawa a gefe ta more sannan ya mori lamari domin bata rowar kam ita, Nahidt ce ta harbu da harbi irin na rowa , mamansa kuwa ta mayar da zuwa abinda ya fi komai sauki a wajenta, dan ta nuna a yanzun a bar Shuwwa da maganar balaguro ita kam bata so, a barta ta reni cikin nan cikin nutsuwar da zata haife shi lafiya ba tare da an shiga wata damuwar ba, duda sun san basu isa su hanna komai ba, aman sunna kamanta kiyayewa

A bangaren Sultanma yana gabatar da mulkinsa daidai gwargwadon iyawarsa, ya saka an fitar da Uncle dinsa Ibrahim an dawo da shi fadar an kebanceshi a waje mai kyau ana ta yi masa dukkan taimaakon da ya dace na sihiri, cikin amincin mai duka kuwa a yanzun ya daina doke doke da neman fita da gudun da yake yi a da, sosai har ya fara kawo hankali a kan kiran sallah yana kamanta son zuwa ya gabatar da ibadarsa, hakan ya sa hankalin Sultan ya karra kwonci ya ci gaba da yin iya kokarinsa dan gannin garinsa ya dan samu daidaituwa, domin gari ne an riga an rushe sai a hankali koda za'a samu kansa, ba laifi samari na jin nasiha sunna kuma kokarin neman aiki hakan ya sa kashe kashe da fadace fadace a kan yan mata du ya ragu, summa yan matan yawanci da suka dakatar da makaranta sun koma bisa nasiha da shirye shiyen da aje gabatar masu a gidan redio na jan hankali da nasiha da nuni cewa kansu suke halakawa ba kowa ba, shi yasa du yawanci wa'inda suke iya jin kira suka sauko suka shiga kimtsa kawunnansu cikin salama sunna dawo da darajarsu koda kadan ne a cikin da yawan

Furera kuwa ta ga rayuwa gannin idonta, domin abu da ya yi abu da kansa ya sakata a mota ua mikata gidansu ya samu datijon mahaifinta ya sanar masa abinda yake faruwa, ya kuma taushi tsohon da ya rikice da tsoron kar aje ya saketa ne? Ya nuna masa ko daya bao saketa ba, zai so ta gyara halinta idan har zata iya zama da shi ta daeo su zauna, idan kuwa ta ga gaba zata karra dan ta samu haihuwar da na kasa bata a gannin shikenan sai a gabatar da komai cikin salama ta yadda zumunci zai dore
A nanne mamaki ya cika tsohon yake maganar wace haihuwa? Shin furerar ta manta accident din da ta yi tun tana budurwa wanda ta shiga mawuyacin hali domin cikinta ne ya fi dakuwa da mashin din da ta hau daga makaranta zuwa gida, wanda likita ke fada masu mahaifarta ta tabu ko kuwa bakin kishinta ne ya rufe mata ido? Shi kam malan rasa ta cewa ya yi domin a nan tsohon ya kirayeta ya tunasar da ita maganar da ya ringa mamakin yadda take rusa kuka tana fadin ai likita ba Allah bane bai isa ya yanke hukunci a kan haihuwarta ba
Rai bace datijon ya salami malan sannan ya lalubi butarsa ta alwallah ya jefeta da ita rai bace yana fadin" Ki kula, bakinki ya iya magana yanzu dai sai ki shige gidan ki ci abinda muke ci, dama ke kike taimaka mana sai ki tsiro da sana'a sannan ki kasa zaman ki ga idan da riba, ke ba'a guje ki dan halayanki ba kece mai abin fada a bakinki? Hurera ba zan ce maki duniya ba domin idan kuka karra lalacewa a kan haka ni zaki dawo ki kashe, Allah ya ganar da ke da kalar ganiyarsa wace zaki fahimta"

Tun daga ranar take rayuwa a gidansu, rayuwar da ta zo mata a cenji, ba yan aiki ba kudin cefanen Malan bale sansanyar muryarsa da lakausan gadonsa uwa uba abinda takewa kishin babu shi, haka ba cimar da ta saba sannan ba sanyin AC domin gidansu rufin asirin Allah ne Alhmdulilah aman iyayenta ba masu kudi bane, itacema ta gyara gida har suka samu rufin asirin domin ko a anguwar a haka sun fi kowa rufin asiri, shine take baza rashin da'arta son ranta har ta gunduri abokin zaman nata, da kyar da jibin goshi bayan ta cike wata biyu a gidansu aka dawo da ita ta dawo ta ci gaba da zama ba ruwanta da kowa sai mijinta tana kuma gannin yadda cikin mattar da ta tsangwama din ke karra girma da kuma irin yadda kamar da wasa yanzun a anguwar ake mutuntata bayan a da ta dora kowa kan hudubar tsiya ana wulakanta bayin Allahn

______________________________________

*Watani tara da kwana bakwai*
Chapter 136 · 0% Book details