← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 138

Sashe 84

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta sake wara manyan idannuwanta a saman bayan nasa daidai lokacin da ya juyo ya sauke dubansa a saman fuskarta

A nutse yana kallon fuskar tata da furucin dake karyata abinda yake son fada, domin ya dace furucin au fito a kausashe da ihu, sai dai gaba daya ya same su da sanyi a gareta yana kallon fuskarta ya ce" Ki yi kokari, ki koyi kilace kanki, ita mace daraja gareta, banzatar da kanta idan ta yi ba shine zai sa a ga kimarta ko a ga kyanta ba, ki kiyaye hulda da kowani namiji har ki samu yancin kanki....."

Ya karashe maganar, aman kuma fuskarta yake kallo sosai ya matse mata waje sosai

A hankali ta ringa hadiye dukan abinda take ji mai kama da tsoron jin furucinsa
Menene a ciki? Kar ta manta itama baban burinta bai fi ya sawake mata ba, da farko shi din ba zabinta bane, na biyu shine mutumen da ya wulakantata ya raba mata aurenta, na uku soja yake, wanda bata so ko a hanya su hadu da junna, so meye a ciki?

A hankali ta dan sakar masa sasaukan murmushi tana dan kawo hannunta dan ta tare kirjinsa domin ji take kamar kirjin nasa zai hade goshinta ne irin ya maki goshinta ne

A dan sanyaye ta furta" Ba damuwa........"

Daga haka ta juya ta nufi ciki wajen Mama dake zaune tana waya da yar uwarta tana sheda mata an rike iyayen matar MUHAY a asibiti tun jiya ta mata whatsup ta ga ta bude aman bata ce komai ba?,shine take ce mata ta kwontar da hankalinta yanzu haka ta kusa shigowa asibitin ta taho ai

A hankali ta zauna a gefen Maman tana lumshe idannuwanta

Baki ta tabe a kasan zuciyarta tana ayana' Irin gashi dan gwal din nan, to a kaina za'a fara ko a kaina za'a rufe? Dama me zan yi da namiji irinka?, Allah na tuba na dangana da masu nunan so ma bale mai nunan kiyaya? Kai zanma rokeka ka sakeni da wuri dan na samu wanda zai iya soyaya ba halaya na kiyaya ba!'

Shi kuma a lokacin da ta yi gaba da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa kafin ya samu kansa da jan wani dogon tsaki ya juya ya fita ya nufi hanyar da zai iya gannin likitan cen, ya kuka dakiki ne ashe? Ya nuna masa a jiya ashe bai gane ba? To ya bari idan ya saketa sai ya nemeta, aman a yanzu ta fi karfinsa walahi!, Baban abinda ya fi bashi haushi da yarinyar girman kai da nuna ita wata ce, to in takamarta kyau sai ta baza ido ta ga irin matan da ya ringa aura yana saki, dukawa suke yi har kasa sunna kukan ya dawo da su ya kiya, zata yi bayani ne!

Sai da Aban Shuwwa ya samu wajen da ya tabata akoy al'uma dake yawan kai kawo kafin ya iya samun nutsuwar fuskantarta yana murmushi ya ce" Bismillah me yake damun amaryar Muhammad ne?"

Dan murmushi Nahidt ta yi tana dan kawar da kanta dan har ga Allah ta ji kunyar abinda ya fada , sai dai ita bata so ya gane ta ji kunya dan haka sai ta juyo tana fuskantarsa ta ce" Aban Shuwwa a tunaninka a nan din ba zan iya rukunkumekan bane hala?"

Ido ya zarro yana dafe bakinsa ya yi gagawar fadin" Astagfrullah, subahannalah, yah Nahidt ya dace ki karra rike istigfari a dukkan motsinki, sannan ki guji aikata aikin da bashi da kyau komai kankantarsa, fisabililahi wannan aiki ai bashi da kyau, gashi ni azumima nake......"

Murmushi ta sake sakar masa ta gyada kai , kafin ta yi yannayi na hankakinta ba a kwonce ba ta ce" Muhammad, ka san wani abu? Abanmu anya ba ya haukace ba?, Ka ga jiya kafin likitoci su saka shi a cikin barci daga inda muke muke jiyo muryarsa yana ihun shi a fitar da shi daga kasar nan, subahannalah gaba daya tamkar ba mahaifinmu ba mutun mai nutsuwa da izza a jikinsa, mutun mai tarin kamala a tare da shi, a yanzu haka tun barcin nan basa bari ya yi doguwar farkawa domin da ya farka hakan yake ambata......" Ta karashe tana mai sadda kanta

Shima dan tsura mata ido ya yi kafin ya girgiza kansa ya ce" MUHYIDEEN ya ce yana tsantsamin sihiri, idan kuwa aikin sihiri ne in sha Allah zamu samu kansa kin ji? Ki kwontar da hankakinki zamu je na gani idan har sihiri ne ina mai tabatar maki in dai ba a zannen kadararsa ba Allah ya rubuta a cikin yannayin nan zai rayuwa har mutuwa, to fa nan da yan kwanaki zamu ga haske a lamarin, ki daina kukan haka kin ji?"

Kanta ta ringaa gyadawa tana sauke ajiyar zuciya

Shima ya sauke ajiyar zuciyar ya ce" Kin ga, da Malama da furerama suka ce a gaisheki"

Dan tsatsareshi da ido ta yi ta ce" Malan ina amsawa harda na fureran"

Dan kallonta ya yi kadan , sai kuma ya dauke idannuwansa a kanta ya nemi da ta sadashi da mutanen dake ciki, dan ya kula so ake a kure shi sosai, shi kuma in sha Allahu ba za'a kureshi ba yau din nan, kuma azuminsa da yardar Allah sai ya kai abinsa a cike cif
___________________________________

A lokacin da MUHAY ya fito da nashi kalar neman fitinar idannuwansa suka sauka a kan matar dake nufowa inda yake

Har ga Allah sai da gabansa ya fadi sakamakon ganninta a wajen nan, sannan zuciyarsa ta yi bakin kirin da ganninta

A hankali ya juya da niyar barin wajen dan ya cenza hanya, sai dai bai kai ga aiwatar da hakan ba ta yi murmushi tana kawar da makeken gilas din dake saman fuskarta wanda ya cinye rabin girman fuskar mai kalar duhu tana kallonsa da kyau ta ce" Ina zaka je?"

Dakatawa ya yi ya sauke numfashi dan ya daidaita kunar da zuciyarsa ke yi ya juya a saukake ya kalleta sau daya duba irin na ido cikin ido kafin ya ce" Hajia momy ce ke tafe?"

A hankali ta ringa ji ranta na baci da kiranta da sunnan momyn nan da yake yi, sai dai ba komai ta tabata jinkirinta zai zo karshe wata rana, dan haka itama sai dan murmusa masa tana sake binsa da kallon da ya fi tsana a duniya kafin ta ce" Nice kw tafe sweet men"

Baki ya tabe ya juya ya koma ba tare da ya ce da ita ta biyo shi ba, sai itace ta daga kafarta da dan sauri tana biye da shi tare da kallon askin kansa wanda sama sama ne aka aske masa , bakin gashinsa ya samu gyara na musaman sai walwali yake, har zuwa kunnensa da wuyansa

Dakin da Mama take ya tura a hankali ya shiga da salama a bakinsa

A yanzu SHUWWA na kwonce a saman bed din dake dakin, Mama kuwa tana zaunenta ne da carbinta a hannunta tana ja

Murmushi ya sakarwa Maman kafin ya wuce direct wajen da Shuwwa ke kwonce ya zauna a gefenta hakan ya sa ta dan janye kaffafuwanta sannan ta so juwaba barin da garun yake, sai dai dannewar da ya yiwa rigarta ya sa ta kasa aiwatar da hakan sai a haka ta tsaya

Shigowar ouseinarta ta sakata sakin murmushin da ya fito tun daga kasan zuciyarta mai cike da so da kauna harma ta mike daga zaunen da take fuskarta na idasa wadatuwa da farin ciki ta ce" Marhababuki yar uwatah......"

Ouseinarma wani sansanyan farin cikin ganninta ne ya mamaye zuciyarta, tsakani da Allah tama son yar uwarta so daya tak da babu hadi, baban matsalar da yake sakawa take karra yin nesa da ita shine soyayar da take yiwa yaronta mabambanciyar soyayar da ta dace ace tanai masa

Ita da kanta ta sani, ta san cewa abinda take ciki ba alkhairi bane, ta kuma san cewa lalle yaronai mutunci ne da ya kyaleta har yanzu bai tonata ba, aman kuma baban abin Tsoron bata jin Tsoron ya tona tan, ta gaji, ta gaji iya gajiya

Doguwar riga irin yar dubai din nan mai watsetaen stone tun daga sama har kasa wadda a kalla zata ci dubu casa'in ce a jikinta, sai dai dametan da ta yi ne ya saka yar uwarta bin rigar da kallo harma ta kasa hakura ta ce" Kanwa, wannan damamiyar shigar fa?"

Shigar tata ta bi da kallo , sannan ta juya wajen wanda ta yiwa din, abin takaici ko kallo bata ishe shi ba, uwa uba abinda ta gani a bayan wajen da ya zauna ya saka gabanta faduwa da sake zubawa wada ke koncen ido har sai da Mamma ta sake fadin" Haba Ouseina wannan ai ya dame da yawa, da ki hakura da ita ko kuma ki bada a bude maki, idan kuwa in tela ya taba lalacewa zata yi ki ringa saka mata baban hijab a sama, wanann ko a zaman gida bata dace da ke ba Kanwata"

"Zaki fara ko?, Ko zama fa ban yi ba ni yau kin fara kuma, wai wacece ke kwonce haka a bayan Baban yarona?" Ta fada tana mai son nufar Wajen da Shuwwa ke son mikewa dan ta gaisheta aman kuma ya wani danne mata rigarta ta kasa aiwatar da motsin kirki, shi kuma yana sane da dane rigar tata da ya yi, haka kawai yake ji a kasan ransa baya so ta yi mata irin abinda ta saba yiwa sauran matan da ya aura kafin ita

Muryarta cen ciki ta ce" Yalabai ka danen riga ka dagani na tashi......."

Kasancewar Mama ta juya tana fadin" Ina zuwa bara na ga ina Nahidt ta makale ne haka su zo su ci abinci, hakan na nufin ta fita a dakin da gano Nahidt ya saka shi juyowa da kyau ta yadda ya sauke idannuwansa a saman santaleliyar cinyar SHUWWA da take son ya dan daga ta janye rigarta
Chapter 84 · 0% Book details