Sashe 36
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MUHYIDEEN din kuwa da mamaki ya kalli CHIEF of army yana nuna Shuwwar dake daf da kafafuwansa muryarsa ciki ciki ya ce" Dama wannan ce ka aura min Dad ?"
Da hannayensa ya nuna wajen kansa alamun gyadi gyadi ya ce"Mahaukaciya ce fa, nd yarinyar nan du haduwar da na yi da ita sau biyu kadai na gane banda harkar aure auren maza ba abinda ta iya.....ni kuma meye hadina da mace irin wannan da bata da kishin kanta? Kuma ma Barauniya ce har kudin mutane take kwata, Lolz Dad me zan yi da bazawara wacce maza sukai ta dauka? Wannan ai zubar min da mutunci ne za'a yi a cikin kasar nan Father............... ka ga kawai ta je na......."
"Idan bakinka ya bude ka furta kalmar saki wa wannan yarinyar ka sani ka nuna min ni ba kowa bane kuma ba zan taba zama kowa ba a rayuwarka, domin da ace ELHAJ NE Allah ya jikan rai ya daura maka aure ko kafura ce zaka yi hakuri ka daidaitata har ta dawo ra zama musulma!, Idan har ka saki yarinyar nan MUHAY ka wulakantani kuma bana tunanin akoy abinda zai sanyaya min zuciyata dangane da kai har na koma ga ubangijina, idan har ka saketa dan kawai batai maka ba ko dan wani abin ya shiga tsakaninku da ya hadasa maku gaba ka wulakantani Muhay ka nuna min iyakata kuma ba zan taba yafe maka ba, Muhay idan ka saketa dan ta auri wasu kai din ba bazawarin bane? Nawa ka aura ka saka? Kennan sai a zageka da haka? MUHAY yarinyar nan ta zame maka mutu ka raba takalmin kaza!,, Mun gaji hakanan MUHAY, mun gaji, ao kake duniya ta idasa karda zargin da ake yi maka ne? Ko so kake mu shiga uku mu dawo abin nuni da baki? Meye yake yawo a kanka ne? Me kake son nunawa ne?, Kai mai daraja ne mai mutunci ne, jinnin mutunci ne, yaya zaka budi baki wannan karron ka yi saki irin na jahici bayan kana da ilimi?, I'm sorry my freind kana da damar sakinta ko barinta, aman ka sani idan har ka saketan hakan na nufin ni da bake takama da kai da bugun kirjina da kai ashe ni ba kowa bane ba kuma komai bane haukana ne nake yi a duniya ban sani ba?, MUHAY mahaifiyarka kuma zaka karra kuntata mata a kan sake saken da kake yi, Bismillah kana da damar sakintan bismillah" Father ya tari numfashinsa da sauri yana fada
A haukace ta juyo ta daga kanta dan ta matse masa wuri ta yadda dole sai ta yi hakan zata iya duban fuskarsa domin ya fita tsayi
Ido cikin ido suka kalli junna tana motsa bakinta tana masa alamun kamar wace ke furtawa kanta kalmar sakin haka kuma lokaci daya ta hade hannayenta a yau da bakinta ita SHUWWA dake neman aure ido rufe ne take furta "Furta, ka ga, manta maganar babanka ka yiwa girman Allah ka sakeni, ka furta dan darajar mai daraja a duniyarka"
Tsaf ya gama hardace abinda take fada
A hankali ya lumshe nauyayun idannuwansa yana sake yarda cewar she is md
ya sake budewa ya sauke a kan fuskokin mutanen dake falon baki dayansu har ya dawo kan fuskar SHIEF OF ARMY
Idannuwansa ya lumshe a kansa ya sake budewa a kansa a hankali cen kasan makoshi ya furta masa " Fine it's k "
Daga haka ya juya yana taku irin nasa na sauri mai cike da balaki da tashin hankali da bacin rai ya bar gidan kwata kwata yana tataro jama'arsa yana ayana 'yau zaku gayawa yan garinku tunda sai da na ce ban fito da kudin aure ba kuka hada akai min, daga ku har ita sai kun yi dana sanin sanina a rayuwa!'
Ihu ta kurma tana dukewa a wajen tana bubuga hannunta a kasa tana fadin" Wayo zai tafi bai tsinken tashin hankali ba, ku dawo da shi ya sake ni, wayo na shiga uku na rantse sai ka sake ni, kai waye ya aura min shi? Waye ya aura min soja? Waye ya aura min wannan? Walahi da na tare da shi gwara yara su maida ni biri a kula min igiya ana wasa da ni a titi, da na aureshi gwara na auri Abdul dan mai shinkafa, kai da na aureshi gwara na zauna a haka shine alkhairina, wayo sun kasheni , idan ka yarda na tare a gidanka sai na halaka farin cikinka, sai na wulakanta zaman lafiyarka sai na???????....". Firgitttt ta mike zata kuma saka wani ihun sai kuma lluuuuuuuuuu ta tafi sakamakon sumewar da ta yi numfashinta ya dauke gaba daya ta dimu a kasa kusa da cafet
Sallalamin dake bakin baban Hamza ne ya samu ya fara ambata, hakama CHIEF OF ARMY
NAHIDT ta sauke ajiyar Zuciya tana fadin" Allah ya takaita rigimar, yanzu bara mu samu mu kaita wajen da idan ta farka za'a samu sasauci, MUHAMMAD ina zamu kaita ne?"
Sai da gabansa ya fadi da ta wani ce Muhammad kai tsaye hankalinta kwonce kamar wani d'anta , shi walahi tsabar girmama shi da mutan anguwa suke sunna boye sunnansa da matansa ya sa idan ya ju an ambaci sunnansa kai tsaye har gabansa ke yankewa ya fadi
CHIEF OF ARMY kam Shima sai ya farra tunanin to ko dai bata da lafiyar kwakwaluwar ne?
A sanyaye ya furta" Ya salam, Elhaj anya bamu yi gagawa mukaa yanke hukunci wa yarinyar nan ba tare da mun tuntubeta ba? Ni na dauka farin ciki zata yi da Allah ya bata Son, ka ga hankalinta ya tashi harda sumewa ko dai na maido shi na janye masa magangannun da na masa a kan maganar sakinta ya saketa ko zata samu nutsuwa?"
Da sauri Malan da ya gama kiran likitar dake duba matansa ya ajiye wayar yana fuskantarsu a nutse ya ce" Aa ranka shi dade ba za'a yi haka ba, dan Allah a yi min alfarma a barmata aurenta a kanta, ni na san idan ita wuta ce shi ruwan kashe wuta ne, na tabata zasu zauna da junnansu, kar a kashe auren nan dan ta tada bali, a basu dama idan har basu jitu da junna ba zuwa gaba sai a raba auren, ka san wancen sakin da akai mata dan ya saka an kaisu ofishinsa ne ya sa aka saketa shi yasa ta kulace shi"
Su kam sun ga abu, sun ga mamaki gannin idannuwansu sun kuma kamu da mamakinta har karshen rayuwarsu, ta yadda ta cira din nan nufinta me ta so aikatawa? Kai da wani lusarinema da ta kai masa walahi, anya kuwa zamansu zai yiwu?
Gogonsu ce a sanyaye ta ce" Malan, da Abansu, da Elhaj dan Allah ina so a bani yaren nan mu je gida na basu kulawa koda ta ta sati daya ce , dangi su gansu, a fadawa dangi ga iyalin TINANA , sannan a saki sanarwar nemansu, ni na kasa yarda cewar sun mutu, yaya kuma yaya maganar sunnan nan?"
Wani kakausan kallon da ya watsa mata dake nuni da baya so a taso maganar sunnan mahaifin su Shuwwar ya sakata yin gum da bakinta
Watau gaba daya abin ya rudar masa da kansa
Ta so su je kai tsaye gidan sarautar garin nan da yan matan wani tunani ya darsun masa a zuciyarsa wanda ya barawa kansa sai Allah , so yake ya bi komai a ilimance ta yadda zai warware kullin da ya daure masa kai a kan lamarin nan, ya tabata wanda ya yi sanadiyar barin babansu kasar nan koma waye yana bibiye da rayuwarsu ne kuma in sha Allah sai ya gane abinda yake binne!
Zigum zigum dai suke, gogonsu bata samu amsar bukatar da ta gabatar ba domin kowa cikin mazan nan yana da kalar nasa tunanin a kan hargitsin da ya hanga dangane da rikicin zamantakewar MUHYIDEEN da SHUWWA, sunna nan du hankalinsu tashe har likitar ta zo
Ta dubata sosai, ta yi mata dabarun da zasu dawo da ita cikin hayacinta, sai dai tana farkawar da wata rigimar ta farka ido rufe tana fadin" Haba dan Allah, Aba, Aba ka gani kau? Hala shi Aalkalamin kadarar tawa da ake fadi bashi da lafia ne? Ya tashi ya rasa inda zai zana ni yau kuma sai aure da kumurci?, Gwara ya gane rayuwa ya sakeni, domin zama da ni babu alkhairi, ya sakeni na ce!"
Da dan sauri NAHIDT ta karasa kusa da Malan sosai ta yadda sai da ya dago idannuwansa a tausashe yana kallonta ya dan katsa kadan ,
Ita dai bata damu ba ta yar uwarta take ta rage muryarta sosai ta ce" Ka saka a maka mata wata allurar barci mana kar fa uban mijin nata ya saka a saketa dan bata da hankali, kai ka san hankalinta ne a tashe idan ta farka ka totofeta da adu'a ka mata nasiha zata nutsu ai ka sani ko? Kar ka bari a sakar maka y'a Shuwwa zafa ta rikice ta fara halaya mararsa kyau fa"
Ajiyar zuciya ya sauke kawai ya sake matsawa kusa da likitar a tausashe shima ya yi mata bayana, ai kam ta ce" Ai nima Ustaz abinda nake ta tunani kennan domin jinninta hawa yake yi, gwara a bata nutsuwa ta samu isashen barci, bara nai mata allurar barci Allah ya sa na zo da jakana"
A haka aka samu akai mata Hamza na rike da ita tana dan fuzge fuzge da kyar aka samu ta yi lakwas ta kwonta jikinta ya saki sai barci yaa dauketa
Ajiyar zuciya du suke saukewa sunna kallon kyakyawar fuskarta mai alamu da innocent face, kamar idan ka saka yatsarka a bakin Shuwwa ba zata ciza ba, gashin kanta kuwa ya yi mata lumbuk a gaban goshinta , lebenta yaa sake yin ja sai kyalkyali yake yi na abin dan tawun samman lebenta da take cijewa a ciki alamun rigima na cinta iya ci