← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 138

Sashe 106

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyarsa da ta yi baya baya a hankali ta rike garun dakin ta sake zuba masa ido, sannan ta zubawa matar nan dake kwonce ido, kafin ta lumshe idannuwanta hawayen da take ta sharewa na tausayinta tun dazun wasu suka sake zubo mata masu daci sosai sai kuma ta rike hannun Tinana da ta sake rike hannunta a hankali ta shiga bin bayanta suka fice a dakin kwata kwata suka fice a wajen har suka hade da y'ayanta mata da suka yi zuru zuru an hanna su shiga wajen , Suka wuce su ba tare da sun iya kula tambayoyinsu a kan jikin mahaifiyarsu ba, ya rage sauran mace daya da kuma su Dad, wace itama ta sauke ajiyar zuciya ta girgiza kanta ta juya ta wuce a dakin tana tunanin tabas son zuciya da rashin godiyar Allah sun kai matar nan sun barota , hakan ya rage daga Dad sai Sultan, sai Muhyideen da ya ki sakin bakin nata

Da karfi Dad ya shamace shi ya warce hannunsa a saman bakinta, kamar jira take ta dora da fadin" Ke kuma Salma yadda na haife ki da cikina aman kike juya min baya a kan kudirina da shirina na son kashe dan iskan yaron nan ba damuwa, ai gari da yawa maye ba zai ci kansa ba, da kudina a jakata na tabata zan janyo da yawa da zasu kama min, sai na ga an fita da gawarsa a makara a wulakance zan samu nutsuwar zuciyata, mijina na ni kadai ne sai ko y'ayana, du wanda ya ratso duniyata da mijina sai ya shiga uku wannan alkawarina ne!, Sannan da mijinki ke maganar karra aure ki sani ba zan taba bari a maki kishiya ba, yar iska mai zuciyar mahaukata da baki san ciwon kanki ba bale na uwarki! Ana wulakantani kina nanuke da su ke ga ta kirki ko? In dai mutun ne mugun ice ne,, su ji suke tamkar ki mutu su karra yawon kudin gadon ubanki a kanki............., Ita kuma uwar Uma itama sai na................"

Bakin ya sake damkewa bayan ya bi Father da kallon tausayi yana girgiza kansa ya waiga gannin Aban Shuwwa na kokarin barin dakin a birkice ya ce" Sultan "
Wani irin birki mahaifin Shuwwa ya ja ya juyo da sauri yana kallon bayan MUHYIDEEN

MUHYIDEEN ya sake tausasa kalamansa ya furta" Aikinka ne hanna yaduwar fitina ko wace iri ce Abah, ka taimaka ka shiga a matsayin da Allah ya nadaka a kai ba wani dan adam ba, kana da ruwa da tsaki a ciki a matsayinka da Allah ne ya baka, ka dube mu ka kama Abahna, ka kwatanta masa cewar wannan din ba komai bane ba, karma ya daga hankalinsa a irin wannan, Allah ne ya kadara masa haka , wannan al'amari a rubuce yake tun kafin a halicemu, Dan Allah kar ya rikita lafiyarsa ko ya saka a ransa ta yadda zan rasa wani uban a karro na biyu, ya sani wannan din sirrinmu ne na cikin gidanmu, dama ba lale kowa ya zama yadda ake so ba, fatana wannan din shine na karshe a wajenta, Abah ka fada masa bani da karfin fuskantar wani hargitsin bayan wanda na bari a dakina da kuma wanda na tarar din nan a irin wannan lokacin, Aba bani da karfin iya jure haka a irin wannan lokacin Abah....... ba zan iya ba Abah....................." Ya karashe a matukar raunane yana sake kallon yadda take dago kirjinta da karfi tana mayarwa a jigace haka kuma so take ya sakar mata bakin ta idasa tonawa kanta dukan asirin dake ajiye saman zuciyarta wanda ya hadasa mata nauyin zuciya sosai ya hanna mata sukuni take kwana take tashi da shi ( Astgfrullah wa atubu ilaiki )

A hankali ya karra sada kansa yana ta tofa mata adu'a, tun tana yi karfi da yaji har muryarta ta disashe ta dawo yi a hankali , kafin ta yi shiru idannuwanta rintse, watau barci ya yi awon gaba da ita
Sai da ta yi barcin nan ne sannan likitocin suka shigo aka shiga jona mata magungunnan du da suka dace da ita domin dama sai abin ya lafa ake jonawar

Ya jima zaune yana kallonta da tunanin yanzun da mahaifiyarsa ce, ko shi kansa ne haka ta faru da shi da yaya zai yi da ransa?, Tabas yana bukatar uzuri haka zai so a yiwa mahaifiyarsa uzuri, zai so koda a kan son zuciya haka ta same shi a yafe masa, shi yasa tunda ya fuskanta ya kuma gane cewar itace ya watsar da dukan kudirinsa na son sai ya yi fito na fito da ita, sannan ya yi ta rokon Allah kar Allah ya bata damar idasa saka rayuwarta a uku ta hanyar samun rayuwarsa, ya yi ta faman nema mata sasauci a wajen ubangijinta, babanma abinda ya bata masa rai shine saka camera a cikin dakin iyalinsa wanda ya gano hakam ya faru ne da hadin baki da taimakon biyu daga cikin yarensa dake gyara masa gida kafin aljanarsa ta dakatar da su suka saka camerar, na bangarensa kuwa lokacin da aka saka masa yana sane, ya dai lalata abin ne ba tare da sun ankara ba, sannan ya yi anfani da damarsu dan ya tantance wace mace ce zata iya zama da shi ba tare da ta nemi rayuwarsa ba komai mugun halin da zai nuna mata a gareta?, A haka suka ringa cin galaba a kan matan da ya ringa jerawa suka mayar da shi tamkar wani dan tasha yau ya dauka gobe ya saki da ita da muryar y'arta wace daga baya ya gane cewar ai itace dayar muryar dake yiwa matan da zai aura barazanar kashe su a kansa, har suka fado kan Aljanarsa da yayunta mahaukata suka rawaito masu ashariya daki daki, daga nan sai suka barta suke bibiyarta da son samun hoton tsiraicinta dan su yi mata anfani da shi, shi yasa ya faukota ya dawo da ita nan domin haka kawai yake ji a cen kasan zuciyarsa idan suka ga tsiraicinta ya wulakanta ba zai iya dauka ba

A hankali ya mike bayan ta shiga barci ya fita a dakin
Ya zo ficewa ya hade da y'artata mai dafe mata baya
Bai yi wata wata ba ya damketa ya dawo da ita dakin da dayar dake biye da su tana zarro ido a tsorace
Da garun dake dakin ya makata ta hanyar hankadata har sai da ta daku da garun a tsorace ta zube kasa tana zazaro ido da kallonsa

A kausashe ya ce" Ruwanki ne ki ci gaba da wulakantar da kanki, ruwanki ne ki yi biyaya ki cenza halayanki, abinda nake so da ke shine ki sake gigin shiga hurumina, a nan ne zan baki mamaki domin ke hargagin karya kike cewar zaki kashe a kaina, ke burga kika iya a kan kowace magana, ki yi komai banda iyalina....dan ni kaina ban gama tantance abinda nake iya aikatawa a kan iyalina ba!"

Daga haka ya fice a dakin ya je wajen doctern da yake sheda masa ai an koma da iyayensa gida, Father ne ya ce su wuce gida gaba dayansu
Shi dai bai iya aikata komai ba sai barin salahun su kula da marar lafiyar ya yi ya bi bayan iyayen nasa

____________________________________

Tabas Father ya gigice da jin wannan lamari, ya tsorata da duniya da abinda ke cikinta
Da idannuwansa ya yi hawaye mai zafin gaske, ya birkice ya nemi zaucewa, sai dai wace aka fi cutarwa a lamarin bayan ta samu ban baki da nasiha sosai a wajen mahaifiyar Shuwwa sai ta same shi ta nuna masa cewar wannan din ba wani abun bane da ya zarce aikin shedan, ta nuna masa ita ta yafe ta kuma fodewa Allah da abin bai girmama ba, sannan SUKTAN da ya bashi dama ya yi kukansa sosai sai da ya gama ya fuskanceshi ya sanyayar da muryarsa sosai ya ringa tausarsa ta hanyar nuna masa rayuwa da abinda ke cikinta, girman kadara da ladan juriya a haka, ya nuna masa sam kar yace zai yi mumunar magana ya yi mata fatan shiryuwa, dan Adam yanzun abin tsoro ne, tabas dan Adam abin tsoro

Sunna tsaka da haka ya dawo ya same su a bangaren Aban,

Tunda ya shigo SULTAN ya sake kafe shi da ido yana tuna furucin da ya yi a dazu na kiransa da sultan da kuma nuni da ya yi cewar Allah ne ya nada masa abinda yake da hurumi a lamarin kowa, hakan ya sa yake kallonsa ko a yanzun harma ya gaishe shi bai gane ba sai da matarsa da ta cika da mamaki ta sake tabo kafarsa tana nuna masa ana gaishe shine ya ankara harma ya farka a doguwar sumar ko nace kashangar din da ya yi yana mai kallon sojan mijin y'ar tasa da kallon mamaki

Shima ya kula da irin kallon da yake yi masa, sai dia bai nuna ba ya karasa gaban Dad da mama dake zaune sunna binsa da kallo

Dad ya lumshe idannuwansa hawaye na zuba a gurbinsu ya ce" Da na san makashinka yana tare da ni , da ban yarfa an kai yanzu ana wulakantamin kai ba, da na san............"

"Aba...." muhay Ya fada a sanyaye yana katse maganarsa
A hankali ya dora da fadin" Wannan din sirrin cikin gidanmu ne, da ya faru a tsakaninmu ne, kuma ba yau ba na yafe mata , sanadiyarta har na gama samun wace............a sanadiyarta har na samu abinda bana tunanin yana samuwa da gagawa a cikin duniyar nan tamu ta yanzu, dan Allah na roke ka, ka yi hakuri ka dubamu dake zagaye da kai, kar ka bari wannan ya daga maka hankali, ka hori matarka son ranka dan gobe kar ta Kuma, aman kuma ba maganar saki ko wulakantarwa domin Allah ya saka albarka a tsakaninku, Abana baka isa ka hanna abinda Allah ya hukunta min ba, inaga farin ciki ya dace ka yi da abin ya zo da sauki ko?"
Chapter 106 · 0% Book details