← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 138

Sashe 111

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki ta kalli daga dakin da ya fito , hakan ya sa ta ce" dama akoy hanyar dake sada wani dakin da wani ne?"

Kin bata amsa ya yi yana yi mata kallon da zata iya fasarashi da harare, hakan ya sa ta mike tana fadin" Mu je dai in gani "

Gaba ta yi ya bi bayanta , haka kawai idannuwansa suka sauka a bayanta dake juyi kamar wace ke yin hakan da gaya, yana biye da itan idannuwansa kyam a saman bayanta har ya zo gam ya hade da garu ba tare da ya san ya karaso wajen ba kuma a daidai garun yake tafia ba
Kasancewar abin ya zo masa a ba zata dole ya yi saurin dora hannunsa a goshinsa yana furta" aushhhhhh"

Turus ta yi ta juyo da sauri dan gannin abinda ya saka shi yin Aushhh, sai dai tana juyowa ya yi gagawar ajiye hannunsa yana matse fuska irin ga jarumin nan, hakan ya sa ta bi kirjinsa da kallo da hannunsa har ta sauke dubanta a kan hannunsa na dama da ya jimke, wanda ke nuna alamun ya daku fa

Bakinta ta dan tabe kadan da dan baya baya ta fara idasa shigewa dakin , sai dai me itama tana shiga ta harde da dogon wandon da ya cire ya yar a nan kan kofar dakinta hakan ya sa sai da ta yi tangal tangal kafin ta diba duwawu a kasa

Dan kara ta saki tana dafe kugu hadi da kallon abinda ya yarda ita
Da wani takaici ta dago dubanta ta sauke a kansa domin sai ta kula kamar wanda yake murmushi a saman lebensa, sai dai sunna yin ido hudun sai ya sauke idannuwansa kasa wajen wandon yana kallon wandon hadi da dan cicije lebensa na kasan

Da takaici ta bi dakin da kallo, ai kam ta ga gajeran a yashe a nan kusa da gadonta, gadon da ta yiwa gyara na kasa da kasa, tunda ta gyara shi fa tana son shiga ta kwonta aman idan ta tuna shinfidar da ta malala masa sai ta ji cewar gaskiya tsaftar jikinta ba zata hau gadon ba, watau gadon ya sakata maka masa shinfidar yan gayu irin ta sarakai , shinfidar da ta rantse da ubangijin talikai ta dauki kusan minti ashirin tana yinta, shine ya tako ya cire mata dan kampai ya yar mata a gaban gadonta sannan ya cire safar kafafuwansa da ya tako datin kasar da ya fito da na anguwanni ya dora mata a saman shinfidarta ita?, Uwa uba abinda ya fi kona mata zuciya ashe takalmin dake kafarsa da shi ya shigo mata daki? Oh no wannan daya, ba zata dauki wannan ba gaskiya
Hakan ya sa ta dago yar yatsarta ta yi kalar balbalin balaki sannan ta shiga fadin" Saurara malan saurara, ba zai yiwu ba gaskiya, a gidan nan za'a zo ne a dauki byro da takarda a ware abinda ake iya yi na yi hakuri da wanda idan aka yi lalle lalle za'a iya tono abin bacin raina, ka ga yarda gajeran wando a ko'ina ba tsafta bane, kazanta ce tukuru mai lasisin tsiya, idan ka cire yabadaibadai dinka kaimin bayi ajiye min idan na shiga zan wanke na shanya, bale ka ga ba zan dauki a cikin gidana a ringa shigo min da takalmi ba, lallalalalalaalalalalala, sannan a dakina a zo min a ari tawul dina kuma a karashe da ajiye min safa a saman bed? Shinfidar nan ai kana gani ka san na wahala wajen yinta, to shi musulmin kirki ba an ce ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa ba?, Wannan lamari sam ban ji dadinsa ba, kar a kuma ina dalili ina dan mafari ne........?"
Ta karashe tana sake kallo fuskarsa, domin tunda ta fara magangannun nununawa ne take yi tana jujuyawa ta yadda zata masa gwari gwari ya gane da kyau ya kuma kiyaye, sai da ta ajiye maganar tata ne sukai ido hudu, ido hudun da ya so tuna mata cewar a maganar da ta yi fa kamar shine mai gidan, yama taba fada mata cewar ta daina cewa gidansa gidanta dan ba gidanta bane, sai gashi yau ta ce gidan nan nata ne,
Ido ta kikifta tana shagwabe fuska irin na jariri dan shagwaba, hakan ya saka shi saurin nunota da yatsa ya ce" Kar ki saki, kar ki saki ki min kallon nan dan ko kin yi sai na fada maki!"

Bakin ta idasa shagwabewa hakan ya saka shi zubawa fuskar tata ido yana kallonta har na tsayin minti daya da sekwani kafin ya sake gimshe fuskarsa yana fadin" Ba zai yiwu da gidana ace za'a bani karamin daki maimakun wannan, sannan da kike cewa wandona ni dan kampai ba dan kampai bane ba!, Kuma yanzu na fara cire wando na yar a inda na ga dama ai ban ce ki dauken abina ba! Ke ke tsayama ki ji......."
Sai kuma ya yi tsittt kamar redio ce ke yi kuma aka kashe, da sauri ya sake kallonta sannan ya kalli kansa, wani iri ya ji na kunya na son lulubeshi da takaicin kansa, yanzu wannan yar kucik din yarinyar ce ya tsaya yake kirtawa kashedi? Wannan har jaririyar ce ya yiwa kashedi?

Juyawa ya yi yana tafiyar nan ta gagawa sanann wace ake jefa kafa hakan ya sa ta bi bayansa da kallo har ya bacewa ganninta kafin ta sauke nanauyan ajiyar zuciya ta janye wandin daga kafafuwanta ta mike ta karasa ta duka ta dauke gajeran ta nufi bayinta a bayane tana fadin" Gidana ne ba naki ba....yenyenyenyen, gidana ne ba naka ba malan, sai ka daukeni daga nan din na gani mana!"

Ko da dare ya yi bayan ya dawo daga sallar isha'i ya gama salama da masu gadi ya shigo falon ya samu falon ba kowa , hakan ya sa ya nufi dakinsa yana cire doguwar rigarsa hadi da shafa cikinsa yana jinsa a cike har yanzun domin dazu ya shaki girkin da ya tarar sosai, ya ci girkin nan sosai da sosai har sai da ya ji zai yi amai, a gaskiya ya san yarinyar koda ba hankali akoy iya girki

Yana bude dakin ya ji wani sabon kanshin turaran wutar mai dadi
A hankali ya samu kansa da sakin lalausan murmushi yana kunna fitilar dakin, domin kanshin ya masa dadi a hancinsa

Idannuwansa yake warawa sosai a saman kanta
A kwonce take saman gadonsa ta dukunkunne ga dukan alamu barci ta fara

Idannuwansa ya kankance ya nufi gadon ya saka hannunsa yana jan bargon hadi da fadin" Ke ke sauko min a gado meye haka?"

A zabure ta farka tana kallonsa, sai kuma ta rintse ido tana sakin dan karamin kukan tabara ta ce" Walahi na gwada kwana a dakina ba zan iya ba, tsoratani ake yi har ce kin ake yi wai ke fita, ka ga ban saba kwana ni kadai ba domin tsoratani ake yi ......."

Ido ya sake zuba mata yana tunanin shin me ya aikata na laifi da horonsa ya kasance da wannan yarinyar ne? Hasbunnalahu wani'imal wakim shi kam yaya zai yi da yarinyar nan ne? Ya san ai tana da aljannu aman kuma har su hannata kwana ita kadai yanzun a dakinsa zata kwanan masa ne? A yana kwana davan dabanma yaya suka karata balle a sunna barci daki daya?

Bargon ya idasa janyewa ya sauke shi kasa ya shinfida da kansa sannan ya dauki matashin kai ya jefa sama da idannuwansa ya mata nunin ta sauka kasan

Shinfidar ta hanga , ta kuma kalle shi, wai tsakaninsa da Allah kasa zai sauketa ne?

Gannin yadda ya tsaya mata kerere ya sakata ziro kafafuwanta tana jan dogon wandonta mai santsi ta sauke kafafuwan nata kasa tana sake binsa da maraitacen kallo irin na a ji tausayin mutun din nan, har ta idasa sauka yana tsaye yana kallonta ta hau saman shinfidar tana kallonsa shi kuma ya ka ya haye saman gadon yana sake hade fuska da tunanin haka kawai ya gaji za'a wani hau masa gadonsa shi a hada shi da kwonciyar kasa?

Tana kallon ikon Allah ya yi kwoncinsa yana bata baya hadi da jan dan karamin tsaki ya yi takuraren kwonci kafin ta yi zuru zuru tana tunanin kwonciya a kasan nan , ba dan komai ba sai dan sanyin da ta tabata sai ya kusan halakata

Tana zaunen nan har ta kusan minti talatin, kuma shi kuma tunda ya yi kwoncin nan bai motsa ba, asalima rigarsa ya maida tunda ya ganta a kwonce a saman gadonsa, kar tai masa kallon nan da take masa kamar ta ga kwarto (🙄)

A hankali ta cire ribom din kanta tana tunanin yadda za'a yi ya sauka daga gadon nan ita ta haye

A hankali ta barbaza gashin kam nata sannan ta koma ta kwonta

Ai kam sanyin ne ya fara ratsata da gasken gaske, gashi kayan barcin nata riga da wando ne sakaku masu santsi ba masu kauri ba, hakan ya sa suka lalafe mata da sakata rawar dari

A hankali ta aniya fitar da nishin da gangan tana gantsarewa
Sai ta ja iska sai ta saki nishi mai karfin gaske hadi da yar shashekar kukan da gangan tamkar tana cikin barcin nan, sai ta juya kwoncinta ta kaiwa gadon duka da kafarta har sai ya bada dan sauki dam sai ta janye ta dukunkune

Ido yake karra rintsewa yana rige abin rufar dan kar ta saka shi a uku, aman sai da ta gama fahimtar da shi cewa ita din tashin hankalinsa ce, idan kuma ya hadu da ita ko ma second daya ne sai ta birkita masa lisafi bayan babu abinda yai mata? Ita bata san hakin dan Adam da ake kiyayewa bane?

Da karfi ya mike zaune yana sasautowa yana kallonta
Irin yadda take abin kamar wace take bori,
Sai kuma ya ji tausayinta ya tsirga masa a zuciya, sai ya ji yana neman yiwa kansa fada kan ya fa ringa yiwa yarinyar nan uzuri duba da wani abin aljannu na iya sakata aikatawa

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya sauko ya duka ya cicibeta, hakan ya sa ta bude idannuwanta a zabure gabanta na kwonci kwonci ya fadi ta yi kiri kiri
Chapter 111 · 0% Book details