← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 138

Sashe 125

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannan hudubar ta fice ta nufi bangarensa, a lokacin da ya shigo din kennan shima bayan sun gama salamar bakin da suka yiwa Nahidt din rakiya harma ya yarda da maganar cewa masu yi mata hidima zasu zo nan da sati guda idan an gama tantance wa'inda suka dace a kawo mata in sha Allah

Tunda ya shigo falon da lalausar salamarsa yannayin gudun jinninsa ya fara cenzawa

A hankali ya ringa amsa gaisuwar Malama dake masa da murmushi kwonce a saman fuskarta, sai kuma ya juya bangaren da Nahidht din take wanda yake ta son kallo tun zuwansa aman ya hanna kansa dan yiwa mai adalci adalci

Idannuwansu ne suka sarke da junna, sai kuma ta yi saurin sada kanta hakan ya sa farar alkyabar dake jikinta sake sadowa ta sake tare gaban goshinta

Dan Murmushi ya sauke na fahimtar kamar wace take jin kunyar hada ido da shi ko menene? Sai kuma ya girgiza kansa yana ayana' Ba dai Yayar Y'ata ba, idan ta ga dama Yanzu ne zata ce min Muhamadu kamar wata gwogwona'

Shigowarta da doka kofar da ta yi ya saka shi waigawa da dan sauri ya zuba mata ido

Salama ta yi ciki ciki, haka kuma jikinta daga ita sai dan kwalin nan da ta yiwa dauri irin na birkitatun yan barikin nan tana taunar cingam, kana gannin yannayinta ta aro lamari ne irin na fitinanun mararsa jin magana irin wa'inda barikin bata karbe su ba suke mata cin karfi da yaji, watau mararsa nutsuwa a barikinma, irin masu ja da karfi da son nuna su din yan duniya ne ta kowani hali

A kujerar da ya dace ya zauna ta karasa ta zauna sannan ta dora kafa daya kan daya tana taunar cingan hadi da yin kas kas kas da cingan din

Har ga Allah ta ba Nahidt dariya, ta ba Malama tausayi, ta kuma ba Aban Shuwwa mamaki da tunanin ita kuma nata salon kishin haka ya sakata dawowa? Subahannalah a haka ta fito dan rashin sannin ciwon kai ta zo har bangarensa? Duda gidansa ba gida bane dake cike da maza, aman ko dan shedanun aljannu ai zaka kamanta rufe jikinka, bale masu aikinsu mata dake yi masu aiki sunna girmama su har sukan duka har kasa su gaishe su da kiransu malamansu, me take son nunawa a haka?

Ajiyar zuciya ya sauke, da yannayinsa na sanyi ya kai zaune a saman kujerar dake gefen ta Malama wace kuma take facing din su biyun

Sake zuba masu ido ya yi d💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 7️⃣2️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Ajiyar Zuciya ya sauke, da yannayinsa na sanyi ya kai zaune a saman kujerar dake gefen ta Malama wace kuma take facing din su biyun

Sake zuba masu ido ya yi daya bayan daya kafin ya yi dan gyaran murya a tausashe ya furta" Asalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu yah ku iyalaina"

A ciki Malama ce kawai muryarta ta bayana a tausashen itama, Nahidht kam ta amsa aman a saman lebenta haka kuma a zuciyarta ta ayana' Toh fa Allah ya kawo mu'
Inda Furera ta tabe baki tana ayana' Namiji munafuki algungumi macuci!'

Sake gyara zamansa ya yi ya ci gaba da fadin" Alhmdulilah, kamar yadda kuka sani harma kuka kasance sheda ga wannan rana, yau ta kasance rana ta farin ciki a garemu baki daya, ranar da Allah ya nuna min na sake kamanta sunnar ma'aiki ta hanyar karro maku yar uwa, abokiyar zama, wace nake fata da adu'ar Allah ya sa zamanku ya kasance alkhairi a garemu baki daya, koda da halin karro wata na cikashe hudun ya zamto ta tarda gidana irin gidan da ake koyi da halayan matan shugaban halita annabi muhamadu sallalahu alaihi wa salam, ta yadda sai dai ta zamto cikashin farin cikina in sha Allahu rabih"

A yanzun kam ido cikin ido Nahidt ta dube shi da duba irin na ka fa fara isata, ko ka fa fara kauce hanyar nan, wanda sunna yin ido hudu sai da ya boye murmushinsa domin karara ya gane tabin fadan da ya yi ya karbu ta yiwuma ya samu amsa wa martani a kusa kusa, sai kuma ya idasa da kallon Uwar gidansa wace ta yi murmushi ta sada kanta a nutse ta furta" Allah ya doraka a kan hanyar farin cikinka Yah Ustazzzzz"
Wani tsadaden murmushi ya sauke mata yana sake gannin girmanta a kasan zuciyarsa
A kasan zuciyar Nahidt kuwa fadi take' Kan balaki, Allah ka sa matar nan ba kililin kasau take min ba, wannan gaskiya itace kishi da ita Balaki ne, gwara ka fafata da mahaukaciyar nan da irin su uwar gidan Malan, yo fisabililahi ni kaina matar girmamata nake a zuciyata bale kuma mijinta, kai jama'a Allah ka saka mu a damshin malamar Aban shuwwa, ka bamu hali irin nata'

Furera kam Allah kadai ya san irin zagin da ta rawaito a yau a cikin zuciyarta ta kuma auna shi kan mai uwa da wabi, ba ogan bale makarabansa

Sake muzgutawa ya yi yana fadin" Hajia, da Furera Ga Nahidht, Nahidt ga Hajia da kuma firera, zan so ku yi zama na adalci a tsakaninku, ku kyautata kyautatawa junna sai ku ga Allah ya baku ikon kare hakin dan uwanku harma da ni kan kaina, ina fatan zan samu haka a wajenku?"

Tsakin da take ta rikewa ne ya bale daga bakinta, ta kuwa ja shi da karfin balakin da ya saka suka sake dubanta gaba dayansu
Da sauri Malama ta dauke maganar da fadin" In sha Allah ya ustaz, Allah ya bamu ikon fin karfin zuciyarmu alfarmar annabi da alkur'ani"

A dole ya janye dubansa a kan Furera ya lumshe idannuwansa yana hadiye abinda take son hadasa masa, watau bacin rai, hakan ya sake kunnata da kona mata zuciya
To a kan me zata zauna a mayar da ita kamar wata banza a waje ?

Shi kuma sai ya sake karkatawa garesu yana tuna ranar da aka kawo furerar, a ranar ita da kanta ta yanke cewa zasunna yin kwana bibiyu ne a gidan, da kanta ta ringa amsa adu'o'in nan tana ta rawar kai duda ya daukota ne a matsayin budurwa, sam a ranar bai fuskanci irin haka daga uwar gidansa ba, hasalima sai da ya je yi mata sai da safe ya samu kamar Idannuwanta sun yi ja, a nan ya gane cewa lalle Malama na sonsa irin son da ta kasa hanna shi son wani abin bayanta, harma ta taimaka masa, ta kuma yi da zuciya daya, a ranar sai da yaa dade yana rarashinta har ta dawo kyakyata daria kafin ya bar dakinta, sai ga yau gashi gaban sabon salo, wai shine har furera ta manta kalar horon da yake mata a gado take masa tsaki?
Dan murmushi ya saki na gefen baki yana ayana' zaki yi bayani ne'
A bayane kuwa sai ya sake fadin" Yaya kuka tsara sabuwar tafiyarmu ne? Zaku jone da kwana bibiyun da kuke yi kamar na da ko zaku cenza ne?"

Malama ta dan watsa hannayenta ta ce" Ai bibiyu ya fi Malan, ka ga ya fi bamu dama haka kaima, shi fa'idar kwanaki bibiyun inaga kowa ya fahimce shi a nan, a lokacin da furera ta yanke shi har na yi mamakin bibiyu bai yi nisa ba? Aman daga baya sai na fuskanci bibiyun nan shine cikon nutsuwata, inaga ni dai daga wajena in sha Allah bibiyun ya yi min, da zarar Amaryarmu ta fita a kwanakinta na amarci sai mu jone da bibiyu ko yaya kika ce amarya?"

Tunda aka fara fara maganar Furerar bata ce komai ba sai fuzge fuzgenta da take da tsakinta, aman a Yanzu sai gata ta budi baki da yatsina tana kallon uwar gidan malan ta ce" Ban fahimci zaki yi magana ki tambayi bakuwar da kika ganni yau a gidanmu ba Hajia ko har hade min kai ne za'a yi tun yanzu a fara hura min wuta ne?, Bayan wannan wasu kwanakin amarcin kike nufi? Kar dai ki ce min kwana bakwai irin na budurwa bayan kin san, na san, ya san a hangame take tamkar kifar gari? Ko salon cin amana ne............?"
Chapter 125 · 0% Book details