← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 138

Sashe 65

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malan ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai a nutse ya ce" kina jina?, Ina so ki fuskanceni da kyau sannan ki fahimci abinda nake son fada maki, SHUWWAR ko wanene, ko me yake tare da shi ina so ke ki zamto wace zata gagaresu da karfin adu'a fa gujewa daga wayarsu, SHUWWAR kina jin abinda nake nufi da ke?, Ina so ki ji tsoron Allah, ki sani mutumen nan yana da hakki a kanki, ki kiyaye dukan wani abin da zai zamto cutarwa ne a gare shi, zan je na samu manyana da nake maganar sirri da su na sanar masu damuwarmu ba tare da na basu sunna ba, dan su tayamu fadawa Allah, zamu hanna kanmu barci na tsayin sati biyu mu ga yadda Allah zai yi, idan kuma suka ci gana da kiranki ki yi kirana ki sanar min ko ki zo ki sanar min domin mutanen nan babu abinda ba zasu iya yi ba sunna iya sauraronmu ta waya su gane kin fadawa wani Maganar su maki ila, ki taso ki zo ki sanar min ni kuma na samu mijin naki mu yi maganar in sha Allah, Allah zai toni asirinsu ko su waye da izinin Allah, fatana ba hakinsu ya ci ba suka taso masa"

SHUWWAR ta ringa amsawa, sunna haka Hajia Rabi'atu ta dawo, daidia ana kiran sallah a dole ya mike itama ta dauki Nikaf dinta ta fice tana fada masu gidan Hamza zasu wuce

A lokacin da ta zo cikin motar wani fadan ne suka bude sabo, har suka isa gidan Hamza
A nan falon Fauziya suka baje bayan su masu yin sallar sun gabatar suka shiga hira , a nan Shuwwar ke fadawa Fauziya abinda Nahidt ta yi, ai kuwa suka sakota a gaba tamkar zasu cinyeta danya tana kare kanta , har sai da ta gaji ta ce" Ke Shuwwar da Fauziya ku tashi ku ci uwani mana wai? Na ce ba zan auri Muhamadu ba na ga ubanda zai min dole yai ga jaraba ba zan aure shin ba, iskancin banza iskancin wofi , ba zan aure shin ba!"

Ai fa summa suka sameta wannan ya fadi gaskiyarsa, wannan ya fadi tasa, SHUWWAR ta dire magana da fadin" Shi kadai nake da shi ubana a duniya walahi sai kin aureshi dan ba zaki hada masa ciwon zuciya ba ke muguwa!"

Sunna tsakiyar musun ne wayar SHUWWAR ta dauki kuka

Cirota ta yi tana dubawa , lokaci daya ta zarro ido tana masu alamun su saurara sannan da hannunta ta nuna masu mai kiran ko wanene

Saurarawar suka yi gaba dayansu suka nutsu sunna sauraro

Da irin wancen muryar aka ce" Muna fatan kin gama yin tunani, kin gama yanke hukuncin zaki bamu hadin kai mu hadu mu kawar da shi a doron kasa domin zuwa yanzu mun gama sannin cewa har rapping dinki yake kokarin yi a cikin gida, shin zaki amince mana mu cin masa a lokacin da bai yi zaton haka daga garemu ba?"

SHUWWA ta yi dan murmushi ta ce" To wai su wanene ku? Yaya zan yi baban aiki irin haka da ku bayan ban sanku ba?"

Amsa aka bata kamar haka " Ba sai kin sanku ba da zarar mun samu burinmu gaba dayanmu a lokaci daya, kawai ki bamu dama mu kuma zamu ajiye maki abinda zaki masa anfani da shi ki kawar mana da shi ba tare da likita ya gane kashe shi muka yi ba"

SHUWAR ta gyada kai tana kallon Nahidht dake miko mata hannu kan ta bata wayar domin tare suke sauraro gaba dayansu
Ta ce" To ga yayata zaku tatauna kan abin"

Bata tsaya jiran ta cewarsu ba ta saka amsa kuwa sannan ta a
ajiye

Wani bahagumen , lankwasashen ashar ne NAHIDT ta nado ta nadawa mai maganar bayan ta bambance cewar mace ko namiji da mai maganar take ta dora da fadin" La'anane sai mun ci ...............dinka!"

Tana rufe baki Fauziya ta dauka itama ta bada nata mamakin harda kyatsewa ta dire tana firfito da idannuwanta sannan Shuwwar ta shafa fatiha.........domin a dogon da ta daukoma aka katse kiran sai karan kashe kiran da suka ji ne ya shaida masu an katse

Shiru suka yi sunna kallon kallo, a sanyaye Fauziya ta ce" Yanzun kuma mu duka zai kashe kennan..........mun shiga uku"

Nahidt ta ce" ke bari tsinane, babu abinda ya isa ya yi da mu dan iska, kadanma ya ji na so na masa zagin mahaukata na ce da shi kai Uwaka!"

SHUWWAR ta yi daria tana kwontawa ta ce" Baku da mutunci yan matannan ko kadan............
Da wanna suka shantake, da hira tsakaninsu wace suka jima basu yi irinta ba suka nemi shashancewa sunna shan dariya a tsakaninsu sallar la'asar ta sake tashinsu yi, daga nan suka shige kicin dinta tare suka dafa sasaukan dahuwa ta dauki uban kifi da nama sannan suka baje suka ci aka ringa fitarwa da sojojin da suke tare, wa'inda basu yi tunanin zasu samu abinci a wajen matar uban gidan nasu ba, sai dai fitowar abincin ya saka su maida hankali suka ci abinsu sunna masu jin dadin hakan da tunanin lalle ita din zata zamto uwar sojoji

Ba su su tashi a gidan Hamza ba sai da magariba ta sanyo kai sannan suka shiga kimtsawa suka tarkata sukai mata salama suka kama hanyar tafiya,

Sunna tafe SHUWWA na fadin ta rantse da Allah sai an yi auren nan kwana kusa ma kuwa, in kuwa tsoron Furera Nahidt ke ji ta fito a mutun ta fadi cewar tsoronta take ji

Ita dai ta shaka ta yi mata gummm dan ta fahimci so take ta kaita makura su daku a motar ta yadda zasu bar abin fada

_____________________________________

Tunda motarsu ta sanyo kai a makeken tsakar gidan na LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY gaban dukansu ya yanke ya fadi

Ba komai ya ja haka ba sai gannin jerin motocinsa da ya fita da su, kafin shi dake zaune saman kujera hannayensa rike da jarida ya dora kafa daya kan daya ga Dukan alamu karanta jaridar yake yi, sai ko Wajen kofar da sojoji hudu ke tsaye sunna kikitu da kofar sun rasa ta yadda zasu budeta gashi mai banbare kofar an tafi a dauko shi aman ba'a karaso ba, gaba dayansu jinninsu a akaifa da tarin mamaki da tsoron aikin da matar oga ta aikata yau na kile bangarensu ta tafi da ky, gashi ya dawo a kadan ya yi minti talatin yana jira

"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, SHUWWAR dan baban babanki hala ky din kofar cen daya tak ne muka kule muka tafi da shi!?"

Shuwwar din kanta cikinta sai da ya juya ta kaleta a zabure ta kada bata amsa, da kyar ta iya yarfe hannunta ta ce" Walahi da na sani da ban aikata haka ba, shi kadaima masifa yake bale an tabo shi, yau Nahidt dukan sojoji ya wajabta a kanmu wayo Allahna"

Nahidt ta zarro ido tana fadin" Ya wajabta a kanki dai kece matarsa, kuma ke kika rufe gidan ai kau? wai tsakani da Allah mema ya dawo da shi gidan nan yau da wuri?"

SHUWWA ta rintse ido gannin motar ta tsaya, sannan ta ji an bude mata bangaren da take kafin ta ji ana magana kamar haka" Barka da dawowa Madame, a kawo ky na bude kofar "

Hannunta na rawa ta wurgawa Nahidt jakar, Nahidt ta bude ta ciro ky din ta mika masa sukai tsuru tsuru sunna kallonsu aka je aka bude masa sannan ya dakatar da su ya amshi kayansa ya masu maganar da ita dai bata jin me yace kafin ya ga gaba dayansu sun sara masa sun fice, nan da nan harta direbobin mazan suka fice suka barsu daga su sai ransu

Gwauron numfashi SHUWWA ta sauke ta fito a motar tana nufar ciki ta shiga ADU'A a bayane tana kallon Nahidht da ta biyota aman ta ki ta bita ciki ta zauna a saman kujerar nan tana saurare

Yawu mai daci ta hadiye ganninsa zaune yana fuskantarta a lokacin da ta shigo

A hankali ta nufo shi, shi kuma kallonta yake yanaa ta maimaita kalaman da suka yi ita da mai kiran nan a waya har lokacin da ta ba yayarta wayar cewar toh ga yayarta zata masa magana suka ringa bada bada da dayar muryar da bai san ko wacece ba sunna durawa mai kiran ashar, har ta karaso gabansa ta zuba gwuiwoyinta a kasa ta hade hannayenta ta ce" Ka mana rai ka yafe mana, bamu san yau da wuri zaka dawo ba, aman gaba idan zan je gari zan tambayeka lokacin dawowarka , ka san abindama ya tsaida mu Nahidht ce, Nahidt ce miji ya fito mata ta masa wulakanci ta ce bata so, an rarasheta, an mata nasihar ta ce bata so, dan Allah ka taimaka ka mata ihu na tabata tana tsoron soja zata maka biyaya, ko auren dole ne a mata da Abanmu yana sonta shi, yadda akai min auren dolen nan itama a yi mata shi dan Allah ........"
Ta karashe tana hade hannayenta biyu har tana kokarin zama a kan kafafuwansa sannan tana tare Nikaf dinta dake son dawowa ya rufe fuskarta tana kuma hankalce da hannunsa koda yaka so marintan nan, sai ta yi ta kanta!

Tunda ta fara maganar yake sauraronta, haka kuma yana karantarta har ta dasa aya
Sarai ya san dan ta mantar da shi rufe masa faki da ta yi ne ta sako shi a maganarta , aman fa ta ce a aurawa yayarta abansu sai ya samu kansa da mamakinta harma da maimaita kalmar ABANSU?

kafafuwansa ya janye gannin so take ta fada masa a kausashe y💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 3️⃣6️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Chapter 65 · 0% Book details