Sashe 24
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuma a nutse yake basu bayani ya ci gaba da fadin" a ranar da na dagawa Babana hankali da rigima da tashin hankalin wai an ce ji shege ne? Sai ya samu ya zauna da ni shi da mamana dake rike da ni ya ce, Hamza ka daina kiran kanka da shege, domin ba wanda aka samu ba aure bane shege a adinance, shege shine wanda akai ratsen samunsa a cikin zamantakewar matan mutun Idan ya ziyarci iyalinsa ba ranarta......., 'A fa tasa fahimtar kau?' Sai babana ya ci gaba da ce min Hamza ni dan da ka ganni a nan a lokacin ina te ke da bada tsaro a garinku aka tsinto ka, wanu manomi ya tsintoka ya kawo mana kai, mun hau bincike mun saka ka a hannun masu kula da kai sosai, a tsayin sati daya da kwana hudu muka samo labarinka, Mahaifiyarka haifafiyar garin Tanus ce , ta sameka haka ne ba da aure ba kuma aka koreta a gidansu dan sun ki yarda su amsheka, uwa uba saurayin nata ya ki ya amsheka, kai dai wahala ta isheta ta samu wata mata ta ce zata yi mata hanyar zuwa Saudiya Neman kudi, da zarar ta je ta bada kai da fata ta biya kudin jirgin da akai mata itama ta bata naira dubu dari biyar, in ta yarda su yi, idan bata yarda ba karma a fara domin yadda sukai dalilin zuwanta sunna iya yin na dawowarta ba tare da sun bari ta dauko ko tsinke ba, wannan dai shine dalilin da ya sa mamana ta kawo ni gonar Baba Augui ta ajiyeni ta tafi saudiya, maganar da nake yi maka dai har i zuwa yau babu ita babu labarinta, dangina kuwa ba ni ba su Gaskiya dan na kurce su kamar yadda suka ki daukana!"
Shiry falon ya dauka na dan lokaci
Yan matan nan tunda ya yi maganar mahaifiyarsa ta je saudiya sai ya kasance sun sake kura masa ido
SHUWWAR ta ce" Dama haka suke yi ne? A biya masu su zubar da bayansu ba ruwansu su yi tafiyarsu su je su haifa su kuma mutu su bari?"
Malan ne ya yi dan gagawar fadin" Ehm, ki yi shiru, bawan Allah kai kuma me ya kaika gidan giyar?"
Dan dagowa Hamza ya yi ya dan kalli Malan sannan ya maida kansa ya ce" Sha nake yi, an yi an yi na daina abin ya gagara, yanzu haka dai ta jiya ce kadai ban sha ba, aman in sha Allah ni na san watarana zan daina, na fada a shaye shaye ne sanadiyar abokannan banza, aka taki rashin sa'a babana a duniya yanaimin makauniyar soyayar da ba zai sakani kuka ba koda dan sanadiyar hannani shan giya, mamana kam na iya bakin kokarinta, a wajenta na gane ilar shan giyar kafin na gane haka da kankin kaina, domin sanadiyar ina shan giya na ga wulakancin rayuwa kala daban daban, na nemi aure sau biyu abinda yake faruwa da neman auren nawa ke sakani a kuncin zuciya, Malan ka gaa dai yada nake , ina aiki, ina karantun islamiya har yanzu, aman a haka kuma nake zuwa na sha, ban sani ba, ko kuma zaku hanna min mata?"
Wani shauki ke diban Fauziya da ta kure shi da ido, a hankali ta sada kanta a lokacin da ya dasa aya tana mai tsintar zuciyyarta da mangarinsa wa kanwar tasu, tana ji a ranta wannan din ai bashi da aibu, shan da yake yi kuwa idan har Allah ya nufe shi da dainawa zai daina ne in sha Allah, ita ba abinda ya birgeta da shi sai halayansa na fadin gaskiya kai tsaye, duda basu da tabacin gadkiyar ya fada, aman mutumen da zai fadi laifinsa kai tsaye ba tare da jin kunyar d'an Adam ba, gaskiya abin a duba ne
Malan ya lumshe idannuwansa yana tunanin mizanin dora wannan lamari
A hankali ya furta" Astgfrullah "
Ya sake yin shiru sannan ya dubi fuskar Hamza da ta NAHIDT, sai kuma ya kore da gagawa abinda fuskokinsu ke fada masa yana mai tunanin kaye kaye ne irin na tunanin mutun
A nutse ya ce" Malan Hamza, na gode, na gode matuka da ka ceci yarinyar nan ta hanyar nuna mata ilar saka kanta a rayuwar da ta so sakawa, ka sani daga yau, daga yanzu zan ringa sakaka a adu'ar Allah ya kawo gagarumin dalilin da zaka fita a harkar shaye shaye, domin shaye shaye bashi da anfani, bashi da kyau ga kiwon lafiyar dan Adam, kai ka san shaye shaye yana hadasa rayuwa irin ta wulakanci, sannan uwa uba shaye shaye laifine ne a adinin musulunci yana da zunubi mai girman gaske, Allah ya sa ka daina"
Da amen suka amsa , shi kuma ya sake yin shiru yana ta yanyanke hukuncin furucinsa ya ce" Dangane da maganarka da Shuwwar, zan iya ce maka gaskiya ban shiryawa ganninta fadawa wata rayuwar makamanciyar haka ba, sannan ba zan ce maka aa kwata kwata ba, zan iya ce maka ka je ka yi ta adu'a idan har shuewar rabonka ce, Allah ya tabatar maka, ka ga sanadiyar sakinta da mijinta ya yi dan mahaifinsa baya sonta ne kawai ba dan wani dalilin ba, zan tashi ne na sake mikata wani hannun da nake hangen wani tarzomar? wannan karron sai dai ta yi hakuro ba zata sakani aikin gagawa ba, domin na yi mata sau daya, na mata na biyu, na mata na uku babu riba a ciki ko daya, a koda yaushe faduwar ta fi cin ribar yawa........ina fatan ka fahimta Malan Hamza"
Idannuwan yan matan nan uku yadda ka san zasu fado kasa dan kallon Malan, sai dai a cikinsu babu wace ta iya budar bakinta ta furta A ne domin wanni irin hade fuska da malan din ya yi kai ka ce zai hau yaki da dayansu ne
Hamza ya sake gyada kansa yana jin wani farin ciki na kalaman da ya samu bayan an ji ko shi waye, yana dauke da tabo biyu a rayuwarsa wa'inda malan bahaushe ke jifa da shi dan huce haushi ko dan kin bawa, sai gashi an saurare shi , an bashi damar fadin abinda yake da na fadi, kuma an masa kyakyawar magana, a duniyama kaf banda babansa waye mai yi masa irin maganar nan haka?
Yana murmushi ya ce" Na gode sosai Abanmu, aman dan Allah hakan na nufin ba zan kuma zuwa nan ba?"
Malan ya sauke wata ajiyar zuciyar yana fadin" Zaka kuma zuwa mana, aman idan na kirayeka, yanzun idan zaka fita ka ba mai gadi numberka domin ban fito da waya ba zan tuntubeka in sha Allah"
Da godiya sosai ya mike ya fice bayan ya yi masu salama yana mai jin kaunarsu har cikin ransa irin kauna ta ban mamakin nan, gaba daya dangin Shuwwar yana jinsu har cikin zuciyarsa hakan ke bashi tsoro da jin tsoron kar dai su hanna masa ita, domin ga dukan alamu soyayarta bata fara damkarsa da wasa ba
"Muhamadu rasululahi" ta fada da karfinta tana zarro ido da mikewa da sauri ta leka ta ga ya tafin fa, ya tafi da sauri ta dawo tana kallonsa ya karasa fadin" Sallalahu alaihi wa salam"
Sannan ya dubeta yana fadin" Ke yaya zaki ambaci mai daraja, mafi daraja a cikin masu daraja baki idasa hade sunnansa yadda matsayinsa ya kai ba? Baki san hakan baban kuskure bane?"
A dan rikice tana zama dan daf da shina kasa a gabansa wanda Hakan ya saka shi dauke kansa a kanta yana hade fuska sannan ya dan matsar da kafafuwansa sosai
A dan birkice ta ce" Ai zan karasa ne, Sallalahu alaihi wa ahlihi wa asahabihi wa salam"
"Malan me ka yi? Kaf a cikin manema auren Shuwwar akoy mai hankali dan mutunci irin wannan ne? Yana zuwa ya min, na ji ya shiga zuciyata, harma na ji wannan din ai mijin aure ne, shine zaka nemi ja masa aji har ya ki dawowa? Idan ya ki dawowa na rantse maka sai mun je nemansa gidajen manyan sojojin da sukai ritaya har Allab ya sa a dace, Malan yanzu fisabililahi meye ribar haka da aka aikata? Ka gaa shi ya rakamu gidan su wancen shegen muka amso akwatunnanta gasu nan, kuma shine zaka wulakantar da shi? Da acema auren kawai ka daura masu ai da ya fi , malan ko dai ko dai kana cikin mutanen dake iya yi masa kiyaya dan yana cikin jerin masubaikata kaifi sannan an haife shi ba da aure ba? Malan ka hanna masa y'a ne dan shi din mashayi ne?" Ta karashe tana dora hannunta jikin babar rigarsa daga gefe tana irin son ya juyo din nan ya fuskanceta
A kan hannun nata ya sake dora idannuwansa da dan karfi ya janye rigarsa yana fadin" ke, ki, ki fa daina abu irin na jahilci daina kunace min wuri mana hakanan, tashi ki koma kusa da yan uwanki tashi tashi!"
Fuskarsa ta kalla da sauri jin furucinsa sun kausasa sosai
Ai kam shayinsa ne ya sake darsuwa a zuciyarta, hakan ya sa ta mike ta koma tana zaunawa hadi da sake zuba masa ido
Akwatunnan ya sake zubawa ido sannan ya maido dubansa kansu ya ce" Me kennan?, A kan wani dalili kuke so karfi da yafi sai kun nunawa duniyar cewar baku da daraja sannan kun wulakantar da kanku? Me hakan yake nufi da zaku he ku dauko yan akwatunnan da take da layi uku kala daban daban a dakinta? A cikinku wacece bata da suturar da zaku je neman kari?, Ku kunna tunanin kun kauro duniya da zaman dindindin ne? Na ce hala an maku albishir din an cire ku daga cikin wa'inda zasu tsaya a gaban Allah a yi masu hisabi? Ko bakwa tuna kwwonciyar kabari mai tsayi ne?! Subahannalah yaushe zaku daina kwaba shirme kunna ci ne?"